← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 239 OF 267

Sashe 239

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsalle ta buga kamar yarinya ta fada kan gadon Maman da rabon data ganshi a ido bare ta hau tun dana da yanci tayi juyi akai se kuma tayi saurin sauka tana dariya kamar wata fagal, kayan ta diba ta fita falo ta jona Iron ta fara gugar Mama ta shigo ta zauna haka ta ringa gugar dukda ba magana sukeyi ba amma taji dadin yau gashi sun zauna inuwa daya da Maman ga kuma Abba sun shirya. Ta bude baki yafi sau nawa da niyyar yiwa Maman magana seta kasa duk kuma tana ankare da ita har aka kira sallar Azahar ta ajiye Gugar ta fita ta dauro alwala Anty na hidimar girki tayi mata sannu bata tsammanin ta amsa a ranta tace
"Kyaji dashi idan ma baqin ciki kikeyi na shirya da ubana sedai ki mutu" ta wuce falon Maman a can tayi sallah Mama ta ringa Mamaki ganin yau Umaimah ce take sallar Nafila bayan ta idar da Azahar din tayi Raka'a biyu sannan ta zauna tana lazumi Umaimanda Farillar ma yinta take kawai dan ta zama dole idan ta idar kuwa bata tsammanin tana Addu'a dan minti biyu yayi yawa ta tashi daga gurin se gashi yau bayan ta idar tafi minti talatin zaune tana lazumi kafin ta daga hannu tana addu'a nan ma ta dade kafin ta shafa sannan taci gaba da gugar bata dade da ci gaba ba suka jiyo karadin Bibi se gata ta fado falon ta watsar da jakar ta a bakin qofa da gudu ta fada kan Umaimah da tayi saurin janye Iron din ganinta nufota

"Ke kuma ya haka daga ina kike harda uniform kin fadowa mutane daki babu sallama haka akeyi?" Mama ta fada kafin ta bata amsa Mu'ayyad da Iman suka shigo da sallama, seda suka cire takalmansu kafin suka shiga ya durqusa a gaban Maman ya gaisheta ganin haka itama Iman tayi yanda yayi Maman ta amsa cikin kulawa sannan ya juya ya gaida Umaimah dake ta kallonsu

"Tashi ki fita ki cire takalmin nan a waje da zaki gama tako dattin makaranta dana gari kike taka mun daki babu sallama bare gaisuwa qanwarki ma ta fiki hankali". Baki Bibin ta zumbura tana qara maqalqale Umaimah Mama ta zare mata ido tana daga maficin dake gefenta tace
"Sena zaneki da wannan idan baki tashi ba futsararriya kawai me irin halin uwarta" seta miqe tana bubbuga qafa irin na tabararrun yara ta fita tana zuwa saitinta kuwa ta kwada mata maficin a baya da qarfi ta kwalla qara kuwa kafin ta kwanta a gurin zata fara birgima ganin Maman ta fizgo wayar caja daga jikin socket yasa ta take da gudu ta fice daga dakin
"Ja'ira daki tsaya dana cire miki iyashegen da yake damunki"

"Yanzun nan ta gama birgima a school Mama saboda Driver yace baze kawo mu nan gidan ba seda ya kira Dady har wurgar masa da waya tayi a qasa" Mu'ayyad yayi maganar cikin nutsuwa tamkar Mahaifinsa se Mama ta riqe baki tace
"Eh ba shakka ai daman barewa ba zatayi gudu danta yayi rarrafe ba to kuwa uwarki zakici bamu gama da wata bama balle ki tashi ki fitine mu, yanzu Ina Dtiver yana waje ko ajiye ku yayi ya tafi?"
"Ina ga ya tafi naji tace masa se anjima ze dawo ya dauke mu" Mu'ayyad din ya sake fada se Mama tace
"Dabdi itace ma me gaya masa abinda zeyi kenan?"
"To ai Mama shima Dady se abinda take so yakeyi ba shiyasa take yin haka ba ta ringa mun rashin kunya a school a gaban friends dina kuma idan na doketa ta gayawa Dady ni yayi mun fada kuma a gida ma ko Mamah ce tayi mata fada Dady baya so" yanda yayi maganar zaka gane jin haushin abun har ransa

"Ai kuwa ya dakko hanyar da bazata bille ba kuma tilas ya gyara wadda bata tashi a sangarce bama ta fitini mutane balle wadda tun tana qarama babu kwaba ai kuwa ba'a taki gaskiya ba".

Umaimah dai kanta na qasa ta gagara cewa komai kan wannan magana da Mama take yaba mata ita da yarta seta shiga tattara kayan gugar data gama ta shige mata dasu daki ta ajiye akan gado se anjima idan ta yarda zata shirya mata su a wardrobe. Dakinta ta wuce can ta tarar da Bibin kan gadonta a kwance tana ganin Umaiman ta tashi da sauri ta rungumeta tana cewa
"Momy nayi missing dinki da yawa"
"Kai Bibi se kace ba last week kuka zo ba me yasa zaki ce se an kawo ku yau daga makaranta bayan akwai islamiyya yau?"

