← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 242 OF 267

Sashe 242

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uhm Nuru se anjima Habibi muje idan ka gama"
"Oh ashe tare kuke?" Noor din ya sake fada fuskarsa dauke da murmushi ya miqawa Khalil dake tsaye tamkar an dasashi hannu da niyyar Musabaha seya kalleshi ya kalli hannun kafin ya dauke kai, be ko bi takan magungunan dake qasa ba ya bar gurin cikin takunsa na nutsuwa. Dakyar ta iya daga qafa tabi bayansa tana jin Noor din ya biyota da wayarsa yana cewa ta saka masa numberta amma taqi koda kallonsa, zuciyarta ta tsinke da tsoro bazata manta kashedin sa ba tun a zamanin baya akan Noor din ballantana a yanzu da take matsayin mallakinsa lah shakka kuma tasan yaji maganar su ita bata ma san yanda zata wanke kanta ba dukda ai ba wani tayi ba da be kamata ba.

Kamar munafuka haka ta bude murfin motar ta shiga, ta saci kallonsa ya riqe haba da hannu daya dayan kuma ya dafe sitiyarin motar sedata maida murfin ta kulle kafin ya tayar da motar ba tareda tace masa komai ba.
"Wlh Habibi kawai ganinsa nayi a gurin" ta fada cikin rarrabewar murya, shiru ya mata kusan minti biyar suna ta tafiya kuma ba hanyar gida suka nufa ba ta cire ran baze kulata ba kamar daga sama taji yace
"Wanene shi?" Da sauri tace masa
"Nuru ne"
"Nuru?" Ya maimaita da sigar tambaya seta dafe bakinta yanda kasan zata rusa kuka tace
"Noor ne, wannan dan makwaftan nan namu Abokin Yah Habib"
"Dan maqwaftanku ko tsohon saurayinki? Shine har kike jaddadamun sunan soyayyar da kike kiransa dashi wato NURU ko a gaban mutane kina washe masa baki kina dariya saboda kinga abinda zuciyarki take so ai shikenan" Khalil yayi maganar a fusace.

Kuka ne ya kwace mata ta fara rantse rantse ya dakatar da ita da cewa
"Karki qara harzuqani, idan dai dai kikayi kanki Allah dai yana kallo kuma har yamadidi wato kukeyi dani na zama mace bana amfana miki komai tsohon saurayinki yaci zarafina kina tsaye kina murmushi nagode, tunda naga yanzu ya nutsu ya samu abinyi idan kinada buqata sena sawwaqe miki kije ki aureshi shida yake Namiji yake da abinda ze baki ni kuma naci gaba da rayuwata a yanda Allah yaso ya ganni" Khalil din ya sake fada daidai sanda ya faka mota a qofar gidan Mama Hauwa. Ta daga kai ta kalli gidan a firgice ta sake kece masa da kuka tana cewa
"Wlh Yah Khalil ba haka bane ni ban san a ina yaji maganar nan ba rabona dana ganshi tun ranar daka koreshi daga gidan sama da shekara hudu ban sanke ganinsa ba. Kaga gidansu can ma Tunda Hajiyarsu Tayi aure an raba musu gado babu kowa a ciki sunma siyar da gidan a ina zan ganshi me zanyi dashi kuma sannan daka kawo ni gida yanzu me zanyi?"

"Ki fitar mun a mota" ya sake fada a fusace, wani irin mugun kishi ne yake cinsa, saqe saqe kawai zuciyarsa takeyi masa idan bata matsa daga kusa dashi ba ze iya rufeta da duka a yanda yake ji"
"Ba zaki fita ba" ya sake daka mata tsawa ganin taqi fita sema kai data hade da guiwa tana rizgar kuka seya ja wani dogon tsaki saboda yanda kukan nata kuma yasa yaji ba dadi, tada motar yayi suka bar layin shi bema sanme yasa ya kawo ta gidan ba tsabar yanda ransa ya baci ne yasa ya rasa ina ya kamata ya kaita ma kai tsaye Kamfani ya wuce da, a office dinsa ya barta ya shiga meeting tasha kuka ta gode Allah haka siddan tana lallaba rayuwarta Nuru ze jangwalo mata tashin hankali. Ita wlh ta manta dashi, koda a yanzu ba zaman dadi takeyi da Khalil ba amma rashin wani abu be taba sa ta tunano wano Namiji ba balle Noor da tun data auri Khalil ya zama tarihi a zuciyarta tamkar an goge mata tunaninsa haka taji se yanzu kwatsa ze dawo ya haddasa mata fitina da Mijinta shida Allah.

A nan tayi sallar Azahar Sakatariyarsa ta kawo mata lafiyayyen abinci da nama fal dan wannan cikin ya mayar da ita kamar Kura. Ranta ya danyi sanyi tunda har ya tuna da akawo mata abinci irin wanda take so tasan ya huce ko ba duka ba. Tana zaune a qasan carpet din Office din bayan ta gama cin abinci tana maida numfashi ya shigo ya mata kallo daya ya dauke kai dukda fuskarsa babu fushi irin na dazu. Kalar tausayi tayi tana masa sannu da zuwa ya amsa a ciki kafin ya shiga hada kan takaddu yana cewa
"Ki tashi akai ki gida"
"Ni zan zauna idan ka tashi se mu tafi tare" ta fada cikin muryar shagwaba, seya waiwaya ya kalleta kafin yaci gaba da abinda yakeyi kawai yaji ta fasa masa kuka. A fusace ya sake juyawa yana cewa
"Saboda kinga na kulaki bayan haushinki nakeji shine zaki zo kina mun kukan banza to ki tashi ki tafi idan ba haka ba kuma ki kwana a nan dan ni fita zanyi kuma daga inda zani zan wuce gida".

