← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 242

Sashe 149

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ta bakanta mashi rai, domin waɗan nan chemical ɗin suna da wahalar samu, shiyasa ma ya ɓoyesu a gida, wannan ɗan kaɗan ɗin da ta zubar mashi millions of dollars yake, chemical ne mai haɗarin gaske na haɗa nuclear mai karfi sosai, yanzu haka gabaɗaya ya tsastsaga mata kafa, saboda sake shi da ta yi ya faɗi ƙasa ya ɗan taɓa ƴan kafafunta.

Jininta a kafa ne ya fara zuba, lokaci guda ta sandare kamar wadda lantarki ya busar. Siririn tsaki ya ja ya rasa me É—aya zai fara yi?. Daga bayansa muryar Auta ta katse shi da cewa. "Yah Omerish kaga Pretty? Yanzu na je É—aki ban ganta ba". Da yake ya bawa kofar shigo baya ita kuma Pretty tana kwance a kirjinsa sai yasa Auta bata iya gane Pretty na É—akin ba.

Ya lura da akwai shakuwa sosai a tsakanin Auta da Pretty, dan haka sai ya ce mata. "Jeki parlour ina zuwa". Ya yi mata hakan ne dan kada ta ga gawar Pretty hankalinta ya tashi, dama daga jiya zuwa yau ya fahimci tana cikin damuwa, daren jiya da ya dawo ya shiga bedroom É—insu, a nan ya sameta tana sambatu cikin barci, yau da safe kuma kafin ya shiga wanka sai da ya tsaya a jikin window É—insa ya zuba mata idanu tana zaune wajen dolphins, dama ya sa a ransa yau idan ya dawo daga office ya je ainahin gidansu ya dawo zai tambayeta me yake faruwa?.

Juyawa Auta ta yi ta fita hankalinta bai kai kan jinin kafar Pretty dake malale a kasa ba. Tana fita ya raba jikinsa da nata, da hannu É—aya ya É—agata izuwa balconynsa, saman É—aya daga cikin kujerun dake wajen ya kwantar da ita.

Ita kuwa Auta parlour ta koma ta zauna tare da buga tagumi tana jiransa. A gurguje ya fito daga cikin bedroom ɗin nasa, rufe kofar ya yi dan ma kada ta Autar ta shiga taga gawar Pretty, bai tsaya bi ta kanta ba ya nufi waje yana ce mata yana zuwa. Ta yi mamakin ganin yadda yake tafiya tamkar zai haɗa da gudu, amma bata kawo wani mummunar tinani a ranta ba, tana san tambayarsa ya ga Pretty, sai dai kafin ta buɗi baki tuni ya sauka ƙasa.

Shiru ta yi tana tinanin ina Pretty ta shiga kuma?. Can kunnuwarta suka tsinkayo mata wayar dake ruri a waje. Da sauri ta miƙe ta nufi waje. Filin dolphins ɗinta ta koma, wayar natan ne dai yake ruri. Tana zuwa ta ɗauka, guyson ne yake kiranta, a hanzarce ta yi picking tare da kara wayar a kunnenta tana faɗin.
"Hello Yah Omar". A maimakon ta ji voice ɗinsa sai jin muryar Hoorain ta yi ya amsa mata da Hoonaira. Ai bata san lokacin da ta zube ƙasa a wajen ba, tamkar zata kurma ihu saboda daɗi, har ta rasa abin faɗe ma.

Shi kuwa yana kwance a kan gadan jinya, da shi da Abbonsa dik suna gadan jinya, gara Abbonsa ma ya É—an samu lafiya, ya farfaÉ—o yana iya gane waÉ—an da suke kansa. Shi kuwa Hoorain yana gab da mutuwa King ya samu labarin daga bakin masu tsaronsa cewa Hoorain zai iya rasa ransa a kowani lokaci daga yanzu, hakan yasa King ya ce a fitar da shi a kaisa hospital. Time da aka fitar da shi ranga ranga aka wuce da shi hospital, baya iya taka kafafunsa ma, sai É—aga shi warriors suka yi. Jiya aka fitar da shi, yanzu a can guyson ya je ya kai mashi waya ba tare da sanin King ba.

Wai me ya faru a kingdom of power bayan tafiyar Smart ne?.

Cikin bedroom É—insa King ya nufa hankalinsa a tashe. Shi kuma Smart kai tsaye babban gate na kingdom É—in ya nufa. Sun zo dai'dai wani waje dake kusa da fadar King ta biyu, idan baku manta ba na faÉ—a a baya fada gudu biyu ne a kingdom of power, so King baya amfani da É—ayan, saboda ainahi na mahaifinsa King Abdul Malik ne, to fadoji a da suna haÉ—e ne, sai ka shiga ta cikin É—aya zaka je É—aya, bayan hauwar King Zuhair mulki sai ya rabasu, aka toshe kofar tsakiyar aka buÉ—ewa kowanne nasa kofar yana cin gashin kansa.

So sun zo giftawa ta dai'dai wannan fada na King Abdul Malik wani irin haske ne ya bayyana daga cikin fadar ya shiga cikin motar tasu, sarai Smart ya ga hakan, amma hankalinsa ta yi gaba wajen tuƙi, bai wani bi ta kan hasken ba, ita kuma Auta dama ta kifa kanta a kan gwiwowinta tana kuka, Pretty dake zaune kusa da ita a kanta wannan haske ya sauƙa, dama saboda ita ya fito, saboda Spender dake tattare da ita, dik yadda aka yi da akwai alakar Spender da wannan fada, ina ga yana daga cikin dalilin dayasa King Zuhair ya rufe fadar ƙin faɗawa mutane gaskiya ya yi, dik yadda aka yi akwai abin da ake ɓoyewa, amma lokaci zai warware mana komai.