Baki ta tura tana cewa
"Ni Momy so nakeyi na ganki kuma indai baki dawo gidanmu ba kullum haka zan ringa cewa se an kawo ni kefa kika ce zaki dawo gashi an yi wata da yawa baki dawo ha Dady ma idan na tambayeshi yaushe zaki dawo baya cemun komai Momy kodai kema irin na Mamansu Halima Dady ya sakeki ba zaki dawo gidan mu ba?"

Rasa abinda zata gayawa yarinyar tayi dan haka ta wuce bakin gadon ta zauna Bibin ta sake binta tana maimaita mata tambayar still tayi shiru seta zauna tana cewa
"Daman na sani Dady ya sakeki yanzu Mamah ce matarsa kenan muma step Mom ce kawai damu zata ringa maltreating namu yanda akeyiwa su Halima?"

"Me yasa kika fiya surutu Bibi Wacece Halima kuma me Steo Mom din tasu take yi musu?" Umaimah tayi qargfin halin fada se Bibin ta riqe hannunta tana cewa
"Momy Step mom dinsu Halima muguwa ce daman kuma mun karanta wani story book na wicked step mom, dan Allah Momy ki dawo kinji ni bazan iya zama a gidan bakya nan ba".

Kallonta ta ringayi yanda take maganganun da suka zarce wayonta to ita yanzu wane bayani zatayi mata da zata fahimta ba tareda ta sake kawo wata maganar ba?
"Ko saboda Dady ya auri Mamah ne ya sakeki ba zaki koma ba?" Bibin ta sake jefa mata wata tambayar kafin ta bata amsa tace
"Zan gayawa Dady ya saki Mamah kawai ki dawo ni daman bana sonta takura mun takeyi kullum tayi ta mun fada idan nayi abu kuma ba haka takeyiwa su Mu'ayyad ba".

Murmushi yayi ya kalli Mama data rafka tagumi tun zamanta kuma batace komai ba yace mata
"Toh kinji kiyi magana ta tabbatar kin haqura indai ba kuma da sauran wani abu a ranki ba" seta janye tagumin tana cewa
"Toni me zance Alhaji ai ba yanzu ya kamata muyi maganar ba tuntuni ya kamata ace anyita tunda se yanzu tayi lokacinmu to ni banda lokacinta seta jira se randa nayi"

KHALIL

Ayyukansa yaci gaba dayi, wuraren qarfe hudu ya tashi kai tsaye gida ya wuce yayi mamaki dabe tarar da motar yaran a ajiye ba dan haka yayi tunanin ko Humaira ta aiki Mannirun ne, seda ya fara shiga gurin Hajiya ya kai mata Fruits din daya shigo dasu kafin ya wuce bangarensu, falon shiru se motsin Ruqayya da ya jiyo daga kitchen seya wuce sama qilan suna can. A falo ya tarar da Aryaan yana bacci da alama wasa yayi ya gaji baccin ya daukeshi ba tareda ya sani ba ya gyara masa kwanciya ya wuce dakinta yana tunanin toh ina sauran yaran suka shige tunda be gansu a bangaren Hajiya bama.

Humaira na zaune akan kujerar dake dakin tana shan Baqin lipton dan tun da suka dawo daga Asibin take kwance sallah kadai ke tada ita gaba daya kasala ta mata rubdugu se yanzu ta samu tayi wanka tasha ruwan Tea saboda cikinta da ya daure dalilin bata ci komai ba. A sanyaye tayi masa sannu da zuwa ya amsa yana qarasawa kusa da ita ya rungumeta ta gefe yana cewa
"Ya jikin?"
"Da sauqi, yau ka dawo da wuri" ta bashi amsa seya saketa yana cewa
"Yah kwana biyu ayyuka sun mana sauqi so far kusan duk wasu constructions da mukeyi mun kammala se ragowa shiyasa bana kewayen Site"

"Toh Allah ya taimaka ya kawo wasu ayyukan na Alkhairi" ta sake fada se ya amsa mata da
"Amin Baby" yana murmushi yana bala'in jin dadin yanda take masa addu'a a koda yaushe kuma yana ganin hasken hakan.
"Ina yaran naki naji gidan shiru ne?" Ya tambayeta seta ajiye kofin hannunta tana cewa
"Ban sani ba koda suka dawo sun shigo ina bacci dan ban dade da farkawa ba qila sun wuce islamiyya"
"Ok" ya fada kafin ya fita daga dakin zuwa nasa. Seda yayi wanka ya canza kaya ya fito sannan itama ta fito falon Saman ya kalleta tana zaune a spot dinda Umaimah take yawan zama sanda tana gidan, dukda ya canza kujerun falom saman dana qasa amma dukda haka wani lokacin idan ya kalli guraren da take yawan zama se yaga kamar ze ganta a gun. Kusada Humairan ya zauna ya kalli Aryaan dake baccinsa yace
"Ba za'a tashe shi ba kuwa baccin la'asar karya kasa na dare"
Chapter 239 · 0% Book details