← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 242

Sashe 104

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wanka a Musulunci yana da matakai daban daban bisa ga dalilin yin sa. Wankan Haila wanka ne da mace take yi bayan gama al'ada domin komawa cikin tsarki. Ga yadda zaku yi shi. Abu na farko niyya, a zuciya ki yi niyyar wanke jikinki daga haila zuwa tsarkin. Sannan sai bisimillah. Ki ambaci sunan Allah Idan ba a cikin banɗaki kike ba, dan ba'a ambatar sunan Allah a waje mai najasa, so in dai a ɓanɗaki ne no need for bismillah. Abu na uku wanke hannaye, ku wanke hannayenku sau uku. Abu na huɗu alwala. Ku yi alwala kamar yadda ake yi don sallah. Na biyar wanke kai. Ku jika gashin kai da ruwa sosai har ya gama jika. Abu na shidda shi ne wanke jiki gabaɗaya. Ki fara daga gefen dama, sannan ki wanke gefen hagu. Bayan kin kammala wankar zaki iya shafa sabulu mai kamshi ko turare a gefe gefen gabanki don kawar da warin haila. Ku lura da kyau wajen wanke gashin nan, Idan mace tana da gashin da ke tattare, ma'ana ta tsefe kai, to dole ta tabbatar da ruwa ya isa har fatar kanta, kunga kuwa sai ta jiƙa gashin sosai, a wannan gaɓar ana samun matsalar fahimta, wasu suna cewa sai mace ta tsefe kai zata yi wankar haila, to ingantaccen magana ba gashin kanta ake san ruwan ya taɓa ba, fatar kanta ake san ruwan ya jiƙa wanda idan bata tsefe kai bama tabbas sai ruwa ya fi shiga fatarta, dan haka ku lura da wannan".

Tin da momma ta fara magana dik suka wani yi ƙasa da kai suna sauraronta da kyau, sai satar kallan Mahnoor Chuchu take yi, taga kyakkyawa ƴar gayu kamar ita.

Cigaba momma ta yi da cewa. "Wannan shi ne wankar haila cikakke, shi kuma wankan janaba ana yin sa ne bayan saduwa ko mafarki (nocturnal emission.) Yana daidai da wankan haila, sai dai ba dole ba ne mace ta yi amfani da turare bayan sa. Shima matakan yinsa gasu nan kamar haka. Niyya, bisimillah, wanke hannaye sau uku, wanke al'aura, yin alwala, jika gashin kai da ruwa, wanke jiki gabaÉ—aya, wannan shi ne wankar janaba".

Shiru suka yi, gara mah Mahnoor ta daure ta ce da momma sun gode. Ina fatan ba iya su Mahnoor bane kawai suka ilmantu da ilimin alkalamina? Allah ka kara mana ilimi mai albarka mai amfani ka sakawa iyayenmu da suka tsaya mana wajen ganin mun samu ilimi ingantacce wanda har jama'a suna ilmantuwa daga garemu, a koda yaushe ba zan gaji da cewa ku mun addu'a kowace iriya ce in dai na alkhairi ce a gareni ina kauna kuma zan ji daÉ—i sannan ina godiya Allah ya bar kauna, ni ko baki kaunata ma ki daure ki mun addu'ar alkhairi please.

Chuchu ce ta tambayi momma wacece Mahnoor?. Cikin nitsuwa momma ta fayyace mata ita tsab, sannan ta É—aura da cewa tana fatan zasu haÉ—a kai tamkar yadda Jawad da Jaish suke tamkar twins.

Riko hannun Mahnoor Chuchu ta yi, fuska É—auke da fara'a ta ce. "In Sha Allah momma muma zamu kasance tamkar twins kamar dai su Yah Jawad.

Sosai momma ta ji daɗin furucin Chuchu, miƙewa ta yi ta nufi toilet tana faɗin bari ta yi wanka tana zuwa. Tana shiga toilet Chuchu ta dawo da kallanta a kan Mahnoor.

"Ina fatan zaki É—aukeni kamar twins sis É—inki?". Ta tambaya tana kallanta. Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tare da cewa In Sha Allah sun zama Æ´an uwa. ÆŠan rungumeta Chuchu ta yi tana faÉ—in. "Gaskiya kina da kyau sosai".

ÆŠan siririn murmushi Mahnoor ta saki kafin ta amsa mata da. "Kema kyakkyawa ce sosai ai".

Sallamar Jawad ya katse masu hirar tasu. Da sauri Chuchu ta dawo da kallonta a kansa. Ganin shi ne yasa ta yi saurin sakin Mahnoor ta tafi da gudu ta faÉ—a jikinsa tana murmushi. Rungumeta ya yi yana faÉ—in. "Shi ne aka barni aka zo wajen momma ko?".

"Kai Yah Jawad, yanzu fa nazo kuma momma É—in ce ta kirani". Jinjina kai ya yi kafin ya ce. "Nima momma É—in ce ta tura mun text a kan inzo, ina take?". "Ta shiga wanka, Yah Jawad ga matar Yah Jaish fa". Ta yi maganar tana É—an raba jikinta da nasa.

Kai kallansa a kan Mahnoor ya yi, maganganun sirrin da suka yi da momma ɗazun ne kawai ya faɗo mashi a ransa, ƙaƙalo siririn murmushi ya yi ya sakar mata kafin ya ce. "Sannunki".

Kasa ta yi da kai tana É—aga mashi gaisuwa cikin girmamawa. Chuchu sarkin iya soyayya sai ta ce. "Mahnoor kin ji momma ta ce mu zama kamar twin irin Yah Jawad da Yah Jaish ko?". GyaÉ—a mata kai Mahnoor ta yi alamar e ba tare da ta yi magana ba.

