← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 267

Sashe 89

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Khausar mekike tunanin kinyi? Meye wannan me kike nema a gurina da har zakiyi mun irin haka?" Khalil ya fada cikin tsawa kamar yana gabanta se tace
"Aa fa ka denayi mun tsawa Malam me nayi maka?"

"Me kikayi mun kike tambaya na ma? Wadannan hotunan a ina kika same su yaushe aka dauke su?" Khalil ya sake jefa mata wata tambayar, Khausar taja qaramin tsaki tace
"Lokacin da kuke fita yawon shaqatawarku da Hadiza ni kuma na saka wanda yake bibiyar mun dukka sahunku yana daukar mun hotunana" se yayi saurin katseta da cewa

"Qarya kikeyi wadannan hotunan ba gaskiya bane, babu ko guda daya da yake ainihin yanda aka dauke shi dan ban taba riqe Hadiza kona taba jikinta cikin sanayya ta ba"

"Wannan kuma matarka da sauran mutane zakayiwa bayani idan na watsasu bani ba, ni daman abinda yasa na kiraka na zata zamu samu fahimta ne cikin sauqi amma naga alamar cikamun kunne da ihu kawai zakayi dan haka na barka lafiya ka kuma kuka da kanka duk abinda ya biyo baya" Khausar ta fada tana qoqarin kashe wayar ya dakatar da ita cikin wata murya yace

"Me kike da buqata?"
"Yawwa now you are talking like a smart Man amma da se wani surutu kawai kakeyi" Khausar ta fada kafin taci gaba da cewa

"Da farko inabuqatar ka turamin da 1M a account dina kudin bata lokacina da kudin aikin yaron da na saka yake daukan mun hotunanku, sannan idan kayi wannan se muyi magana kuma akan buqata ta ta gaba" tana gama fadin haka ta kashe wayar ba tareda ta jira amsarsa ba, qarar shigowar Message ya sakashi rufe bakinsa daya bude tsabar mamakin Khausar, account number ta turo masa kuwa tana sake jaddada masa ya tura sannan ya kirata su qarasa magana.

Tissue yaja ya goge zufar data tsatstsafo masa a goshi gaba daya ma ya rasa tunanin me zeyi yanzu kenan Khausar Blackmailing nasa take so tayi ta ringa tatsar sa kudi akan laifin da ne aikata ba amma me yasa zatayi masa haka? A zatonsa Aminiyar Hadiza ce me yasa zatayi musu haka dan wannan abin bashi kadai ta shafa ba harda Hadizan wannan tunanin da yayi ya sakashi saurin daukar wayar ya shiga kiran Hadiza sedai tun daga yanayin muryarta jikinsa ya qarasa yin sanyi.

"Ta turamun nima ta kuma fada mun wasu banzayen sharudanta idan ba haka ba zata turawa Mama da Yaya hotunan" Hadiza ta fada lokacin da ya gaya mata saqon Khausar daya samu.
"Amma me yasa zatayi haka Hadiza daman Khausar ba Aminiyarki bace me yasa zata ci amanarki ta nemi saka mu a tashin hankali?" Khalil ya fada murya a sanyaye se Hadiza ta saki kukan da take riqewa tana cewa

"Daman Mama tace tana zargin ka gama dani shiyasa ka gudu kaqi aurena. Bansan waya dasawa Mama zargina a zuciyarta ba ada duk inda zanje Mama bata damuwa ta yarda dani ita da kanta tana fada amma haka kawai komai ya chanza. Ta kai ta kawo har tana fada mun da bakinta cewar tasan duk Barikin da nakeyi nake fakewa da sunan aiki, tun abin yana damuna nayi kuka har ya zaman mun jiki sedai kullum ina addu'a Allah ya wanke ni ya kuma kawo min Miji nayi aure sannan ina Addu'ar Allah ya tonawa duk wanda ya shiga tsakanina da mahaifiyata Asiri se yanzu na gane Ashe Khausar ce, me nayi mata? Yanzu idan ta fitar da hotunan nan da sauran da tace tana dasu da wane baki zan kare kaina a gurin Mama?" Hadiza ta qarasa tana fashewa da wani kuka me tsuma rai.

Gaba daya kansa ya qara zafi ga damuwar da yake ciki ga kukan Hadizan, cikin muryar rarrashi yake mata magana
"Kiyi shiru Allah shine shaidar mu bamuyi duk abinda yake a cikin hoton ba, kuma qarya takeyi da tace miki tana da wasu kawai so takeyi ta firgitaki. Ki kwantar da hankalinki yanzu zan kai report gurin yan sanda akan tana so ta bata mana suna idan anje can ta fadi gaskiyar yanda ta hada hotunan qarya".

"Aa Khalil ni nasan wacece Khausar hatsabibiyace ta gaske duk abinda tace zatayi zatayin, kuma ba ita kadai ta shirya wannan abin ba, ko da ace ka saka an kama ta ragowar Abokananta zasu iya aikata abinda bamuyi tsammani ba. Ta taba bani labarin wani abokinta da yake aikin computer, a lokacin wata yarinya aka saka yayiwa sharri ya dora fuskarta akan wani nude video suka turawa Mijin da zata aura qarshe haka suka lalata auran ita kuma suka kassara mata rayuwa" Hadiza ta sake fada cikin kuka kafin taci gaba da cewa

"Dan Allah Khalil ka bita a hankali, duk abinda tace kayi idan da hali kayi mata mu samu mu tsira da Mutunchinmu daga ni har kai"

"Miliyan daya fa tace na tura mata yanzu" Khalil ya katseta se tayi saurin cewa
"Miliyan daya, Anya Khausar tana da hankali?"

