Sashe 46
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saboda zafin da jikinta yayi dole likita yayi mata akluran saukar da zazzabi kafin ya hado mata da magungunan da zata sha tareda dogon gargadi akan sakawa ranta damuwa kodan qaramin cikin da take dauke dashi, shi ya gaya musu satikan cikin bayan da yayi mata scanning a yanzu cikin nata na sati na takwas su kuma suna sati na goma da aure haka suka kama hanya babu me cewa dan uwansa qala har suka dawo Hotel din, bata jirashi ba dukda yanda take jinta kamar zata fadi saboda rashin kwarin jiki amma haka ta shige sedai tun a reception ta rikice dan ta manta inace hanyar bangaren da suka saukan, seta samu kujera ta zauna tana mayar da numfashi, ta daga kai kenan ta hango yarinyar dazu data gani da Khalil.
Fara kyakykyawa kana ganinta kaga fulanin usul koma ace ta hada jini da Larabawa suna tsaye da wani babban mutum suna magana, mantawa Umaimah tayi da duk wani ciwo datake ji a jikinta ta miqe a zabure ta nufeta sedai bata kai ga isa kusada ita ba Khalil da shigowarsa gurin kenan ya riqeta kamar dan sanda ya kama barawo.
"Ka sakeni na koyawa waccen kilakin hankali ta yanda bazata sake gigin kula Mazan wasu ba" ta fada muryarta bata fita sosai sabo kukan data sha, be kulata ba se qara daure fuska da yayi ya shiga janta tana turjewa
"Bayero" sukaji an kirashi se ya tsaya tsak tareda Juyowa Umaimah ta sake zabura amma riqon da yayi mata bana wasa bane,gaba daya ya mannata da jikinsa sannan ya kama tsintiyar hannunta seda tayi qarar Azaba ta shiga kiciniyar qwacewa har budurwar ta qaraso inda suke.
"Lafiya dai naga kana riqeta?" Ta fada tana kallon Umaimah da Khalil ya matse kamar burodi bugun qato ta kasa kwakwkwaran motsi, tafiya ya farayi yana cewa
"Bata jn dadi ne daga Asibiti muke, baki tafi ba kenan ko kun fasa Dinner?"
"Ai yanzu goman tayi nayi meeting da wani client dina ne akan wata kwangila idan abunuwa sun zama ready zanyi maka magana ma kayi taking care of the Arcitectural part" Burdurwar ta fada har sannan tana kallon Umaimah data haqura ta fawwalawa Allah, haka ya jata qiii suna isa dakin kafinma tace wani abu ya saketa ta tafi taga taga zata fadi Allah ya taimaketa ta dafe kujera.
Nunata yayi yace
"Wallahi Umaimah karki kuskura ki kaini bango dan bazaki ji dadina ba ki kuma shiga hankalinki karki kuskura ki sake maimaitamun irin shirmen da kikayi yau idan ba haka ba Allah zaki gane shayi ruwane" yana gama fada ya shige bandaki ya barta zaune tana binsa da kallo.
Kukan baqin ciki ta sake rushewa dashi, har yayi wankan ya fito tana zaune, seda ya gama shirin baccinsa tsaf kafin ya dakko ledar Abinci data magunguna ya dawo gabanta ya zauna, hannunsa ya dora a goshinta ta janye, jikin nata har sannan da zafi rau. Tausayinta ne ya kamashi dan haka ya sassauta fuskarsa dake dinke babu fara'a cikin lallashi yace mata
"Zo kici abinci kinga jikinki da zafi har yanzu ki dena wannan koke koken ya isa haka"
"Ni bana ci, kaje ka kaiwa waccen me kama da bulalar tunda itace..."
"Umaimah" ya kira sunanta cikin dakewa amma murya a tausashe kafin ya saka kwayar idonsa cikin nata dake zubar da hawaye dolenta ta sauke idonta qasa dan bazata jure irin kallon da yake mata ba.
"Me yasa ke baki son zaman lafiya koda yaushe kin fi so ayita tashin hankali? Abinci nace kici ba wata doguwar magana ba idan kuma kinqi zan danneki na dura miki dan bazan lamunci ki ringa barmun baby da yunwa ba"
"Seka durawa babyn yaci dan indai ta bakina abinci ze wuce ya samu ba kuwa zeci ba tunda shi ka damu yaci bani ba" ta fada tana murguda masa baki tareda juya masa qeya, murmushi yayi a ransa yana jinjina irin qaunar da Umaimah takeyiwa tashin hankali, seya saka hannu biyu ya juyo da ita yace
"Allah ya baki haquri Maman baby dukkanku na damu kuci, kinga zafin jikinki qaruwa yake ki ci ko yaya ne kisha magani ki kwanta dare yana qarayi".
Shiru tayi masa tana ci gaba da jan hanci a ranta kuwa Allah kadai yasan me take ayyanawa.
"Bazaki matso kici ba?" Ya sake fada yana kallonta amma ko gezau sema miqe qafafunta da tayi ta jingina da kujerar bayanta tana shirin bacci, Abincin ya bude, Soyayyen dankali ne da Kaza dan ya se shawarma, sun rigada sunyi sanyi.