Ba iya haske ne kawai ya fita daga cikin wannan fada ba, akwai abubuwa da dama da suka nuna alamar bayyanar Spender a wajen. Sai dai da yake Smart da gudu suka gifta wajen sai basu ga komai ba bayan wannan haske.

Akka dake cikin bedroom ɗinta tana kwance sai da ta zabura ta miƙe zaune a lokacin da su Pretty suka gifta wannan fada, a jikinta ta ji hakan, take ta ji jiri na ɗibarta, jikinta ne ya fara tsuma. A lokacin su uncle Abbas sun koma part ɗinsu. Wayarta Akka ta ɗauko, number King Zuhair ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin suna tsaye a tsakiyar bedroom shi da momma suna ƙoƙari neman Smart dan ya dawo.

Muryar Akka na kermar ta ce. "Zuhair dik yadda aka yi Spender ya dawo cikin Masarautar nan, ku yi gaggawar gano in da yake". Yadda take magana ya yi matuƙar ɗaga hankalin King, a hanzarce ya ce mata. "Ki kwantar da hankalinki Akka dole nema mu nemosa, gani nan zuwa kin ji?".

Da okey ta amsa mashi kafin ta katse kiran, hankalinta ya yi matuƙar tashi, dik yadda aka yi Spender abu ne mai tsananin haɗarin gaske kuma barazana ne ga al'umma shiyasa take shiga damuwa sosai,!.

Kingdom of power dai ya rikice.

A ɓangaren su Mammie kuwa, kuri da cika baki ta rinƙa yi a kan wlh ba zata kyale Smart ba, sai ta ɗauki mummunar mataki a kansa, dan haka dole su fara gagarumin shiri, ta yi rantsuwa da Allah ba zai daki Sarina a banza ba, uncle Abbas dai shiru ya yi yana jin surutan nata ba tare da ya ce uppan ba.

Ɓangaren su Khadija kuwa, ita dai Khadijah tana cigaba da kula da babynta babu wani damuwa abinta, yaro sai kara wayo yake yi yana rikiɗewa yana komawa jinin Akka sak, dik yadda aka yi akwai alaƙa ta jini tsakanin yaron nan da Abdul Malik family.

Ita kuwa Zee tana nan da wannan hali nata, ta koma bedroom É—in mama Haulat a part É—in Jaish da kwana, dan ta yi fushi ta sallami part É—in surukarta mama, ta fa kamu da san Dr Raj, amma ta tsani uwarsa, kai wato akwai dirama a gaba fa.

Ita ma Fanan ta koma bedroom É—aya a part É—in Jaish ba tare da sanin momma ko yarjewarta ba, shi ma Jaish bai sani na, shi yana can ma garden a can ya kwana, yaki dawowa part É—insa, wai baya san kwata kwata su haÉ—u da momma dan tabbatar rashin kunya.

A ɓangaren shi kuwa Jawad yau kwanan zaune ya yi yana rarrashi, ita dai ta ce ba zata zauna da shi ba, sai dai kuma bata da kafar tafiya wajen mummyn nata. A can kuma mummyn nata tana can tana faman sallar dare tana rokan Allah da ya rabata da shaiɗanin da yake ƙoƙarin ruɗar zuciyarta dan kawai Smart ya bayyana a matsayin ɗan kin, shaiɗan na san ruɗarta a in da take ta jin rashin daɗin bayyanar nasa, ance zuciya bata da kashi, haka ne kuwa, domin kuwa ga shi nan dai mummy ma shaiɗan nasan kai ta ya barota, tsawon shekaru yana zaune da kowa da zuciya ɗaya da amana, bata ɗauki duniya da zafi ba, yanzu kawai abu na neman birkice mata.

Sai addu'a take yi tana karatun Alqur'ani mai girma, to fans É—inta sai ku tayata da addu'a kada shaiÉ—an ya yi galaba a kanta.

Idan muka waiwaya ɓangaren Mahnoor kuwa, momma ta kira wayat Jaish har ta gaji ya ki ɗagawa, dan a cewarsa bai san me zai ce mata ba ɗan albarka. Haka momma ta tsaya Dr ɗinta mace ta yi wa Mahnoor dik abin da ya dace, ta kuma bata magunguna da suka dace sannan ta tafi, baiwar Allah ta ga bone ita kam.

Ita kuwa Mahreen sai dai shirin Allah, dan kuwa a cikin dressing room na momma ta laɓe tana ganin su Omaid suka rinƙa jigila da guyson suna ƙoƙarin gyara ɓarnar da suka aita. Da kyar suka samu suka iya cire mashi dafin kunamar, amma ya sha kuka kam, dik abin da suke yi a kan idanun Mahreen suke yinsa, a ranta take cewa. "Wannan Yah Omar ɗin dai an yi rago, kannen nasa ma sun fishi jarumta, sai ka zauna kana kukan ciwo dan wauta?".

Daga gefe can kuma uncle Jahiz ne ya je neman Zee a part É—in mama bayan ya baro bedroom na Akka, dan ba zai iya barci ba sai ya sanyata a idanunsa, ya kamu da zazzafar soyayyarta ne da alama. Da ya je bai ganta ba sai ya tambayi Khadijah ina take?! Nan take faÉ—a mashi ai bata nan. Bai kawo a ransa matsala suka samu da Aneesa ba, yasa hannu ya É—auki babyn Khadija ya nufi waje da shi, Allah ya gani yana kaunar yaron nan over, kamar shi ya haifesa haka yake jinsa.
Chapter 149 · 0% Book details