Sashe 208
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A saitin Khalil ta tsayar da idonta se kawai ta fashe da kuka tana cewa "Kasan ina kishinka Khalil me yasa? Me yasa zaka hadani da wata Mace dame na rageka da zakayi mun kishiya Khalil me nayi maka" ta qarasa cikin daga murya tana sake rushewa da kuka.
Halifa ne ya matsa kusada Hajiya qasa qasa yace "Anya Hajia Anty Umaimah bata da motsi a kwakwalwarta nidai ina ga akaita gurin likitan kwakwalwa dan abinda takeyi ya fi kama da na masu motsi a kai"
"Uwarka Aisha gata nan a kusa da kai itace take da motsin kwakwalwa, se kaje ka tono ubanka Ummaru a kabari yazo yayi mata magani" Umaimah ta fada idonta cikin na Halifa babu ko dar da tunanin matsayin uwar tasa da ta zaga a gurinta.
"Umaimah ashe baki da mutunchi har haka? Hajiya Aishar kika ambata kika zaga harda Mijinta da yake kabari saboda ke baki da mutunchi kin kuma zubar da tarbiyyar da muka baki a titi ko kin kyauta nace kin kyauta, ki tashi ki wuce mu koma Asibiti ga motar Ambulance nan sunzo da ita zasu dauke ki" Mama da shigowarta kenan ta fada cikin tsananin fushi tana qarasawa inda take ta kama hannunta. Seta fizge tana cewa
"Wallahi babu inda zani, indai kuma ana son zaman lafiya se dai Khalil ya saki yarinyar nan. Ba'a halicce shi dan kowacce mace ba bayan ni dan haka bazan taba raba shi da wata ba".
"Ke a wa? Yanzu har kin isa mace da zaki tsaya kice baza'ayi miki kishiya ba ko kuwa kenan har wata macece data san ciwon kanta balle tayi kishin mijinta? To bari kiji kishi ba hauka bane idan zaki dawo hankalin ki tun wuri ki dawo saboda kinga ana lallabaki ya saka kike botsarewa ko to daga yau zanga uban da ze sake lallabakin, ki tashi ki wuce muje aure kuma Khalil da Humaira har mutuwa idan yaso baqin ciki ya kashe ki shasha sha mara tunani" Mama ta sake fada a mugun fusace.
Se Umaimah ta miqe tana cewa "ai ko baki fada ba nasan kina baqin ciki da zama na ni kadai a gidan mijina ina yin yanda naga dama bayan ke kina da kishiya dole kiyi murna tunda anyi mun, to wallahi daga ke har ita Hajiyar baku isa ba, naga itama ba ayi mata kishiyar ba shine ni zaku taru ku hada baki ayi mun ko to sedai ya zaba koni ko ita,
Idan kuma ita ya zaba to se na kashe shi in yaso kowa ya rasa"
Mari Mama takai mata kafin ta rufeta da duka tana cewa
"Kaiconki Umaimah kaiconki, wallahi da ba'a gida na haife ki ba tabbas zance ke ba yata bace ba jinina bace dan kaf ahalina dana Ubanki babu me mugun hali wanda be dauki kalmar kisa a bakin komai ba irin ki, kafin ki kashe shi ni gara na miki dukan daze lahantaki Muguwa me baqar zuciya"
"Aa Hajiya ki bari ki dena jifanta da wadannan kalaman yawun uwa kaifi ne dashi akan Da, Ke kuma Umaimah kiyi haquri mu bar komai zuwa safiya in Allah ya kaimu" Hajiya Aisha ta fada tana qoqarin janye Umaiman ai kuw ata hankada ta da yake a bazata abin yazo mata se gata tim a qasa ta bugu da qugunta sosai har seda tayi qara.
"Karki sake tabani munafuka tun farko ai komai yana hannunki da kinso ki gyara da ba'a zo haka ba se yanzu ne zaki ce na bari da safe toh an qi a bari din" Umaimah ta fada tana zarewa Hajiya data zuba mata ido kawai tana kallonta ido.
Khalil kuwa runtse idonsa yayi, Allah kadai yasan irin daci da qunar da zuciyarsa takeyi masa a duk sanda Umaimah ta zagi mahaifiyarsa amma yana danne zuciyarsa ne ya hanata aikata mata abinda take raya masa saboda yana mata uzurin me rangwamen hankali, kishi ya taba mata kwakwalwa qari kuma da cikin da take dauke dashi.
Yasan Umaimah nada kishi amma be zata zata bari hankalinta ya gushe ta ringa abu irin na mahaukata ba akan abinda ita ce silar faruwarsa, meye lefinsa dan yayi aure bayan ita ta bashi qofar na yaje yayin sannan yanzu zatazo tana tambele da rashin hankali har tana iqirarin zata kashe shi?
Hadiye wani abu daya tsaya masa yayi ya bude baki dakyar yana nufar ta yace
"Duk abinda zakiyi Umaimah ni zakiyi wa ni nayi miki laifi karki sake zagin Mahaifiyata ko wani akan wannan abun ina kuma yi miki uzurine kawai saboda halin da kike ciki a yanzu"
"Ni kake yiwa uzuri Khalil? Idan ka sakeyi mun uzuri kai ba dan halak bane, idan baka dauki mataki akaina ba to Aisha da Ummaru shegenka sukayi kai ba dan halak bane
Sannan kace karna sake zaginta ko? (Seta waiwaya ta kalli Hajiya datayi suman zaune tun dazu kawai tana kallon Umaimahn) tace
"Aisha kinci uwarki, Khalil ka tsireni na zageta kayi abinda zakayi"
A mugun fusace Halifa yayi kanta amma se Hajiyar tayi saurin riqe shi tana cewa
"Barta Halifa wannan ba Umaimah bace, na tabbatar idan ba shafar Aljanu ba to ta samu tabin kwakwalwa amma wannan ba Umaimar da muka sani bace"
"Uwarki ce mahaukaciya bani ba" Umaimah ta sake fada kafin ta rufe baki Abba ya kai mata wata mahangurba ba shiri ta durqushe a gurin ko ihu ta kasayi saboda yanda duka ya shigeta .
