← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 222 OF 242

Sashe 222

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ƙoƙari haɗa kalmomu dake kama da mutuwa a cikin zuciyarsa yake yi dan ya fitar da kalmar da Smart ya faɗa ba mutuwa ba, wai irin zai ce wata kalma mai kama da mutu kenan sai ya ce haka Smart yake son cewa ya manta ya ce mutuwa. Da haka suka isa gida, tin bai gana kashe motar ba Smart ya fito ya buɗe gidan baya, ko kaɗan bai bi ta kan Leesharh ba ya ɗauki Auta ya nufi cikin gida kamar gidansa.

A gaggauce Ramish ya kashe motar ya bi bayansa, ita ma Leesharh da gudu ta rufa masu baya. A parlour saman kujera ya shinfiɗe Auta, sannan ya ciro wayarsa ya dannawa number Zash kira, yana ɗagawa ya ce mashi. "Mun iso everything is ready". Yana kai karshen maganar ya katse kiran. Dai'dai lokacin Ramish ya shigo ciki, har tsoron sake tambayar yayan nasa yake yi, dan zuciyarsa ba zata iya ɗaukar jaddada mashi mutuwar Auta ba, a bakin kofa ya tsaya ya ƙasa ƙarisowa ciki.

Binsa da kallo mai ɗauke da fassara kala kala Smart ya yi kafin ya ce. "Zoka zauna mu yi magana akwai in da nike san zuwa". Kai ya ɗan girgiza yana kallon gawar Auta ya sake kallan Smart, alamar ba zai iya ƙarisowa ciki ba. Nisawa Smart ya ɗan yi kafin ya ce. "Zunaira bata mutu ba, shikenan zo ka zauna".

Wani irin dogon numfashi da Ramish ya ja tare da dafe saitin zuciyarsa shi zai tabbatar maka da suna bala'in kaunar Auta fiye da kawunansu, sonta a cikin jinin jikinsu yake!!. A hankali ya karisa ya zauna kusa da ita, dai'dai lokacin ita ma Leesharh ta shigo.

"Zunaira bata mutu ba, ta shiga doguwar suma ne, Zash zai kawo likitocin da zasu lura da ita, zan barta a nan a hannunka, ka bata kulawa sosai wanda nasan ba sai na faÉ—a maka ba zaka yi hakan, kada ka bari kowa yasan tana raye, ina san dad ya É—anÉ—ani azabar da ta ji a zuciyarta lokacin da ya yi mata sanadiyar mutuwar wanda take so, ko mijin nata kada ka bari yasan tana raye, zamu bari a matsayin ta mutu, sai ta samu lafiya sosai, idan tana san zama da Abdussalam É—in sai a barsu, idan kuma bata so sai a raba auren". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kanta. Yau tin da ya É—aura idanunsa a kan Ramish yake yi mashi wani irin kammani kamar Hoorain haka! Shi da yake yasan kamannin Hoorain tin yana Paris, akwai hotunansa ma dayawa a wayarsa wanda shi Hoorain É—in yake turawa Auta a lokacin da suke soyayya!.

"Yah Omerish amma me yake faruwa ne? Dama bata san Abdussalam ɗin ne aka yi auren?". Ramish ya tambaya!. Jinjina mashi kai Smart ya yi kafin ya faɗa mashi dik abubuwan da suka faru na yadda King ya hanata Hoorain har hakan ya yi sanadiyar mutuwar Hoorain ɗin, da ta ji Hoorain ɗin ya mutu shi ne ta shiga doguwar sumar nan! Sosai Ramish ya ji ɗacin abin da dad ɗin nasu ya yi, tsabar ɓacin rai bai san lokacin da ya ce. "To shi dad ɗin akwai wanda ya taɓa hanashi san ransa ne? Amma me Hoorain ya yi mashi bayan soyayya da Zunaira? Hukuncin ya yi tsauri".

Kai tsaye Smart ya ce. "I think Hoorain ɗansa ne ko kuma suna da wani kwakkwarar alaƙa a tsakaninsu"............ Wata uwar zabura Ramish ya yi, with harsh voice ya ce. "Ɗansa kuma? How comes?".......... Dan furzar da iska mai tsananin zafi daga bakinsa Smart ya yi kafin ya ce. "Dik ajiye waɗan nan batutuwa, yanzu dai zan turo jami'ai guda goma su yi tsaron gidan nan, zan turo wasu biyu daban kuma su yi tsaron Zunaira sosai, ban yarda a bata komai daga wani waje ba ba tare da sanin jami'an dana wakilta ba, ban yarda ta ci wani abinci ba face wanda waɗan nan jami'ai zasu girka mata, sannan su zasu rinƙa yi mata komai, kai dai ka saka idanu a kansu, kuma zata so ganinka a kusa da ita. Idan na gama bincike a kan koma menene you will get the result, maybe zan dawo gareku cikin satin nan, maybe kuma zan iya fin hakan".

Tashin sense, shiru Ramish ya yi yana mamakin abubuwan da suka faru, wannan wace iriyar musifa ce? Ya jefawa kansa tambayar. Zuba mashi idanu Smart ya yi yana kallan face É—insa, dik yadda aka yi Smart yana hasashen Ramish É—an waye, tausayinsa ne sosai ya kama shi, ya zai ji idan aka toni asalinsa? Gaskiya King bai yi mashi adalci ba sam sam.

"Don't trust anybody my brother, idan da dama kanka ma kada ka yarda da shi gabaÉ—aya, ka kula sosai". Cewar Ramish.............Jin jina kai Ramish ya yi kafin ya ce. "Yah Omerish ina jin kamar Raj ba kanina bane, saboda abubuwan da suka faru".

