Sashe 52
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lah na manta ban miki bayanin su ba, wannan Yaya Shafa'atu ce yar gidan Yayan Hajiya da akayi bikinta kwanaki kin tunata? Wannan kuma Yaya Lubna qanwarta ce" Habiba ta fada bayan data Ajiye kofin da tasha ruwa.
"Ayya Amarya sannu ai munso zuwa Allah beyi ba" Umaimah ta fada tana fadada fara'arta, Shafa'atu tayi mata murmushi tace
"Babu komai ai gashi yanzu mu munzo" se Umaiman ta miqe tana cewa
"Kusha ruwa bari na dora abincin rana tana qarayi" se Habiba tabi bayanta tana cewa
"Muje na tayaki Anty". Tare suka shiga kitchen din ta bawa Habiba gyaran Attaruhu da Albasa ita kuma ta fito da Kazar data saka fridge ta shiga ta dora mai.
"Ita dayar bata da aure ne?" Umaimah ta jefawa Habiba dake yanka Albasa tambayar se tayi shiru dan bata tsammaci da ita take ba, seda Umaiman ta sake maimaita mata kafin tace
"Wa? Wai Yaya Lubna? Bata da aure ta tsaya ruwan ido dan da tare zaayi bikinsu da Yaya Shafa'atu aka fasa. Itafa nan a dole da Yaya take so, idan kinga kukan data sha lokacin bikinku se kinci dariya bafa ta zo ba ko yanzu dakyar Hajiya ta sakata ta biyo mu" Habiba ta jerowa mata bayani.
Sakare tayi tana jnta, zafin da taji ya ratsa mata hannu har zuwa cikin kwakwalwarta ya sakata watsar da robar data zuba naman kazar da zata soya. Sam ta manta da ta dora mai tana shirin zubawa ne take tambayar Habiban ta tsoma hannunta bata sani ba.
Da sauri Habiba ta taso ta shiga yi mata sannu da qoqarin riqe hannun da Umaimah keta faman yarfewa saboda Azabar radadi.
"Sannu Anty, kawo a zuba ruwan sanyi Allah yasa karta tashi" Habiba datayi saurin dakko ruwan qanqara ta sakr fada. Se Umaimah ta miqa mata hannun tana sakin kuka kamar wata yar yarinya kukan baqin ciki biyu.
Na farko ga radadin zahiri na qonewar da tayi ga radadin zuciya najin budurwar Mijinta ce tazo mata gida, ai kuwa setaci ubanta seta gaya mata dalilin daya kawota da har ta jawo mata guzurin qonewa, sannan shima ze dawo ya sameta, wato saboda budurwarsa nae har yake cewa taje ta bude suna tsaye a rana ko
Habiba na gama zuba mata ruwan ta fice daga kitchen din dan bata ga ubanda zata girkawa abinci ba kuma, dakinta ta shige Habiba na biye da ita fuskarta dauke da damuwa tace
"Anty kona kira yaya na gaya masa?"
Kallon hannun Umaimah tayi, dukda tana jin radadi a saman yan yatsunta da sukayi jaa amma bata zaton qunar tayi munin da se anje Asibiti musamman da an zuba ruwan sanyi ta tabbatar ze taimaka gurin hana ta tashi seta girgizawa Habiban kai tace
"Aa karki kirashi, kije ki fara girkin ina zuwa" se Habiba ta juya tana qarayi mata sannu ta fita.
Shafa'atu ke tambayarta lafiya ta gaya mata Umaiman ce ta qone seta miqe tana cewa "subhanallahi muje na gani amma bada yawa bane ko?"
"Eh en yatsuntane suka shiga cikin Mai Allah yasa beyi dai zafi sosai ba" tayi gaba ta kwakwasa qofar dakin Umaimah data kwanta shiru zuciyarta na suya, a fusace ta miqe ta bude qofar, suka shiga Shafa'atun ta shigayi mata sannu tana tambayarta ko zasuje Chemist tunda taga wani a kan layin nasu.