"Khalil kana tsaye, mace ta zagi uwarka a gabanka kana tsaye baka dauki mataki ba Hajiya ko dai bake kika haifi Khalil ba?" Mama ta fada cikin kidima tana tafa hannaye,
Khalil da idanunsa suka rine zuwa ja jijiyoyin kansa gaba daya sun tashi ya kalli Mama yace
"Mama dagaske wannan ba Umaimah bace, ko dai kwakwalwarta ta tabu ko kuma mugayan Aljanu ne suka shafeta amma kema Mama kinsan wannan ba Umaimah bace, kowa ya sani ina son Umaimah itama tana sona na tabbatar ba a hayyacinta take wadannan abubuwan ba".
"Allah ya wadaran soyayya irin taka Khalil Allah kuma ya wadaran zuciyarka zuciyar da kana tsaye matar aurenka zata zagi uwar data haifeka ka saka mata ido ba tareda ka chanza mata kamanni a bugu daya ba, Umaimah ko dai kin siyar da Imaninki kin bi bokaye ne ban sani ba dan dai wannan yafi kama da zuciyar wanda aka tsafance Dodo ya cinyeta dan Ubanki me kika aikata masa?
Ko da yake ba banza ba, tun tuni ya kamata na fahimci cewar Umaimah kin bar turbar Allah da Annabi amma ban gane, taron qawayen da kullum nake harqilon rabaki dasu inda ya kaiki kenan wayyo Allah na ni Malika ubangiji ka yafe mun ka sassauta mun wannan jarabta da kayi mun da kangararriyar yarinya da take neman kaini kabari" Mama ta fada tana fashe wa da kuka, se ta sake kallon Khalil tace
"Saketa mara zuciya, ka saki Umaimah yanzun nan Khalil"
"Mama mu fara mayar da ita Asibiti a bincika kwakwalwarta, idan basu ga komai ba se mu tafi gurin Malam Ishaq qila a can a dace amma nasan ba yin kan Umaimah bane dole akwai abinda yake zungurinta" Khalil ya fada cikin rawar Murya kamar yanda jikinsa ya dauki rawa lokaci daya.
"Wallahi seka saketa Allah yasa Dawanau ce ita ko kuma kukar bulukiya, kai ko kashin awaki na haife ku yau Khalil seka rabu da Umaimah idan kai baka san darajar kanka ba to ni bazan zuba ido yata ta wulaqanta uwar mijinta ba nima na haifa, na kuma san zafin abinda takeyi idan ni akayiwa bayan saki wallahi se na saka an hada mata dan bura uban duka ta yanda ko akuya bazata sake yiwa tsawa ba bare ta zagi bil'adama" Mama ta sake fada cikin hargagi.
"Ai wallahi ko be saketa ba a yau se Alqali ya kashe auran nan, ni kaina da zan iya canzaki daga cikin Ahalina da a take a yanzu zanyi dan banyiwa iyayena haka ba ban san dalilin da yasa Allah ya jarabce mu da ya irinki ba amma muna roqonsa ya kawo mana dauki" Abba ya fada cikin qololuwar bacin rai.
"Abba Mama dan Allah kuyi haquri, ku bari muga safiyar nayi alqawarin idan har aka tabbatar lafiyar Umaimah qalau a take zan rubuta mata takaddar sakinta" Khalil ya fada yana kallon Hajiyarsu da sigar roqo, Hajiya da kwallar baqin ciki ta zuraro mata ta kauda kai, ta bakin na Mama ne itama ta fara zargin shikansa Khalil din ba kansa daya ba, duk yanda akayi da gaske an bawa Dodo zuciyarsa ya cinye in ba haka ba wannan abu har ina?
Kai da Fata Mama da Abba suka dage se Khalil ya saki Umaimah da tunda tasha marin Abba ta durqushe bata sake dagowa ba saboda wani Azababben ciwon mara da kai da suka dirar mata lokaci daya.
"Shikenan, taje na saketa saki daya" Khalil ya fada kamar wanda ze fashe da kuka.
"Uku zaka mata ka yanke duk wata alaqa da take tsakanin ku yanzun nan" Mama ta sake fada,
"Hajiya dayan ma yayi ba se ya qara ba" Hajiyar su Khalil da tunda ta fadi bata sake magana ba ta fada
"Wallahi se ya qara Hajiya ko beyi uku ba se ya mata biyu" Mama ta sake kafewa dole Khalil ya sake qarawa Umaimah da tayi mutuwar zaune jin wannan Drama da ake tsarawa.
"Durun uwar nan, ka sake ni Khalil a maimakon ka saki wannan Yar iskar daka auro? To wallahi dani da kai da ita sedai duk ayi biyu babu" Umaimah ta fada tana miqewa, dukda azabar da take ji a jikinta da a kwayar idonta ma kana iya karantar halin da take ciki haka ta yunqura, kafin kowa ya ankara ta finciki wani flower vase da yake kusa da ita babu bata lokaci ta saukewa Khalil a daidai Mazantakarsa, ihu daya ya kwalla ya fadi wanwar a gurin.