Tashi yayi ya saka a Microwave ya dumama mata sannan ya hado shayi me kauri yana ankare da yanda take satar kallonsa ya gama ya dawo gabanta ya ajiye, muqut ta hadiye yawu saboda yanda qamshin abincin ya daketa amma ta dauke kai sema ta shigayin kamar zatayi Amai, be ko bi ta kanta ba gaba dayanta ya dorata a jikinsa ya daga kofin shayin daya rigada ya saisaita ya kai mata baki, ta kauce ya saka hannu ya danne kanta dole uwar naqi ta bude baki ta shiga kwankwadar shayin dan dama a yunwace take ita kanta tasan yaudarar kanta take amma bazata iya bacci bata ci komai ba.
Tas ta kurbe shayin kafin ya sake ta yana kallon yanda zufa take keto mata kamar wadda ta watsa ruwa, kumbura baki tayi ta sauke kai qasa ta janyo kwanon dankalin ta shiga ci Khalil yaja gefe yana kallonta cikin dan lokaci ta cinye abincin tas ta shiga sauke numfashi dan ji tayi abincinya tafi da duk wani abinda yake damunta.
"Good girl, saura wanka" ya fada yana kwashe kwanukan ya hada da tun na rana data bari ya killace su gefe, ya zata zatayi musu se yaga ta tashi zugui zugui ta wuce bandakin, wanka tayi tsaf tareda Alwala ta fito zazzabinya sauka jikinta ne dai take jinsa babu kwari se quncin zuciya wanda ta dorawa kanta.
Rigar baccindaya rigada ya ciro mata ta dauka ta saka ta dora dogon hijabibta ta tada sallah Khalil na daga kan gado yana kallonta ta idar ta gama Addu'ointa ta shafa seta zame ta kwanta a gurin.
"Ya haka zaki kwanta a qasa? Ki tashi kisha maganin se ki kwanta gaba daya" Ya fada yana qarasa wa inda take, tashi zaune tayi ya balla mata maganin ya bata ruwa ta kora tana gamawa ta sake kwanciya ta duqunqune da hijabinta.
"Wai meye haka Umaimah ya zaki kwanta a qasa cikin sanyi bayan kinsan ba lafiya ce dake ba?" Ya fada yana tsaye a kanta, seta miqe zaune tana kallonsa tace
"Dan Allah bacci nakeji ka qyaleni, idan gadon ya maka girma ka kirawo karuwarka ku kwanta tare ni nan ya isheni"
"Kee Umaimah" Khalil ya daka mata tsawar da seda taji wani abu ya tsirga mata kamar zata saki fitsari a inda take,
"Ni kike hadawa da Karuwa? Ni kike kira mazinaci Umaimah kije cewa na kira karuwa mu kwanta saboda baki da mutunci?" Ya fada yana matsota jikinsa har rawa yake saboda tsabar bacin rai, seta shiga jada baya tana girgiza masa kai dan ta tsorata da yanayinsa amma dukda haka shedaniyar zuciyarta bata rusuna ba dakyar ta bude baki muryarta na rawa tace
"Wannan ta dazun wacece? Kuma ai na ganku ta window ka riqe mata hannu sannan kuka shigo ciki kuma da zaka fita ka kulleni a daki, idan ba gurin karuwa ba ina kaje?"
Hannu ya daga da niyyar kai mata mari ya sauke hannun tareda kaiwa iska naushi, yasan idan yace ze dora hannunsa a jikinta tabbas seya mata dukan mutuwa, safa da marwa ya shigayi a dakin, baya so ya bude baki yayi magana dan yasan baze furta Alkhairi ba, a yanda zuciyarsa take tafasa yana iya furta mata duk abinda yazo ransa amma baze yanke hukunci cikin fushi ba, se ya juya ya kalleta ta maqure jikin gado tana raba ido,
Kallonta yayi na wasu sakwanni a ransa tuhumar kansa yakeyi waya aikeshi ya auri wannan yarinyar? Qasa da wata uku ace ya fara fuskantar wadannan tashin hankulan, Amma qaddar ta riga fata.
Dakyar ya hadiye yawu ba tareda ya kalleta ba yace
"Tashi ki hau gado ki kwanta"
"Ni a qasa zan kwant...."
"Na rantse da girman Allah kika bari na tako inda kike Umaimah sena illataki" ya zaburo mata babu shiri ta haye kan gadon zuciyarta ta shiga lugude kamar zata fasa qirjinta ta fito ganin yana cire jallabiyar dake jikinsa, kafin ta samu damar yin wani yunquri ya kashe fitilar dakin ya zama dundum ko tafin hannunta bata iya gani ta shiga laluben inda zata sauka daga gadon damqar da yayi mata ta sakata yin ihu babu shiri, babu tausayi ko lallashin daya sabayi mata ballantana wannan soyayyar me bin jini da jijiya ya shiga sukuwa akanta kamar ya Samu dokin sallah.
Duk ihu da roqon da ta ringa masa beji taba seda yayi mata lilis ya gaji dan kansa kaso hamsin na bacin ransa ya sauka kafin ya tsallaketa ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwan sanyi lokacin ko dan yatsanta bata iya dagawa jikinta ya saki gaba daya banda tana numfashi ma se ace suma tayi.
Wanka yayi ya fito har sannan tana kwance tana jan numfashi dakyar, so take taja abu ta rufe jikinta saboda zazzabin daya mata rigib ga sanyin Ac ya cika dakin amma ta kasa, kukan zuciya take hawaye na zuba ta gefen idonta tana kallonsa ya fito ya saka jallabiyarsa ya kunna fitulu masu sauqin haske ya tayar da sallah beko nuna yasan da zaman ta a dakin ba.