← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 267

Sashe 106

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta kawai Khalil yakeyi saboda Mamaki ya kasa ce mata komai, ta yaya zata yafewa wanda yayi mata wannan mummunan qazafin?
"Amma Hadiza..."
"Ni sukayiwa kuma nace na yafe, Allah ya yafe mana gaba daya" ta sake katse shi sannan ta juya masa baya saboda wani Kuka daya taho mata ba kuma tason ya gani. Sam bata ji haushin Umaimah da yace ba, bata santa ba tasan haka kawai bazata qirqiri abu ta liqa mata ba Khausar ce silar komai daya faru.
Tunda take da ita koda wasa bata taba sanar da wani irin rayuwar da takeyi ba saboda roqonta da tayi akan ta rufa mata asiri kuma ta tayata da Addu'a saboda ta dena, ta riqe mata amana haka zalika bata taba yin sallah ta tashi ba tareda ta roqar mata yafiyar ubangiji tareda shiriya ba amma shine ta rasa abinda zata saka mata dashi seta bibiyeta da sharrin abinda ita take aikatawa? Amma ba laifinta bane, laifin kanta ne data ci gaba da Mu'amula da ita har bayan tasan zahirin wacece ita, gashi yanzu ta shafa mata baqin fentin da har abada baze taba gogewa gaba daya ba amma yaqinin daya take dashi Allah yana madakata yana jiran kowa da komai.

Gajiya Khalil yayi dayi mata magana tayi shiru kamar me bacci, yana kallonta yace
Zanje gida na huta dan dawowata kenan daga SA ko gida banje ba na wuto nan, zan tafi amma ki sani koda kince kin yafe ni bazan haqura ba dole na dauki mataki akai"
"Kaje amma karkace zakayi rigima da matarka saboda ni, Sonka da kishinka ne suka saka ta aikata komai da taimakon wasu kaga laifi bana ta bane ita kadai" Hadizan ta sake fada ba tareda ta kalleshi ba dole ya juya ya fita daga dakin, a waje ya tarar da Malama Lawisa da Jalilah suna magana yayi mata sallama yayi gaba Jalilah ta bishi.

"Wai ta yafe musu tace" ya fada yana kallon Jalilah dake tambayarsa yanda sukayi da Hadizan, bude ido tayi tana kallonsa kafin cikin wani yanayi tace
"Allah sarki anyi mata mummuna ta saka fa Kyakykyawa ubangiji ya saka mata da mafiyin haka. Anyi amfani da kyakykyawar zuciyarta an cutar da ita. Na tabbata irin wannan halayyar tata ce har ta bawa qawar tata damar cutar da ita ba tareda ta sani ba ita Kuma Umaimah bata kyautawa kanta ba, ban taba zaton koda wasa zata iya aikata kwatankwacin sakarci irin wannan ba ita yanzu koda ace dagaske ne ya kamata ka yayata irin wannan abin a duniya? Idan baka rufawa dan uwanka Musulmi Asiri ba ai baka kuma bankadashi kowa ya sani ba"

"Hmmm kawai Khalil yace dan idan ita tace ta haqura shi be haqura ba, Umaimah ta dade tana abubuwa yana shanyewa, idan har zata iya yiwa Mace sharri irin wannan ba tareda tana da hujjaba gaba besan me zata aikata ba. Dole ya taka wa abin burki ya kuma dauki mataki daidai wanda ya dace da laifinta, A hanya suka rabu da Jalilah tasauka ta bar masa motar ya wuce yana sake jaddada mata akan karta bari kowa yasan da zuwansa ko halinda ake ciki.

*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 44

Gidansu Umaimah ya nufa kai tsaye, yana so ya fara tattara hujjojin da suke hannuntaa kafin ya hada Khausar da Umaimah da hukuma su girbi abinda suka shuka. A qofar gida ya tarar da Ummu-Salma da Yasir kowanne fuska face face da hawaye, ya kashe motar ya fito yana tambayarsu lafiya Yasir ya tafi da gudu ya fada jikinsa yana cewa
"Yan sanda ne suka zo suka tafi da Antyn Boy boy" ya sake rushewa da Kuka.

