Sashe 162
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kunsan a kauye haka suke cewa idan suna faÉ—a, sai su ce waye uban mutun da zai dakesu ba zasu rama ba? So kalaman bala'inta na kauye ta yi amfani da shi a kan Sarina, dan ita bata É—auka ma wani kalmar azo a gani bane, kawai faÉ—arsu na yara take faÉ—en hakan, ita kuwa Sarina wani irin mugun zafi kalmar ta yi mata, wai waye ubanta, lallai yana da kyau ta gwada mata uban nata kuwa.
A fusace ta cakumo wuyar kayan barcin jikinta da nufin ta naɗa mata ɗan banzan duka, to kun san a ɓangaren faɗa kam dai su Sarina kifin rijiya ne, babu wayon faɗa, basu iya faɗa da hannu ba dan ba yi suke yi ba, a barsu dai da faɗa da baki nan suka fi kauri, ita kuwa Mahreen ta yi dambe da mazan kauye ma bare wata Sarina, dan haka tana cakumo mata wuyar riga Mahreen ta yi kasa kamar wadda zata yi sujjada kawai ta finciko kafar Sarina da karfi, kan kace me sai ga Sarina ta zube ƙasa wanwar kafafu a buɗe, ɗaya ya yi can ɗaya ya yi can.
Tana ganin ta faɗi kasa ta yi gaggawar haye ruwan cikinta, yadda dai ta yi wa ƴaƴan ɓoɗejo bogaza, haka ta haye kan Sarina ta hau kai mata duka a kirji kan tula tulanta. Ba shiri Sarina ta fara ihun neman taimako, yau ga wadda ta fita hau ai.
Ai tana wannan ihu kamar tana kara ingiza Mahreen ne, hular kayan barcin dake kanta Mahreen ɗin ta ciro ta cusawa Sarina a cikin bakinta da ta wage take ihun, wai dan ma kada ta tara mata jama'ar gidan bata gama cin ubanta ba a zo a rabasu, dama Sarina ba karfi ba, yanzu kuma ga rashin lafiyar dukan da tasha bata gama warwarewa ba, hakan yasa ta gaza iya kwatar kanta, Mahreen ta rinƙa kaiwa tula tula naushi abinta, ga shi ta tura mata hula a cikin baki ba halin yin ihu.
A dai'dai wannan lokacin guyson ya zo giftawa zai je part na Mommarsa dan yaga Mahreen É—in, yau throughout basu haÉ—u ba, ya je school, bayan ya dawo kuma yana tare da uncle Jahiz, yana san uncle É—in nasa sosai dan yana da ra'ayi a kan kwallan kafa sosai, so ita zai je gani, har yau wajen da kunama ta harbesa tana É—an yi mashi zafi kaÉ—an kaÉ—an. Amma ya rufawa su Omaid asiri bai sanar da kowa abin da ya faru ba.
Ai yana ga abin da yake kafuwa a miliyan ya kariso wajen, yana zuwa bai yi wata wata ba yasa hannu ya ɗagata cak ya sauketa daga kan Sarina. Kun san faɗarta baya karewa, da gudu ta yunƙura zata sake haye Sarina ya yi gaggawar ƙanƙameta yana tambayar me yake faruwa?. Ƙoƙarin kwatar kanta ta yi da ta cigaba da jibgar Sarina tana wani huci kamar wadda ita aka jibga, sai dai ina ta ƙasa kwace kanta, kuma da hannu ɗaya ya riketa, hakan zai tabbatar maku ba wai karfi ne bashi da shi ba, shi dai kawai goyon kaka ne.
"Lafiya meya haÉ—aki faÉ—a da Aunty Sarina a cikin wannan dare kuma?". Cikin wannan sanyin nasa ya yi maganar. Ganin ta kasa kwace kanta ne yasa ta ce. "Ni ka sakeni in gamasa cin ubanta". ÆŠan zaro idanu ya yi yana mamakin kalamanta, ya ma rasa me zai ce.
