← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 242

Sashe 99

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali ya dawo da kallonsa a saman kirjinta da gabaÉ—aya tudunsu suke a waje saboda yanayin kayan jikinta da yanayin kwanciyar da ta yi. A hankali ya É—an haÉ—iyi yawu kamar wani da ya ga abin kwaÉ—a yi. Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya kai hannunsa jikinta, hannun nasa sai wani kerma yake yi. Wuyar rigar tata ya É—an ja mata sama, sannan ya É—an sunkuyo da kansa a kanta. Sumbata ya manna mata a baki. ÆŠan motsawa ta yi kamar tana san farkawa.

A hanzarce ya miƙe kaman maras gaskiya, da sauri ya nufi switch na ɗakin, kashe mata wutar ɗakin ya yi, da sauri ya fice kamar zai kifa ƙasa. Bai zame ko'ina ba sai cikin motarsa, ko da ya shiga ya kasa jan motar ya tafi, ya ɗauki good 30 mins a wajen yana ƙoƙarin controlling na feeling ɗinsa kafin ya iya driving.

Da kyar ya iya tada motar da gudun gaske ya nufi gate, da yake gate ce mai amfani da na'ura, da kanta ta buÉ—e kanta ya danna waje da gudun gaske. Ammo tana tsaye a windown bedroom É—inta dake fuskantar harabar gidan tana kallansa har ya tafi, sannan ta nufo É—akin baby. Kamar yadda ya barta haka ta sameta, addu'ar barci ta zo ta yi mata dik da tana da yakinin ya yi mata, dan ya saba yi, sai dai bata san yau kansa ya É—auki zafi bai yarda ba ya tafi.

Bayan ta gama yi mata addu'ar ne ta fito ta wuce nata bedroom É—in, ta koma saman bed É—inta ta kwanta cike da tinanika kala kala a ranta.......... ASUBA TA GARI.

🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥

"Haulat bani waje bari in yi magana da ita". Cewar Momma kenan, tana san ganawa da Mahnoor wanda bata yi hakan ba ko sau ɗaya, so yanzu tana san su gana. Zaune suke a bakin bed ita da Mahnoor ɗin, Mahnoor kanta a ƙasa.

Miƙewa mama Haulat ta yi cikin girmamawa ta ansa da to tare da nufar hanyar fita. Har ta kai tsakiyar ɗakin sai ta tsinkayo muryar momma tana faɗin. "Nan da 2 hours ki turo mun Mahreen".

Da okey mama Haulat ta amsa sannan ta fice waje. Dawo da kallanta a kan Mahnoor momma ta yi, hawaye bibbiyu ne a face É—inta, da alama ta tina maraicinta yasa take wannan kuka. Janyota jiki momma ta yi ta hau rarrashinta, cike da kauna ta ce. "Kada ki É—aukeni matsayin sirika, ki É—aukeni matsayin uwa". Ta kai karshen maganar tana goge mata hawaye.

Shiru Mahnoor ta yi tana jinjina halacci irin na momma, zamanta da mama Haulat na satin É—ayan nan har ta koyi wasu abubuwa masu muhimmanci.

"A matsayina na uwa a gareki zan yi maki nasihar zaman gidan miji, ki nitsu ki saurareni da kyau, dan a bisa dokarmu a ɓangaren mijinki zaki kwana yau, nan da sati biyu masu zuwa zamu je jimeta, da naso mu je gobe, amma akwai wasu dalilan da yasa sai next two weeks, akwai saye saye da za'a kawo daga Dubai, sai mun haɗa komai zamu tafi, gobe ya yi kusa".

Jinjina kai Mahnoor ta yi tana sauke ajiyar zuciya, tabbas tana jin momma tamkar mahaifiyarta, tana kaunarta sosai ita ma.

