← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 242

Sashe 41

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Hoorain ne ma, dan wannan irin abu haka ba zai taɓa zama waninsa bane, shi ɗin ne!! Tab akwai matsala, kenan Hoorain dama Queen Zarina yake yi wa aiki? Menene yasa ya ci amanar kingdom of power har da mahaifinsa haka? Kenan ya zaɓi wasu a kan mahaifinsa? Ya aka yi Zarina ta san Hoorain? Tin yaushe ya fara yi mata aiki? Aiya mahaifinsa ma zai iya kasancewa abin yarda kuwa? Anya shi ma ba maciyi amana bane kuwa? Kada ku manta a baya alkalamin princess Teema taku ta amana na gaya maku cewa bayan mammiensu Sarina akwai waɗan da suke cin amanar Kingdom of power suke aiki da Queen Zarina, kuma mutane da suke da kusanci sosai da King Zuhair, yardaddunsa ne, in baku manta ba na taɓa faɗa maku zaku sha mamaki a lokacin da gaskiyar zata bayyana, zaku sha mamaki idan kuka gane maciya amanar kingdom of power, ku dai muje zuwa, akwai tashin kai a gaba.

________________________________🔥

Yana tsaye ne tamkar wanda aka sassaƙa, dik da yana cikin hular mayaƙa, hakan ba zai hana ka fahimci babu rahama da imani a tattare da shi ba.

Cike da izza da zallar madarar zalinci Queen Zarina take basu umarnin kalar kisar da take da buƙata zasu yi wa kingdom of power, har da cewa su ɗauko mata Jaish su kawo mata shi, dan a duniya idan akwai wanda take so to ya biyo bayan Jaish yaro ɗan Mommarsa, dan haka a kashe kowa a ɗauko mata Jaish, a shekaru fa ta kai ta haifi Jaish, amma kuma zuciyarta ta kamu da kaunarsa dan tabbatar matacciyar zuciya.

Allah sarki yaro É—an Mommarsa, yana can yana sha'aninsa ana mutuwa a kansa bai da labari.

Cikin girmamawa waɗan nan bakaken azzaluman mayaƙan nata suke karɓar umarninta, zaluncin mutanen nan ya kai su iya zaro jariri daga cikin uwarsa su kashe shi su jefar da gawar babu abin da ya damesu, basu da tausayi ko ɗigo a ransu, ko da yake zukatan da ake sarrafawa da tsafi yaushe suka ga imani da tausayi?.

Akwai cakwakiya, King Zuhair ya bada umarni ga mayakansa da su je su ruguje Daular Qahtaniyawa su kashe kowa su haÉ—o mashi kan mayakansu da bayinsu su zo su zama bayi a kingdom of power ba tare da ya tabbatar da cewa King Al-Mustapah ne ya É—auki Zunaira ko ba shi bane, kawai ya yanke hukunci cikin fushi babu bincike. Ita kuma Queen Zarina ta bada umarnin a zo a kashe mata kowa a Kingdom of power a kama Jaish a kai mata shi su yi aure. Me kuke tinanin zai faru?.

A gefe guda kuma evil kingdom suna can suna ta gagatumin shirin da idan suka dinfari kingdom of power dole su rugujeta su shafeta a doran duniya, wani irin mummunar kafurin shiri suke shiryawa.

Ga shi shi kuma King Zuhair yaki yarda ya karɓi tuban King Al-Mustapah bare ma har su haɗa kai wajen ganin bayan Queen Zarina da su King Abdul Aziz, shi kaɗai kuma ni da ku mun san wlh ba zai iya yin faɗa da waɗan nan masarautu har ukun ba, ga ubansu Black Tiger a gefe, wanda shi tuni ya shirya aje a durkusar mashi da kingdom of power a kawo mashi King Zuhair gabansa ya zo ya yi mashi sujjada ya lashi kafafunsa, batun fitarsa fada ya dakatar da shegun wayakan Robbot ɗinsa ba su afka kingdom of power ba, amma yana nan da shirin a ransa, kuma zasu aiwatar, yanzu so yake ya shiga fada.

Hankalinsa ta É—an kwanta, ya nitsu, bayan haka ya É—auki mataki a kan Sweetie, idan ta bashi Spender sai su ruguje kingdom of power, wannan ne shirinsa a yanzu.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Yau hospital cike yake da ahalin King, Jawad da bai san Jaish ya dawo ba yana hospital zaune kusa da gadan da aka bawa Chuchu, su uncle Taheer dik suna cikin hospital É—in.

Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsu a cikin asibitin, sai dai da ya tambayi me yake faruwa? Basu faɗa mashi Zunaira ta ɓata ba, sai suka ce mashi rashin lafiya ne na guyson da Chuchu.

Ya yarda da hakan, dan haka ya je ya duba jikin Chuchu kafin ya fito ya nufi É—akin da guyson yake kwance. Bawan Allah tamkar babu rai a jikinsa.

Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsa a haka, sai ya yi tunanin ko ciwonsa ne ya tashi, dan haka sai ya yi mashi addu'a sosai tare da tofa mashi, sannan ya fito ya shiga wajen su Khadija.

Harda mai keken napep É—in nasu dik aka taho da shi, idan baku manta ba na faÉ—a maku shi ma É—an arewa ne, É—an Kano ne, so da su uncle Jahiz aka ce masu babu kowa nashi da ya zo, sai suka haÉ—a da shi kawai suka kawo su ana jinyarsu.

Dik wannan bidiri da ake yi fa Sarina da Mammiensu suna part É—insu hankalinsu a kwance suna shabgar gabansu, sai kulla wani minahincin suke ta faman yi, da alama wannan karan mugu mugun abu Mammie take shiryawa wannan ahali!!.

