← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 267

Sashe 6

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari guraren 10 sega Yaya Aminu da sabuwar waya Infinix me kyau ya kawo mata. Ta karba tayi godiya kafin ta kunnata ta jona a chaji ta wuce makaranta dan daman shiri take.
Fix lecture ce ta wani malami da be samu ya gama musu darasin sa ba ga lokacin Exam yayi. Tana shiga Ajin ta hango Rumasa'u da yanzu ko kallon arziqi ba tayiwa inda suke se ta zarce gurin nata dukda su Halima dake mata magana suna nuna mata gurin da suka tanadar mata amma bata kula ba.

Sallama tayi musu ka gaisa da wadanda ke kusa da Ruman kafin ta zauna akan desk din gabanta tace
"Hajiya Ruma fushin ne har yanzu baa sakko ba" dauke kai gefe Ruma tayi tace
"Fushi? Aini ba fushi nake ba Umaimah, buqatata ne bakyayi a cikin rayuwar ki shi yasa na fita na barki da masu hali da ra'ayi irin naki tunda bakya son gaskiya".

"Uhm to yanzu dai ai komai ya wuce, bayan haka fa keda Nabila kukayi cacar baki ba dani ba amma da kika tashi kikayi mana kudin goro gaba daya"

"Ai sanda take zagina ta kirani mayya kurmancewa kikayi da kika kasa magana ko kuwa? Kinga dan Allah matsamun a nan ga malam nan ya shigo" ta qarasa tana janyo littafi daga cikin jakarta.
A kusa da ita Umaimah ta zauna har aka qare lecture din dukda Ruman ba kulata take ba, malamin na fita ta sake kafa mata surutu har seda Rumah ta sakko daga fushin tace mata

"Na haqura amma dai bazan sake jerawa dake ba in dai kina tare da wadancan da basu san ciwon kansu ba" ta fada tana hararar Nabila da tun zaman Umaimah a gun hankalin na kansu.

"Baki haqura ba kenan, itama Nabilan zan mata magana zata baki haquri akan abinda tayi shikenan?"

"Ba shikenan ba, kinsan ni a rayuwa bana jurar wulaqanci bazan tsaya wata banza ta gaya mun magana ko da da nake musu shiru kin sani ba tsoron su nake ba kawaici ne amma yanzu daidai nake da kowacce yarinya a cikin su"

"Ohni Rumah kin zama masifaffiya toh dai dan Allah kiyi haquri" Umaimah ta sake fada
"Shikenan, na haqura"

Da haka suka miqe gaba daya suka nufi qofa. A kusa da su Fauziyya Umaimah ta tsaya tana cewa
"Ku tashi muje mu karbo exam card"

"Yar wulaqanci se yanzu kika san damu bayan kina shigowa muka baki seat amma kika share kikayi tafiyarki abin ki" Fauziyyan ta fada, Nabila kuwa tabe baki tayi suna yar harara da Rumasa'u dake gaisawa da Halima Amarya.

A waje suka zauna saboda Me bayar da Exam card dinbe riga ya qaraso ba,

"Waini meya farune Ruma da Nabila naga se wani fizge fizge kukeyi lafiyar ku kuwa?" Halima ta fada tana kallo su. Fauziyya ce ta labarta mata abinda ya faru tsaf se ta kalle su gaba daya tace

"Ai gaskiya ta fada muku, wallahi Umaimah idan baki canza wannan halin ba babu namijin da ze iya zama dake. Kai gidan aure fa ya wuce duk yanda kuke hasashensa, kunga dai zazzafar soyyar nan da mukayi da Hayati to wallahi ko sati bamu rufa ba muka fara bala'i kawai dan ya bar wayarsa na dauka ina bincike.
Da na zata shwarwarin banzar da muke a nan zasu kawo mun mafita na hau na zauna akai ashe qara tabarbara abubuwa kawai zanyi badan Allah yaso ni Anty Zully tamun orientation ta gayamun gaskiyar abinda yake akwai ba ai inaga da yanzu wani zancen ake ba wannan ba.

Toh wallahi tun wuri in zakuyi hankali kuyi in ba haka ba, jikin yarinya ne ze fada mata"

"Gashi can an bude office din, ku tashi muje" Umaimah ta fada da rashin bama maganar Halima Muhimmanci, suka miqe gaba daya Halima nacewa

"Ina nan da daya da daya zaku same ni, dadina da gobe ai saurin zuwa" suka rankaya office din. Kwankwasawa sukayi aka basu izinin shiga suka tura kai gaba dayan su ciki, mutumin na zaune akan kujerar sa se wani akan kujerun da suke a gefe suna Hira suka shiga Umaimah ce akan gaba tayi sallama karaf idanunsu suka hadu da wanda yake zaune akan Kujerar gefen, kallo daya ta masa ta dauke kai dan vata taba ganin fuskarsa a office dinba is dai idan sabon ma'aikaci ne aka dauka suka qarasa gaban teburin suka gaishe shi ragowan suka waiwaya suka gaida baqon banda Umaimah data kafa kai tana binciko musu Exam cards dinsu a jikinta tana jin ido na yawo akan ta abinda yasa ta ringa sakin gajerun tsaki kenan tana mita a ranta.

Ita ta ringa miqa wa kowa nata suna signing a takaddar dake gefe har suka gama, dake ita ce qarshen fita seda takai bakin qofa kafin ta kalli baqon dake binta da kallo tunda suka shiga ya kasa dauke idonsa akan ta ta maka masa harara qasa qasa tace
"Ayita kallon mutum kamar an bashi ajiya saboda sa ido" tayi waje abinta.