Ita kuwa Sarina lallaɓawa ta yi ta miƙe tsaye, har wani tangal tangal take yi kamar zata faɗi. Hular da Mahreen ta tiɗɗa mata a cikin bakinta ta zaro shi tare da harbin Mahreen ɗin da shi, a fusace ta ce. "Yau sai na ga waye gatanki, sai naga waye ubanki a ƙasar nan, sai kin yabawa aya zaƙinta........".
Ai Sarina bata gama rufe baki ba ta wani daka sufa zata yi kanta tana faÉ—in. "Sai dai ubanki ba nawa ba, shegiya mai kama da akuyoyin Nenne, kuma tun da kika zagi bappana wlh sai na cire maki hakwaran sama". Wato dai kowa yana san iyayesa kuma babu daÉ—i idan aka zagan makasu, amma kuma kai a lokacin da zaka zagi wani ba zaka ji rashin daÉ—in yin hakan ba sai an rama ne zaka san iyaye suna da daraja kuma kana sansu, ita fa ta fara zagin uban Sarina, amma yanzu kun ji da Sarina ta rama shikenan abu yazama laifi an zagi bappanta ba zata bari ba, har da zubar da hakwaran Sarina zata yi, kai Mahreen duniya.
Ƙanƙameta da kyau guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Ki natsu mun in ji me ya haɗaku faɗa".
Juyo da idanunta kansa ta yi, cike da rashin kunya ta yi mashi kallan uku saura kwata kafin ta ce. "Ji yadda yake magana kamar wani babban mutun bayan kai mai kukan ciwo ne kawai, kai da rarrashinka ake yi kamar karamin yaro ne zaka ce zaka raba faÉ—a? Kai fa zan iya zaneka ka yi kuka". Babbar magana!!.
Bawan Allah a maimakon ya ji zafin kalamanta sai ma ya saki cool murmushi kafin ya ce. "To na ji zaki iya zaneni, yanzu dai muje part É—in momma sai ki zaneni a can".
Sarina kuwa hannu ta kai zata kai mata capka ya yi saurin janyeta daga tsakaninsu shi ya shiga tsakanin nasu yana rike da hannunta, a natse ya ce. "Aunty Sarina dan Allah kiyi hakuri, kada ki biye mata, baki ga yarinya bace?". ..... Ai bai gama rufe baki ba ta sake yin tsalle ta dire haÉ—e da cewa. "Wlh ni ba yarinya bace, kuma ma ai na fika tun da ni bana kukan ciwo".
Sarina kuwa, dama zata yi magana da ya yi magana ne, amma jin Mahreen ta capki zancen tana jajjaga mashi masifa yasa ta haɗiye maganarta tana huci. Shi dai har yanzu ko kaɗan kalamanta basu wani taɓa shi ba bare har su ɓata mashi rai, kara burgesa ma take daɗa yi, dan haka bai kulata ba ya sake duban Sarina ya ce. "Aunty Sarina dan Allah ki yi hakuri kin ji?".
Sarina na ƙoƙarin cewa ya kyaleta ta taka Mahreen yadda yakamata ko zuciyarta ya huce, sai Mahreen ɗin ta rigata da cewa. "Kada ta yi hakuri, ta zo ta lililili ta likeni ta zurani ta bakin allura ta sake fitarwa karshen kenan idan ta isah"...... Yau dai guyson yaga ta kansa, ana ƙoƙarin kashe wuta ita kuma tana kara hurata. Sake kaimata wawura Sarina ta yi ya yi saurin janyeta, ita kuma ana janyeta tana wani matsowa zata kaiwa Sarina duka har da wani dunkule hannu wai ita nan jaruma, sai wani kyafta idanu take yi.