"Koma menene idan na tura mata yanzu kinsan gaba abinda zata nema a gurina? Zata ci gaba da blackmailing nawane kuma hakan bashine yake bada tabbacin bazata fitar da hotunan ba kamar yanda tace. Nidai bazanyi falling ma tricks finta ba, inada Aboki DSS ne zan kirashi na gaya masa su zasu san abinda zasuyi akan maganar"

"Aa Khalil dan Allah kabi a hankali bana son abinda ze janyo daga ni har kai mu shiga matsala" Hadiza ta sake fada cikin kuka da tsoron abinda ze iya biyo baya. Tayi kuka tayi nadamar sanin Khausar a rayuwarta. Tsakaninta da ita Alkhairi ne bata san me ya saka ta aikata mata ahakan ba.

"Ki dena kuka kuma ki kwanatar da hankalinki in sha Allahu babu abinda ze faru kinji" Khalil ya fada cikin rarrashi, dakyar ya samu ta yi shiru da kukan, ya kuma tabbatar mata duk abinda ake ciki ze kirata ya gaya mata daga nan sukayi sallama.

Message ne ya shigo wayar ya dauka ya duba.
"Ba DSS ba Allah yasa FBI zaka kaini ka tabbata in har ka kai maganar nan gurin hukuma wallahi sena saki abinda ze sakaka nadama har Qarshen rayuwarka kuma ka turamun da Kudin ina jiranka" abinda ta turo masa kenan ya share zufar data keto masa yana salati a zuciyarsa. Wato tayi Hijacking wayar sa kota Hadiza ne da har take iya sauraron abinda suke fada tabbas Khausar Hatsabibiya ce kamar yanda Hadiza ta fada.

Rasa mafita yayi a lokacin ya kuma rasa shawarar wa ze nema. Gaba daya haka ya qarasa wunin ranar cikin tashin hankali da neman mafita, sanda ya koma gida kasa shiga yayi ya ajiye motar a qofar gidan. Gani yakeyi kamar Umaimah ta rigada taga hotunan nan be san kuma wane kalar tashin hankalin ze fuskanta a gurinta ba. Yana nan zaune a motar har aka kira sallar Magrib seya kulleta ya wuce masallaci a can din ma ya bata fin minti talatin kafin yayi qarfin halin miqewa ya tafi gidan.

A waje ya bar motar dan ya yankr shawarar zuwa gurin Mansur ne bashida Aminin daya fishi ya tabbatar kuma ze bashi shawarar abinda ya kamata yayi.
Da sallama ciki ciki ya shiga palour, Umaimah na kwance a qasa Mu'ayyad na gefe can ta zube masa kayan wasansa yana ta surutai irin na yara. Yunqurawa tayi dakyar ta tashi zaune tana kallonsa. Idan ba idonsa bane se yaga ta zabge idanunta duk sun shige ciki kamar wadda ta wuni tana kuka nan da nan gabansa ya yanke ya fadi kodai Khausar ta tura mata da hotunan amma kuman idan haka ne yasan abinda zatayi baze iya hasasoshi ba.

Dakyar ya bude baki ya amsa sannu da zuwan da tayi masa yana qara kallon fuskarta yace
"Lafiya meya sameki naga fuskarki ta fada?"
"Banajin dadi wuni nayi da ciwon kai da zazzabi" ta bashi amsa tana yatsina fuska dan dagaske bata da lafiyar, yana fita kamar an aiko zazzabi da ciwon kan suka rufeta ba dan Hauwa ba da bata san ya zatayi ba.

"Sannu, bari na chanza kaya se muje Asibiti tunda likitan yace idan bakiji sauqi ba mu koma" ya fada kafin ya daga Mu'ayyad da se sannan ya lura dashi ya taho da gudu suka shige dakinsa. Wayarsa ya kunna masa ya shiga wanka, yana shiga yaji an kira sallah se yayi danasanin ya tsaya yayi isha gaba daya kafin ya shigo. A dakin yayi sallar sa yana jin yanda cikinsa ke qara alamar neman abinci amma bashida nutsuwar da ze iya saka wani abu a cikinsa. Sanda ya fito har sannan tana kwance a inda ya barta, shi ya taimaka mata ta saka hijabi yanajin yanda jikinta yayi zafi alamar zazzabin ya kulle gidan suka tafi Asibiti.

Har sukaje babu Wanda yayi magana a cikinsu, Khalil tunanin mafita yakeyi a zuciyarsa dan ko kafin su fito yaga Text din Khausar akan tana jiransa, idan ya kai gobe be tura mata ba ya kuka da kansa, ita kuwa Umaimah abinda takeji a jikinta shiya isheta. Sun isa Asibitin bayan yan tambayoyi likita ya rubuta mata teat yace suje Lab. Jininta suka dauka bayan yan mintina Aka basu Result, tundaga qofar Lab din ta fasa masa kuka dan ita aka bawa ta bude ganin abinda yake ciki yasakata Kukan Khalil kuwa yi yayi tamkar baya gurin dan damuwar da yake ciki tafi wannan shirmen banzan da take nema tazo masa dashi.

Sanda suka koma gurin likita kwanciya yace tayi a gado ya janyo computer scanning ya shiga dubata sega ciki ya tabbata kamar yanda Test ya nuna har na sati 13 ai nan Umaimah ta sake fasa wani kukan ciki wata uku ita tana me har haka ta faru bata sani ba. Ta gama sakan kancewa tunda bata Period bazata dauki ciki ba, shiyasa tace ma bazata Yaye Mu'ayyad ba seya shekara biyu, yanzu shekara daya da wata biyu ace tana da ciki har na wata uku ina zata saka kanta.
Chapter 89 · 0% Book details