"Babu komai fa ai Man beyi zafi sosai ba kuma an zuba ruwan sanyi na kuma tofa Addu'a daman yanzu zan fito na qarasa girkin" Umaimah ta fada tana qaqalo fara'ar dole se Shafa'atu ta tareta da cewa
"Wane irin girki kuma ga Habiba da Lubna nan s su qara sa idan da wani abinda za'a miki ma duk se muyi kafin mu tafi ki zauna ki huta".
Kamar tace wace shegiyar Lubnan ce zata shigar mata kitchen sedai ta danne ta qaqalo murmushi tace
"Aa wallahi zan iya ai ya dena radadi hannun ya za'ayi na saka baqina aiki" ta shiga qoqarin fita daga dakin suka bita a baya Shafa'atun na cewa
"Haba Anty Umainah ai wallahi indai mu zaki dafawa bazakiyi ba gara mu zauna da yunwa idan bazaki barsu suyi ba in kuma na Yaya ne ki gaya masa kawai yayiwo take away ko ya karbo a gidan Hajiya tunda nasan bazeci girkin su ba"
"Kamar ya baze ci girkin mu ba, me kike nufi? Idan da Allah yayi naga girkin wa ze ringaci?" Lubna da bata saka musu baki ba tuntuni ta fada a tsiwace tana kallon Yayarta.
Se Umaimah ta zuba mata ido kawai, badan tana tsoron hukuncin da Khalil ze sake dauka akanta ba da babu abinda ze hanata nadawa wannan yar iskar duka a cikin gidan. Ita mamakin kanta ma take yau da har ta iya tsayawa inuwa daya da yarinyar da ake iqirarin budurwar Mijinta ce koda yake gashi ma ta tabbatar mata ta fada da bakinta.
Tanajin Shafa'atun ta rufeta da fadan bata da kunya ne waye sa'anta a cikinsu Lubna data dauke kai ta harde a kujerar Umaimah ko a jikinta tana danna waya har yayar ta gaji tayi shiru se Umaimah ta saki murmushin takaici tace
"Ki barta ba laifinta bane kinsan quruciya akace dangin hauka gaskiyarki kuma Habibi bazeci jagwalgwalon yara ba sedai su dafa abinsu suci, Habiba kuje Jellop din shinkafa za'ayi se a soya Kazar da akwai ruwan zobo a cikin Fridge se ku hada" ta qarasa tana zama akan Threesitter irin zaman gadarar nan na me abu da abunsa idonta na kan Lubna aika mata da wani mugun kallo daya sakata shan jinin jikinta kuma Umaiman tayi mata kwarjini seta miqe tana zumbura baki tabi bayan Habiba data fice daga palour.
"Kiyi haquri sam Lubna bata da kunya wallahi" Shafa'atu ta fada tana zama itama se Umaimah ta tareta da cewa
"Haba wani haquri kuma quruciyace take damunta muma duk muyi a lokacinmu ai wata rana ai bazatayi ba, naga alamar kishi takeyi dani nayi mata kwacen saurayi ko" ta qarasa tana yar dariyar da duk me fahimta ze gane bata dadi bace, yaqe ne kawai
Gyara zama Shafa'atu tayi tana dariya itama tace
"Tab jifa wata magana kema Anty Umaimah yanzu idan aka ce miki Yaya Khalil ze kula wannan yarinyar seki yarda ai ni inaga magana ma me tsaho bata taba shiga tsakaninsu ba saboda rawar kanta shi kuma kinsan baya shiri da marasa ji, itace dai take haukanta wai sonsa takeyi amma ai bata taba gigin fada a gabansa ba se mu data raina ta ringa wa hauka da Drama lokacin bikinku, ai abun ma ba gaske bane ba kuma me yuwuwa bane shirmenta ne kawai takeyi"
"Uhm Allah sarki" Umaimah ta fada tana shafa yatsunta da har sannan suna mata zafi, hira suka shigayi kadan kadan dan rabin hankalinta naga tausar zuciyarta karta botsare ta sakata yin abin kunya dan dagaske ji tajeyi kamar take kitchen din ta watsawa yar banza man da ta jiyo suna soya kaza idan yaso taga da bakinda zata sake yi mata rashin kunya har tace da Mijinta ne ze aureta.