Guyson dai da yaga wannan abin fa ba karewa zai yi ba sai ya shammaceta ya ɗauketa cak yana bawa Sarina hakuri ya nufi part ɗin Momma, rai a ɓace Sarina ta ce wlh ba zata kyaleta ba, sai dai kada su haɗu, in suka haɗu sai ta fasa mata baki, ita kuwa Mahreen ya ɗauketa ma bakin bai mutu ba, faɗi take. "Wooooo ƙatuwar banza ta sha duka, kuma na daki banza ba yadda zaki yi".
Kai Mahreen sai shirin Allah.
Bai sauketa a ko'ina ba sai a tsakiyar bedroom na momma, babu kowa a ɗakin sai Mahnoor dake kwance saman bed tana barci, momma taki yarda ta matsa ko nan da can, ta ce a gadanta zata rinƙa kwana tun da ba a nan King yake kwana idan yana ɗakinta ba, gadanta ne ita kaɗai, so Mahnoor zata iya kwana a kai, tun Mahnoor na noƙewa har ya saki jiki ta ɗauki momma matsayin uwa kawai.
Yana sauketa ta riko waist ɗinta da hannu dikka biyu tana binsa da wani irin kallo. Ɗan sunkuyar da kansa ƙasa ya yi alamar kunya da kamala kafin ya ce. "To sarkin faɗa kallan me ni kuma kike mun? Ko dai kina duba ta in da zaki ɗauki fansa a jikina ne dan na hanaki yin faɗa?"....... Kai ta ɗan girgiza mashi alamar a'a, sannan ta ce. "Ina mamaki ne". Ɗago da kallansa a kanta ya yi kafin ya ce. "Mamakin menene kuma?". Ɗan nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Ashe kana da karfa fa? Ban yi zatan kana da karfi ba ai, kuma da kake maganar ɗaukar fansa ai ko zan ɗauki fansa a kan kowa ban da Hammana (Jaish) da mai kama da shi, kana kama da Hamma shiyasa idan ka rabamu faɗa da mutane bana komawa kanka da faɗar".
Siririn murmushi ya saki har sai da dimple É—insa suka lotsa, sannan ya ce. "To nagode da nike cin darajar kamannina da Yah Jaish nike tsira daga dukanki, amma in tambayeki mana?"........... Tsaresa da ido ta yi alamar tana jinsa ba tare da ta yi magana ba........ "Meyasa kike san yin faÉ—a ne?". Shi ne tambayar da ya jefa mata.
Kai ta ɗan ɗaga sama kamar mai tunanin wani abin, can ta sauko da kallanta a kansa, ya yi shiru yana jiran amsa..... "Idan aka taɓoni ne bana iya bari, yanzu ma ban yafewa wannan mai kama da akuyoyin Nenne ɗin ba, dik ranar da muka sake haɗuwa sai na cire mata hakwaran sama dikka".
Shi dai yarintarta da shiriritarta dik yana burgesa, ga shegen san kwalliyar nan nata yasa ya kara jinta a ransa, dan shi ma kamar yadda yake É—an wanka haka yake san Æ´an gayu, bare ita da take caras cas, ga kyau da kirar jiki mai kyau, dik kalar wankar da zata É—auka kyau take yi sosai.
"Please ki dai'na faɗar nan haka ya isa kin ji?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar yana kallan janbakinta da ya ɓata mata gefe gefen baki saboda faɗar da suka gwabza.
"Ni ba zan dai'na yin faɗa ba matsawar za'a rinƙa shiga gonata". Cikin tsiwa ta yi maganar......... Girgiza kai kawai ya yi, sannan ya matsa kusa da ita dab, ya kai hannunsa saman lips ɗinta domin ya gyara mata jan bakin ba...... A miliyan ta ja baya kaɗan tana faɗin. "Kai ma na lura ɗan iska ne mai san taɓa jikin mata, yanzu ka ɗaukeni ban yi maka wata magana ba na yafe maka shi ne har ka samu damar taɓa mun baki ko?".