Kallon Ummu-Salma yayi cikin rashin fahimtar maganar Yasir yace
"Meya faru Ummu? Ina mutanen gidan kuke kuka haka?"
Ita tayi masa bayanin yan sanda ne sukazo suka tafi da Anty Umaimah, se sannan ya tuna Mu'ayyad suke cewa Boy boy, da sauri ya tambayeta me tayi ta watsa hannu alamar bata sani ba kafin taci gaba da gaya masa su Mama da Anty sun bisu, Yaya Aminu ne ya tafi kaisu dan Abba bayanan ya tafi daurin aure Qiru.

Dafe kansa yayi da hannu daya dayan yana riqe da Yasit dake rusa kuka kamar wanda aka ce Umaimah bazata dawo ba. Seya zaro wayarsa cikin rashin Sa'a ta mutu daman babu wadataccen chaji a ciki ya taho.
"Kina da waya ki kirasu muji inda suka tafi?" Ya tambayi Salma tace
"Aa, amma wayar Anty Umaimah na daki bata tafi da ita ba ko na dakko maka?" Kafin ma ta kai qarshe yace eh.
Ta ruga gida da gudu ta dakko wayar ta kawo masa ya karba ya bude dan yasan password dinta. Number Yaya Aminu ya kira cikin Sa'a ya daga suka gaisa yake sanar masa gashi a gida su Yasir sun gaya masa abinda ya faru suna ina ne?

"Daga dawowarka se kaji tashin hankali kuma, muna state CID wallahi yarinyar nan ce ta jangwalowa mutane bala'i ana zaune lafiya" Yaya Aminu ya fada kana jin muryarsa kasan yana cikin matuqar bacin rai, cikin Jimami Khalil yace masa gashi nan zuwa. Ya kalli Ummu-Salma da Yasir da suke jiran su bishi yace

"Ku shiga gida yanzu zanje na same su acan"
"Dan Allah zamu bika Yaya" Yasir din ya fada se ya kama hannunsa yace
"Aa ba'a zuwa da yara shiyasa ma kaga ba'a tafi daku ba. Kuma idan mun tafi gidan a bude babu kowa kaga za'a shiga ayi barna. Ku koma ciki ku zauna yanzu zamu dawo ba dadewa zamuyi ba kinji?"
Suka amsa da "Toh". Seda suka shiga gidan kafin ya tada motar ya bar gurin.
Tunani yakeyi a ransa me kuma ta sakeyi da aka kaita CID? Shikan Bala'in Umaimah ya fara shallake tunaninsa ace mace kamar Shaidan, daga wannan fitina se wannan gaskiya da sake, baze iya ba.

Ya isa CID ya tarar dasu Mama a waje duk wanda ka kalli fuskarsa kasan cikin tashin hankali yake. Abinda ya qara daure masa kai ganin Dr Ma'aruf Mijin Rufaida a gurin kenan tare suka jangwalo Koma menene shi daman ya tsani wannan qawancen nasu, ya rasa abinda yasa Umaimah bata sa'ar qawaye a rayuwarta duk kuma na kirkin daya santa dasu irin Su Rumasa'u ta dena hulda ta kusa dasu se abinda ya zama dole ko idan su suka kawo kansu sannan zeji tayi zancen su ko makamancin haka. Se taron marasa tunani irinta da babu meyiwa wani fada idan yayi ba daidai ba a cikinsu.

Yaya Aminu ne yayi masa bayanin suna ciki yanzu qoqari sukeyi a basu damar su gansu a kuma yi musu bayanin laifin da suka aikata amma dai kamar yanda sukaji wai Qungiyar masu kare haqqin Mata da yara ne suka shigar dasu qara dalilin me dai basu kai ga sani ba.

ABINDA YA FARU
Chapter 106 · 0% Book details