Acan kitchen kuwa Habiba data gama kwashe Kaza daga Mai ta kashe Gas din ta bude Tukunyar shinkafar ta juya ta qara tabbatar da komai yayi kafun ta rufe ta juya kalli Lubna da tunda suka shiga kitchen din ta samu kujera ta zauna tana danna waya bata tayata da ko tsinke ba, cikin bacin rai tace
"Wai Yaya Lubna me yasa kike haka yanzu saboda Allah kizo har gidan mata ki mata rashin kunya dan kinga tana da haquri wallahi idan wata ce nasan seta kwakwkwada miki mari sedai duk abinda za'ayi ayi kuma yanzun ma idan muka koma sena gayawa Hajiya wallahi"
"Karki kuskura kiyi mun rashin kunya idan bata mare ni ba ni sena mareki a nan banza da tafi son bare akan yar uwarta ta jini. Ni wallahi ma sena raina ta na raina ajin yaya Khalil, ace akan wannan dusar ne duk ya tsallake yammata irin mu ai kuwa ya fado qasa"
"Tab wayaga daskindaridi, wai ke nan kina wa kanki kallon wata hadaddiya ne ko kyakykyawa?" Habiba ta fada tana qunshe dariya kafin taci gaba da cewa
"Ai wallahi idan da Anty Umaimah a guri ko a me goge goge bazakiyi daraja ba, fari ne fa kike taqama dashi shima Allah ne ya taimake ki na rantse da a baqa kika zo se an hada da roqon Allah zaki samu shiga koda yake da farin da komai ma gashi nan har yanzu se a slow, ni wallahi banma ci dariya ba Yaya Lubna se jiya da kika cire wadannan sosunan da kike sakawa Ruler sunan wata aba nace na godewa Allah da Hajiya kullum take jajanta sirantata ashe akwai wanda nafi qiba" Habiba da takai baqin qofa ta qarasa fada
Kukan kura Lubna tayi ta kai mata cafka ta goce suka fita tsakar gidan kafin kace me sun kaure da dambe fuskarta tayi jaa saboda bacin ran wannan cin mutunchi da Habiba tayi mata.
"Kaikai meye haka, baku da hankali ne?" Shafa'atu ta fada tana qoqarin raba su dan daga ciki suka jiyo hargagin Lubnan tana zagin Habiba, qin rabuwa sukayi suka ci gaba da casuwa dan dukda Lubna ta bawa Habiba kusan shekara uku a qirar jiki kusan daya suke koma Habiban ta fita kwari dan haka qarfi yazo daya kowa ta kasa kada yar uwarta.
Umaimah na tsaye akan barander ta harde hannu tana kallonsu kawai, Addu'a take Allah yasa Habiba ta damfarata da qasa dan da alama tana dab da samun nasara akanta dan ta fi Lubna dabarun damben tana kallon shafa'atu nata qoqarin rabasu suka maujeta taja gefe tana sosa inda aka daketa tana zaginsu, Allah ne ya bawa Lubna Sa'a ta tade Habiba ta fadi a qasa ta haye ruwan cikinta tana sakar mata blows a fuska bata ankara ba se ji taji an kwasheta da marin daya gigita mata kwakwalwa kafin taji an watsar da ita gefe ta qume qum da Abin flower.
Daga Habiba Umaimah data zazzabgawa Lubna mari da biyu tayi tana kallon Lubnan tace
"Saboda kin zama babbar banza zaki haye kanta kina duka se kin mata lahani?"