Cikin kukan ta shiga cewa
"To ai gara na kwanan da dai na koma gida kana wannan fushin dani bayan kuma Allah na gani ni ba laifina bane hanya ce ya hadamu kuma indai ba zargina kake da wani alkaba'i ba menene zesa ka dauki fushi daga kawai na gaisa da Noor, kai da kake zuwa gidansu tsohuwar matarka har mafarkinta kakeyi me na taba ce maka akai seni daga gaisuwa se cibi ya zama qari".

Jikinsa ne yayi sanyi ya zuba mata ido kawai yana kallonta dan kalamanta sun taba shi amma ai shi da ita ba daya ba. Shi namiji ne Allah ya yardar masa ya kula Mace sama daya amma ita ai Macece kuma matar aure bata da wata hujja da zata kula wani Namiji kuma ma tsohon saurayi babu ta inda alaqa ta kamatu a tsakaninsu tunda dai har So ya taba giftawa kodan gudun shigar shaidan be kamata ace an ci gaba da wata mu'amala data zarce ta dolen dole ba idan ta kama. Dukda haka seya gyara tsayuwa yace
"To ai ni namji ne kuma tsohuwar matata kikace kinga idan naga dama zan iya maido da ita kona auro wasunta na ajiye cikin gidana ke kuwa sedai ki zaba ko ni ko shi"

"To na zabe ka ni babu abinda zanyi dashi ko a da dinma yarinta ce tasa na kulashi amma yanzu dan Allah so kakeyi na wulaqanta shi daga ya gaishe ni ai kaima ba zakaji dadi ba kaifa kake gaya mun babu kyau wulaqanta dan Adam abinda ya fada nima beyi mun dadi ba, kuna badan ina gudun karna kulashi ka sake fusata ba ai da zan mayar masa da martani da yace maka Mace Aryaan da wannan kuma a ruwa na sha su kenan" tayi maganar tana nuna cikin jikinta, seya dan sassauta fushin yana cewa

"Kodan gaba bana so, karna sake ganinko dashi balle magana ta hadaku"
"In sha Allahu, yau dinma ai hanya ce ta hadamu" ta sake fada seya daga mata hannu yana cewa
"Kawai ki amsa mun da Toh, ko a dakin Mama kuka hadu banyarda ki amsa gaisuwarsa ba haka ko kallonsa baya ga na rashin sani banyarda ki qarayi ba. Asibitin ma canzawa zamuyi indai na tabbatar a gurin yake aiki"

"An gama ranka ya dade hasken zuciyata" ta fada tana isa gareshi ya riqe hannunta yana cewa
"Bana so ki kirani da komai banda Haske dan sunansa ne haka kuma kike kiransa. Baki san yanda zuciyata tayi baqi ba sanda naji kin ambace shi da NURU wlh ba qaramindauriya nayi ba na iya danne zuciyata da dake dashi zan hada na muku dukan tsiya a Asibitin yanda gaba baze qara gigin kula matar wani ba kema ba zaki sake kallon Wani da bani ba" dariya tayi tace

"Kayi haquri, kuskure nayi kuma bazan sake ba in sha Allah yanzu ka dena fushin zaka bari na jiraka idan ka tashi se mu tafi gida?"
"Na haqura yanzu ma zamu tafi ai amma kafin nan muje kiji wani abu" ya jata kan Kujerar dake gefe gane nufinsa ya sa tayi saurin janye jikinta cikin dabara tana cewa
"Naqi wayon ni dai mu tafi gidan kawai na gaji ma bacci nake so nayi".

"A sanyaya ya zauna ya janyo ta itama dole ta zauna yana kallon fuskarta yace
"Humaira, kar kiji nauyin komai ki fada mun damuwarki bana so Allah ya kamani da haqqinki ko kuma na zama silar da zaki cutu". Kanta na kallon gefe ta qi yarda su hada ido, kwana uku da suka wuce seda sukayi Magana da Anty Sumayya dataje mata ita ta fara takalarta da maganar wai taga bata da walwala menene matsalarta da yake tafi Anty Unaizatu iya bugun ciki da jan mutum a jiki se gashi ta bude baki ta fada mata abinda yake damunta dan gane da rashin samun gamsashishiyar nutsuwa a gurin Khalil. Ta gaya mata qunci da damuwa basu zasu bata mafita ba ta bude baki ta gaya masa sannan dole se tayi haquri akan wani abun tunda tasan ga abinda ya sameshi ko baya ga haka masu lafiyar ma da yawa haquri akeyi dasu dan haka suyi magana ta fahimta dashi to ita me zata ce masa bayan duk irin dabarun da Anty Sumayyan tace anayi yana mata fiye dasu amma a yanzu bata jin suna mata ita dai kawai wancan abun da da bata so shi take qulafuci har mafarkinsa takeyi.
Chapter 242 · 0% Book details