Dai'dai lokacin da uncle Jahiz ya sako kafarsa cikin É—akin dai'dai wannan lokacin Zee ta fara motsi numfashinta yana fita da karfi karfi.

A hanzarce ya ƙariso gaban bed ɗin nata, ɗakinta daban da na Khadija, iya kaɗai ne nan.

Ganin tana buƙatar taimakon likitoci ne yasa uncle Jahiz ya yi saurin juyawa ya je ya kira likita.

Oxygen suka zo suka sanya mata dan numfashinta ya dai'dai, a saman kujerar da aka tanada dan masu jinya uncle Jahiz ya zauna yana tinanin ina ahalin su Zee suke?.

Tsananin tausayinsu ne ya kama shi sosai.

Oh ta ko'ina ba sauki fa, to bari dai mu leƙa Dubai muga me ake ciki ne wai!.

•••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••••🔥

Tuni Ramish ya miƙawa jami'ansa Leesharh, dama sun jima suna neman kamata, sai yau dubunta ya cika. Sai dai fa ni da ku dik munsan halin Leesharh da ɗan banzan taurin kai, yadda aka rinƙa fama da ita a court ta yi magana lokacin da ta kashe mamarta ta ki buɗe baki ta yi magana haka yanzu ma ta yi.

Dik wani azabtarwa sun yi mata amma taki ta yi magana, har ya kai ya kawo bata iya takawa da kafafunta saboda azabtarwa Ramish, amma dik da haka taki basu haÉ—in kai, daga karshe ma da suka matsa mata sai ce masu ta yi dan Allah su kasheta kawai ta huta, dan ita dai bata ma san a kan me suke tukumarta ba.

Wannan magana ya matuƙar konawa Ramish rai da har yasa bindiga zai harbeta ɗin da gaske, Bilal ya dakatar da shi ta hanyar kwace bindigar ya ce dan Allah Ramish ya barshi da case ɗin a hannunsa, zai sakata ta yi bayani cikin ruwan sanyi, Ramish zafin zuciyarsa ta yi yawa, abu kaɗan ya hasala, dan haka ya bar mashi case ɗin kawai.

My people's kun yarda Ramish ya barwa Bilal wannan case ɗin? Kada ku manta Leesharh ta ce ta taɓa ganin Bilal a gidan masu nikaf, sannan kada ku manta Bilal shi ya fara nunawa Leesharh kauna da tausayawa a gidan, meyasa Bilal ya hana Ramish ya kasheta? Kai bari dai na barku haka kada masoya Bilal su yi mun zanga zanga, amma dai bani na faɗa ba, Leesharh ce ta ce ta taɓa ganinsa a gidan masu nikaf, dan haka dole mu zargesa!!.

Tsabar rainin wayo irin na Leesharh ma, har da ce masu ita fa wannan ba wayarta bace, kuma bata san a kan me ma suke magana ba.

Wato masu nijaf sai da suka yi binciken wacece Leesharh kafin su bata wannan aiki, irin wannan taurin kai haka? Dama irinta Æ´an ta'addan suke so.

Ramish bai so barinta a raye ba, amma Bilal ya ja shi suka bar É—akin da ake horata a ciki É—in, sai daÉ—in baki da kalamai masu daÉ—i Bilal yake yi mashi dan zuciyarsa ta huce ya mance da batun Leesharh.

Yasan wanenen Ramish sarai, yasan idan ransa ya ɓaci ya ce zai yanke hukunci a kan abu to fa sai ya yi, shiyasa yake mashi daɗin baki dan ya mance da komai.

(Ni kuwa nace da a yadda yake cikin ɓacin rai yanzun nan King ya yi mashi waya ya ce an sace Zunaira mana😂 me kuke tunanin zai faru?🤔 Tab na yi nan babu ruwana😂🥱)

A can gefe kuwa, wuni kuka kwana kuka Sharifat take yi, ta gama shiga tashin hankali da damuwa, Allah sarki, tana kaunar Leesharh tamkar ranta, bata taɓa zaton cin amana daga gareta ba, yau tsawon kwana uku tana kuka a kan rashin Leesharh, har ƴar rama ta yi.

Abu Abdussalam ya yi rarrashi har ya gaji, shi ma Leesharh ta kariyar mashi da zuciya, ya ji baya san sake jawo wani jikinsa kuma, hakika ya shiga tashin hankali.

Ita kuwa Ummie, wlh ranta fes, sai addu'a ma take yi Allah yasa Ramish ya kashe Leesharh kowa ma ya huta.

Ramish da kansa ya yi wa Leesharh azabar da sai da ta zaɓi mutuwa a kansa, irin azaban da yake ganawa manyan ƴan ta'adda da jami'ansa idan suka yi laifi ya rinƙa gana mata, amma Leesharh ta daure ta shanye wannan dukka.

Ko sa yake ai ta saba da wahala tun da ta yi zaman gidan AAJ, yarinyar da ake tuhuma da kashe mahaifiyarta ai kunga dole ma zata yi fin hakan.

Hmmmm wato fa Dubai ma ta kama da wuta, ta ko'ina dai ba sauki, to bari dai mu leƙa France muga ko da ɗan sauki sauki can.

•••••••••••••••••FRANCE••••••••••••••••🔥

Sosai Smart ya sha barcin na good 4 hours, sannan ya farka. Misa call ɗin mom ya kai 10 a wayarsa, sai kiransa take yi yaki ɗagawa, da ƙoƙari irin nata wai so take yi ya zo su yi bankwana da iyayen Heleena zasu koma England, har suka tafi ba'a samu ya ɗaga call ba.
Chapter 41 · 0% Book details