Cikin sanyin murya momma ta fara magana kamar haka. "Ki dage da hakuri da biyayya.
Aure yana buƙatar hakuri da juriya. Ki kasance mai biyayya ga mijinki, kuma ki guji nuna rashin kunya ko rashin girmamawa gare shi. Ki kula da addua da ibada. Ki dage da addu'o'i don neman zaman lafiya da albarka a gidanku. Ibada za ta taimaka muku wajen samun kwanciyar hankali. Ki zama mai tsafta da ƙyalli, Haulat zata koya maki kwalliya sosai. Ki kula da tsaftar jikinki, gidanki, da tufafinki. Mijinki mutum ne mai jin daɗi idan ya ga matar da ke da tsafta kuma tana jan hankalinsa, yana da kyankyani ya tsani ƙazanta, a kan kanwarsa ƴar autarsu ya fahimci hakan, dan in ta yi kwalliya wuni yake yi yana yabonta baya gajiya, so yana san kwalliya sosai. Ki koyi maganar mai daɗi da ta dace da shi, dan yana san magana cikin kulawa. Ki guji faɗar kalamai masu zafi ko cin fuska. Kalaman kirki suna gina soyayya kuma suna rage duk wani rashin fahimta. Kula da sirrin gidanki da mijinki. Kada ki yi gaggawar bayyana matsalolinku na gida ga kowa. Kula da sirrinku zai taimaka wajen magance matsalolin cikin sauƙi. Kauna da kulawa. Dik da nasan yana da wuyar sha'ani kuma zai yi wuyar juyowa gareki, dik da haka ki nuna mashi soyayya da ƙauna, sannan ki kula da dangi da abokan arzikinsa. Wannan zai sa ki samu ƙima a gidansu. Hakuri, hakuri, hakuri, ki kasance mai haƙuri. Komai yawan ƙalubale, haƙuri yana da muhimmanci don magance su. Ki rike ibada sosai. Wannan yana kawo albarka a cikin aure. Kar ki yi gaggawa wajen yanke hukunci idan ya yi maki wani abin. Idan akwai matsala, ki nemi hanya mai kyau don magance ta kamar yin nafilfilin dare dan neman maslaha daga wajen Allah. Ki kasance mai ilmantarwa. Karatu da ilimi suna taimaka miki wajen zama mai cikakken basira a rayuwa. Na faɗa na kara faɗa maki, mijinki yana san kwalliya sosai, sannan na manta ban faɗa maki cewa shi mutum ne mai san zanen lalle a hannun mace ba, ko ni da nike mahaifiyarsa idan na yi lalle ya rinƙa magana kenan, ya kalla ya sake kallah, har hoto yake ɗaukar hannuna, Jaish mutum ne mai san lallaɓawa, tin yana karami haka yake, baya san a ɗaga mashi murya, sannan baya san yana magana ki yi magana, ki kula da wannan, baya san cin abincin a kan lokaci, hakan kada ya ɓata maki rai ki ɓata mashi shi ma, cikin ruwan sanyi da sigar soyayya da lalama zaki koya mashi cin abinci a lokacin da kika yi ra'ayi, yana da zuciya sosai, wannan gado ce, dik suna da zafin zuciya da saurin fushi, idan ransa a ɓace kada ki yi saurin kula shi, ki kyalesa na ɗan lokaci ya sauko, in ba haka ba ba zaku kare da kyau ba".......... Ɗan dakatawa ta yi tana mayar da numfashi.

Mahnoor kuwa ta kasa kunne tana saurari yadda yakamata. Shiru ta É—an tsaya na Æ´an mintuna tana kallan fuskar Mahnoor kafin ta nisa ta É—aura da cewa.

"Kin ji kaɗan daga cikin abin da yake so ta waje, sai ta ciki, ba zan ɓoye maki komai dangane da mijinki ba, saboda yanzu a ƴa na ɗaukeki ba sirika ba, burinmu mu shawo kan mijin naki ne, dole na fayyace maki komai dan mu yi nasara".

Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tana kara kasa kunne ta saurara da kyau, saboda tana bala'in san Jaish, dik abin da zai juyo mata da hankalinsa a kanta to tabbas zata yi shi.

"Mijinki yana da sha'awa mai karfi wanda zance maki dikkansu haka suke, sai ki shirya, amma yana da dauriya sosai, sannan baya san mace mai shigar manyan kaya, i mean matar aurensa, saboda na karancesa sosai a kan hakan, dayawan lokuta yana san sayawa kanwarsa kananan kaya dan yana yi mata kallan yarinya, so yana san shigar manyan kaya, wannan zan sa a yi maki akwati set guda a wajen haÉ—a lefenki, so Haulat zata koya maki yadda zaki yi amfani da su".

Mahnoor da bata san me ma mommar take nufi ba a maganarta ta karshen nan, ai sai amsa mata take yi to kawai kanta a ƙasa.

My people's ku tafawa uwa ta gari, wato dik abin da ƴaƴanta suke yi tana sane tana yin recoding a ƙwaƙwalwarta, ashe ta san Jaish yana san lalle, kun tuna idan ya zo ya samu mama Haulat ta yi mata lalle sai ya yi ta yabawa? Ashe dik tana ganinsa, ashe ta iya karantar abin da yake so da wannan da baya so, gaskiya wannan ita ce uwa ta gari, ba tare da ƴaƴanta sun faɗa mata ga abin da suke so ba ta rigasu sanin abubuwan da suke so, wani lokaci suna son abu basu ma san son shi suke yi ba, amma tsabar kula irin nata ita ta gane hakan, wata uwar ko kasheta zaki yi yanzu ki ce ta kirga maki abubuwa goma da yaronta yafi so ba zata kawo maki su ba, kuma tana sansa ba wai bata sansa ba, wasu ne akwai rashin kula sosai wlh, irinsu ne ƴaƴa su yi ya aikata abubuwa tsabar rashin kula zasu ce basu sani ba, yanzu ku momma bata burgeku ba yadda take zayyano abin da ɗanta tafi so ba tare da shi kansa yasan da yana sansu ba? Abin bai ƙayatar daku ya yi maku daɗi ba? Ki karanci yaronki ki san me yake so ma ke zaki fi kowa jin daɗi da moresa, dan in kika san me yafiso fa wlh dik in da zai je sai ya dawo wajenki, dan zai ga kamar dik duniya ke kaɗai ce kika iya fahimtar kika sansa sosai. So yana da kyau dikkan mata su yi koyi da halin momma, ita ake cewa uwa ta gari wlh. Daga karshe Allah ka haɗamu da iyayen miji na gari irin momma.

(Amma fa momma ta gama kwancewa Jaish namu na amana zani a kasuwa😅 zata sa Mahnoor ta raina shi😅🥱)
Chapter 99 · 0% Book details