"To wannan shi ne Yah Jawad É—in da ake magana a kansa, shi ne twins É—in mijinki, kuma shi ne mijina ni". ....... Dogon hancinta Jawad ya ja, kasa kaÉ—an ya yi da murya kafin ya ce. "Da gaske ni mijinki ne my Jannawad?". Ya yi maganar yana É—aga mata gera guda.
Dukan wasa ta kai mashi a kirji tana faÉ—in. "A'a ba kai bane". Hannun nata ya riko. "Sarkin rigima, zo mu je ki bani abinci yunwa nike ji".

"Ka manta momma ta ce ka zo ne?". Ɗan jinjina kai ya yi. "Yeah na manta ne, to bari in jirata". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta suka koma saman sofa suka zauna. Shigewa jikinsa ta yi ta hau bawa flowers ɗinta ruwa. Sai datar kallansu Mahnoor take yi tana ayyana irin haka zasu yi da Jaish ɗinta idan ya fara sonta. Lokaci guda ta tina lokacin da suke Jimeta suke soyayya a gonar bappa, gabanta ne y faɗi dik sai ta ji babu daɗi.

Jawad da Chuchu basu ji kunyarta ba suka cigaba da zuba soyayyarsu har momma ta fito daga wanka. Umarni ta ti wa Jawad a kan shi da Jaish su sameta a part na King nan da 20 mins. To okey ya amsa mata sannan ya miƙe ya fita.

Dawo da kallanta a kan su Chuchu ta yi, ku shirya mu je wajen daddynku ko?. Ta yi maganar tare da wucewa dressing room ɗinta. Tana shiga mama Haulat ta shigo ya kawowa Mahnoor alkyabbarta, ita kuma Chuchu ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsu dan ta shirya da wuri.

After some minutes, gabaÉ—aya sun hallara a gaban King, wato da Chuchu, Jawad, Jaish and Mahnoor. A nan ne momma ta sanar da Jaish wacece Mahnoor, ta kuma ce mashi ta bashi ita amana, ya sani marainiyace, kada ya yi abu domin ita mommar, dik abin da zai yi ya yi domin Allah y kuma duba maraicin yarinyar nan.

Kunsan mutumin da kunya, dik abin da momma take faÉ—a yana jinta amma ya sunkuyar da kansa kasa kamar babu shi a cikin É—akin. HaÉ—esu ta yi ta yi masu nasiha mai ratsa zuciya, ta tunatar dasu girman Allah, ta kuma tunatar da su cewa aure sunana ne na manzan Allah wanda ya fi kowani sunna girma da kima, ta kara jaddawa Jaish da ya kula da Mahnoor tsakaninsa da Allah, daga karshe ta rufe da cewa su wuce bedroom É—insu da matansu.

Sai da ta gama maganarta tsab sannan King ya É—aura nasa shi ma, cikin nitsuwa ya yi masu nasiha shi ma haÉ—e da karfafa masu gwiwa ya kuma ja kunnen Chuchu da Mahnoor a kan su yi wa mazansu biyayya, daga karshe shi ma ya rufe da su tashi su wuce bedroom É—insu.

Miƙewa Jawad da Jaish suka yi a tare, suka wuce gaba Chuchu da Mahnoor suka rufa masu baya. Suna tafiya King ya dubi momma dake zaune a bakin bed ɗinsa. "Na bawa matar Jaish kwautan kujerun makka guda biyar, idan kin je Jimeta ki sanar da iyayenta da wanda ta zaɓa su shirya bana su je Makkah, sannan ina da special kyauta a gareta a matsayina na mahaifi a gareta, akwai kyautar gaisheni da ta zo ta yi zan bata sai kun dawo daga Jimeta".

Matsawa momma ta yi jikinsa, ta kwantosa tana zuba mashi godiya, kamar jira dama yake yi haba ai sai ya fara al'amura.

🔥🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥🔥

Cike da tashin hankali Abbie ya bi bayan Ummie dan ya dakatar da ita daga aikata kudurinta. Sai dai ina kafin ya fito parlourn har ta fice. Cikin zafa ya taka da sauri sauri ya bi bayanta. Tana cab zata shiga part É—in su Ramish ya kwala kiran sunanta. Tana jin ya kirata ta yi saurin rugawa ta afaka cikin part É—in su Ramish. Allah sarki dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, sai ya ji kamar in da yake tsaye ta yi wani irin juyawa da karfi, nan take ya ji kamar zai faÉ—i.

Dafe bango ya yi ya fara bin jikinta ya juya izuwa part ɗinsa. Ita kuwa Ummie, sai da ta shiga cikin part ɗinsu sai ta rasa me zata ce masu ne ma, ta ce su zo suga ta kama Abbie da wata mace nan kuma Ramish ya dallah mata mari kafin ya yi yunƙurin zuwa, dan tasan halinsu sarai, to ya zata yi ta ja su izuwa part ɗin Abbie su ganewa kansu? Ta jefawa kanta tambayar.

Tana tsaye a tsakiyar parlourn tana tunane tunane sai ga Ramish and Bilal sun fito a lokaci guda, suna shirye cikin arabs jallabiya zasu tafi musque. Sun É—an yi mamakin ganinta a part É—insu da asuba haka, Ramish dai ya yi kamar bai ganta ba ya zo zai wuceta, Bilal ne ya tsaya tambayarta me take yi a nan?.

Dai'dai lokacin su Dr Raj ma suka fito da sauri, suma tsayuwa suka yi dan ganinta a nan. Tashin hankali ne ya bayyana a tattare da ita, kame kame ta fara yi masu, can kuma wani idea ya faÉ—o mata, da sauri ta ce masu su je part É—in Abbi yana nemansu abu ne na gaggawa.
Chapter 104 · 0% Book details