Tausayinsa ne ya sake kama Smart, kamar kuwa yasan gaskiya. "Kaninka ne, ka dai'na barin shaiÉ—an yana sanya maka banzan tinani a ranka, keep praying, everything will came and end"........ Shiru ya É—an yi, shi kaÉ—ai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa. Smart zai sake yin magana idanunsa suka sauka a kan Leesharh dake manne da jikin bango tana binsu da kallo. ÆŠan zaro idanu Smart ya yi, saboda tsantsar kamanninta da Zash da ya gani, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa.

Dai'dai lokacin Zash ɗin ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama, ga wasu shahararrun Drs guda uku biye da shi a baya. Miƙewa tsaye Ramish ya yi yana faɗin. "Zash wanene ya faɗa maka ina nan?". Harara ya wurga mashi kafin ya ce. "Awww our bro ka ɗauka sai ka faɗa mun in da kake ko?". Ɗan ɗaure fuska ya yi tare da cewa. "Stop please, wai ya aka yi kasan gidana?"....... "Kana mamaki ne?". Smart ya katsesu. Da sauri Ramish ya juyo da kallonsa a kan Smart ɗin. "E Yah Omerish, friend ɗina ne fa, kuma ni ban taɓa zuwa da shi nan ba, ban san ya aka yi yasan nan ba".

Miƙewa tsaye Smart ya yi. "Ni na turo shi wajenka domin in san dikkan ƴan uwana, ba jami'i kasa da kai bane kamar yadda kake tunani, shi bama SWAT bane, ya shiga jikinka ne kawai bisa umarnina, assistant ɗina ne a wajen aiki, jajirtaccen jami'i fiye da tinaninka, yanzu kuma ni na ce ya zo nan da Drs dan su duba Zunaira".

Mamaki ne ya kama Ramish, dama ya yi mamaki a lokacin da Zash ya shiga hukumar SWAT, dan da kallo É—aya ya yi mashi yasan wannan kwararren jami'i ne sosai, amma sai ya bar abin a ransa, suka cigaba da kasancewa a tare, ashe kuwa hakan ce, jami'i ne. Yana can yana mamaki har su Drs sun dukufa a kan Auta dan jadada aikinsu. Smart bai jira ba ya wuce haÉ—e da yi masu sallama, haka ya zo ya wuce Leesharh ba tare da ya sake É—aga idanu ya kalleta ba. Mayar da hankalinsu su Ramish suka yi kan samawa Auta lafiya, babu wanda ya damu ko ya mayar da hankali kan kamannin Leesharh da Zash bare har su yi bincike!!.

A can kingdom of power kuwa, lokacin da King ya tabbatar da Zunaira fa mutuwa ta yi ta bakin Jaish, wlh yanke jiki ya yi ya faÉ—i, sai dai suka kwashesa zuwa hospital, doguwar suma ya yi, sai da ya shafe kwana biyu a sume likitoci suna ta kokarin a kansa, daga bisani aka dawo jinyarsa a gida bayan ya farfaÉ—o, sai da ya É—auki good 3 weeks yana jinya, baya furta komai sai dai ya yi ta binsu da kallo, kuma dik da haka bai yi danasanin hana aurenta da Hoorain da ya yi ba, ya dai yi fatan da wani take so ba Hoorain ba ba shakka da zai bata shi ko da ba jinin sarauta bane, Hoorain ne dai baya kaunar haÉ—a jini da shi.

Momma bata san Auta ta rasu ba, sun ɓoye mata, ko da ta dawo daga Dubai sai ce mata suka yi tana wajen uncle Muhammad na France, wato daddyn Smart kenan, hakan yasa bata wani damu ba. King dai ya sha jinya, dan wlh har Auta ta farfaɗo ta fara samun lafiya sosai shi bai koma dai'dai ba, kuma kusan kamar commander ya zama, dan wani lokaci sai ya rinƙa magana kamar Auta tana kusa da shi, kamar yana tare da ita suna hira. Abin ya tada hankula matuƙa, yanzu uncle Abbas shi ne yake kula da mulkin kingdom of power, King yana jinya.

Gudun kada guyson ya samu taɓin hankali yasa Smart ya sanar da shi Auta bata mutu ba tana raye, ya kuma sanya Ramish ya haɗasu suka ga juna, ranan sun sha kuka sosai, tin da Auta ta farfaɗo bata yi magana ba sai ranar da guyson ya zo wajenta, a nan ne ta yi magana, ta yi kuka, ta kuma yi wa Hoorain addu'a, daga nan Ramish ya ce tun da ana hutun school a bar guyson ya kasance a tare da ita, dan a dalilin zuwansa wajenta sauki ya kara samuwa har tana magana, Smart ya yi na'am da hakan, shi kuma yana kingdom of power, rashin lafiyar da King yake ciki yasa bai tada balli a kan amsoshin da yake so ba, ya ɗaga kafa zuwa dad ɗin nasa ya samu lafiya.

RAMADAN KAREEM!!.

Ana gobe za'a ɗauki azumi, sai shirye shirye ake ta yi na tarar wata mai falala mai albarka, unexpected Smart ya ga diran mom ɗinsa a kingdom of power, ta ce ba zata iya zama ba tare da shi bane, tin da yaki dawowa shi ne ta biyo bayansa, ya ji matuƙar daɗin ganinta, ya kuma jin babu daɗi yadda ya bari ta yi kewarsa, matar da tin da ya taso fara'a kawai yake gani a face ɗinta, ta so shi fiye da yadda take san kanta, macen kirki adala, ya yi mata addu'ar samun haihuwa sau ba iyaka, ya ji dama ace yana da damar sama mata aihuwa da sai ta gaji da ƴaƴa.
Chapter 222 · 0% Book details