Tsaf ya ji abinda ta fada se kawai yayi murmushi ya kalli abokinsa dake cewa
"Umaimah kenan, sarqa uwar rikici. In kana neman danger wutar baya ka samu yarinyar nan ka gama kawai abokina"

"Allah ko? Ni kuma ta burgeni. Da ace na shirya aure dana gwada sa'a ta dan a kallo daya ta shiga raina kuma tayi dai dai da matar da nake so na aura".

Hannu ya bashi suka tafa yana cewa " Bayero Bayero namu, to ka afka mana, amma fa karka ce ban gaya maka ba zaka sha rikici da ciwon kai a gurin nan kai kuma gaka ba gwanin daukar hayaniya ba"

Murmushi Khalil yayi yace "toh ai hadin shine daidai, idanna dakko mara hayaniya irina ai gidan mu will be boring, gara dai a samu wadda zata ringa mayar dashi lively"

"Hakane, toh Allah ya tabbatar mana da Alkhairi abokina, kace wannan ziyarar bazata da ka kawomun ashe rabone ya kiraka"

"Amin amma da saura, ni yanzu babu ma shirin aure a gabana kasan dai yanda ake lallaba rayuwar ga aiki yaqi samuwa yar buga buga kawai akeyi, qoqari nake na gama hada Masters din nan nayi settling. Akwai abubuwa da yawa danake da buqatar kammalawa kafin na dakkowa kaina maganar aure tunda bazaka dakko yarinyar mutane kazo kana bata wahala ba dole tana da buqatar abubuwan more rayuwa ko yayane a gidan ka" Khalil ya fada.

"Hakane, amma kuma ko a yanzu Bayero ai Alhamdulillah rayuwarka na tafiya daidai zaka iya ajiye iyali, mutum nawa kafin cikin abokan mu da suke aikin abin fa duk intihani ne kawai amma idan kace seka samu yanda kake so zakayi aure zaa dade gaskiya" Nasir ya fada.

Se Khalil ya gyara zaman sa yace
"Hakane nima ba wai ina nufin sena tara kudi zanyi aure ba komai rabo ne a rayuwa, ta yuwu ma naka arziqin seka yi auran zaka same shi amma yanzu Nasir kadai san nauyin gidan mu a kaina yake. Nine ci, sha da suturar mahaifiyata da qannena guda biyu da suke gabanta, kai har masu auran idan suna da wata buqata nifa suke kira ka sani.

Yanzu haka ni ina Masters, ga Jalila nk nake dauke da nauyin karatunta, Halifa bana ze gama secondary ya shiga Jami'a shima ga dai abubuwa nan kala kala babu yanda zaayi yanzu na tattago maganar aure da wadannan nauyin a kaina bayan ba wani kwakwkwaran aiki ne dani ba, bani da muhallin da zan ajiye mace a yanzu, samun nawa na lokacine, se mun samu yar kwangila anyi sannan muke samu, muna dai ta fatan Allah ya buda ya bamu yanda zamuyi tunda dai Allah yaga zuciyar mu".

Numfashi Nasir ya sauke yana kallon abokin nasa da tausayawa, rayuwa kenan. A shekarun baya idan akace akwai wata rana da Khalil Bayero zasu shiga halin da suke ciki a yanzu babu me yarda. Irin gatan da suka tashi a ciki, mahaifinsu tsayayyan mutum me wadata iyalansa su kansu sun shaida tarin Alkahiran sa a rayuwa dan da yawan abokan Khalil da sukayi primary tare ta gomnati lokacin da budi yazowa babansu ya chanza musu makaranta zuwa ta kudi haka ya hada dasu duka ya kaisu ya ringa biya musu kudin makaranta.

Banda Scholarship daya samar musu na fita qasashen waje sukayi karatun degree dinsu gashi yanzu ganiyar sa suke ci, duk kuma abinda suka zama a rayuwa sanadin sa ne.

Bayan rasuwarsa ne abubuwa suka damewa iyalansa, wani amininsa da suke harkar kasuwanci yazo da takaddun da duk me hankalin daya gani yasan na bogi ne akan yana binsa bashin wasu maqudan miliyoyin kudade, ya samu goyon bayan qaninsa da suke uwa daya uba daya wanda ya bada shedar zur a kotu kan Marigayin da bakinsa ya gaya masa cewar akwai bashi tsakaninsa da Alhajin amma kuma babu wanda yasan da hakan ciki harda matarsa da Kuma Khalil din kansa wanda a sannan kusan komai na Mahaifinsu shine akai.

Ansha badaqala musamman da Iyalansa suka kafe akan basu yarda ba, da ace akwai irin wannan magana me muhimmanci da Alhajin ya fada tun yana jinya tunda ba mutuwar fuji'a yayi ba yasha jinya sosai da har seda ya fitar da rai da rayuwa kuma a sannan seda ya fadi duk wani da yake bi bashi ko shi ake binsa amma da yake duniya babu gaskiya, aka je kotun ma suka siye Alqali suna ji suna gani haka suka tattara kudaden daya ce suka bashi wanda seda suka hada da siyar da kadarorinsu kafin suka tada kudin, qarshe gidan da suke ciki kadai suka tsira dashi se wani qarami da suka saka yan haya a ciki. Duniya kenan wata shari'ar se a lahira.

Hira suka taba sosai kafin Khalil yayi masa sallama suka fito ganin dalibai nata zuwa karban exam card zaman shi kuma kamar yana raba masa hankali.

"Ka gaida Hajiya dan Allah, insha Allahu qarshen satin nan zamu shigo da madam tunda sunyi arba'in" Nasir ya fada daidai sanda suka isa inda Khalil ya ajiye Lifan dinsa.

"Aa abokina ina motar ne naganka da Mashin kuma?" Nasir din ya sakw fada.
Chapter 6 · 0% Book details