← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 242

Sashe 62

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin gani ko ranki ya daÉ—e? Dan Allah ki nitsu sai ki fahimtar dani a kan me kike magana? Ban gane me kike faÉ—e ba, ni ban sanki da hayaniya da faÉ—a ba, dan Allah kada ki sauya mun, ki yi hakuri ki fahimtar dani komai, ki faÉ—a mun meya kawoki nan kika jefani cikin tashin hankali tsawon wata da kwanaki ina nemanki?".

Tin da ya fara magana idanunta suke a saman face É—insa dik da a rufe take, wani irin kara É—aure fuska sosai ta yi, cikin zafa ta ce. "Ka sake Ni!!".

"Idan na sakeki zaki iya fama ciwonki ne". A sanyaye ya faÉ—a............."To idan na fama ina ruwanka? Kai da kaso kasheni me zai dameka dan na fama ciwona a gabanka? Jikinka ne ko nawa?".

Idan hankalinsa ya kai miliyan to a yanzu ya tashi, dan yaga bil hakki da gaske take yi, bai san meyasa take cewa shi da ya so kasheta ba, shi bai san komai a kan abin da take faÉ—e ba, tana ta jefashi cikin ruÉ—ani... TO FAH, ME KUKE TINANI MY PEOPLE'S? TO IDAN BA SHI YA KASHETA BA WAYE YA YI HAKAN? MUJE DAI ZUWA.

"Nace ka sake ni ko?!". Cikin ɗaga murya ta yi maganar, hakan yasa ya yi saurin saketa, saboda bai taɓa jin ta ɗauki zafi haka ba.

Da kyar ta iya tsayawa a kan kafafunta, sannan ta raɓa gefena zata wuce. Da sauri ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta, cikin nitsuwa ya fara jero maganganu masu zafi kamar haka.
"Ban san laifin me nayi maki da har na cancanci irin wannan hukunci daga gareki ba, amma dai koma menene ina mai neman afuwa da ki yafe mun, kuma ina neman alfarma, ko da ba zaki sake yi mun magana ba, kai ko da ba zaki sake buƙatar ganin face ɗina a rayuwarki ba, dan Allah ki bani damar na mayar dake gida, dan hankalin kowa a tashe yake, kowa kukan rashinki yake yi, dan Allah ki saurareni, ni ban ma buƙaci jin laifin me nayi maki ba, ni dai kawai na karɓi laifin koma menene, ina neman afuwa".

Kin saurarensa ta yi, ta raɓa gefensa ta wuce tana rike da hannun Pretty, a fili ta furta......... "Sai dai na mutu a wannan dajin da na yarda da kai, gara yunwa da kishin ruwa su kasheni da na bika da sunan ka mayar da ni gida". Kun san modarawa da balai'n zuciya, to ita ma Auta ta gado, ta fusata ba sassauci.

Dafe kansa dake yi mashi tsananin ciwo ya yi, ya sha bakar wahala tsawon kwanaki 35 yana nemanta, daga gari har daji, wani maharbi ne ma da suka haɗu a cikin gari sai ya nuna mashi hotonta ya tambaye shi, shi ne ya ce tabbas ya taɓa ganin kamar ita a bakin ruwa cikin wannan dajin, dalilin da yasa ya shigo nemanta kenan, ya shafi kwanaki 20 ciff a cikin wannan dajin yana nemanta, sai yau Allah ya yi ya ganta, amma taki ta bashi dama ta saurare shi.

Miƙewa tsaye ya yi, dik jikinsa ta mutu, ba abin da yake damunsa a zuciyarsa ma kamar yadda take ta ikirarin shi ya kasheta, to shi a yaushe ya kasheta? Wata ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da. "Ko dai kin bayyana mata soyayyarta da ka yi ne yasa take ikirarin ka kasheta, kila hakance ta cutar da zuciyarta har take gaba da kai".

Tuna hakan yasa ya yi saurin bin bayansu. Can ya iskosu suna san tsallaka wani ruwan dake gudu mai ɗan girma, ba zasu iya tsallakawa ba sai sun shiga su wuce, to suna tsoron shiga kada ace wajen yana da zurfi, Auta tana dafe da cikinta, ita kuma Pretty tana ƙoƙarin samo itace su sanya a cikin ruwan dan su gwada zurfin ruwan.

Gabanta ya kariso ya tsaya, cikin girmamawa ya ce. "Dan Allah ranki ya daÉ—e ki bani dama, dan Allah ki tsaya ki saurareni, kada ki yanke hukunci cikin fushi, tuba nike yi, nasanki da hakuri da juriya game da yafiya, dan Allah ki yi hakuri kin ji?".

"Okey kasanni da hakuri shiyasa ka kasheni dan kana ganin zan yafe maka ko?". Ta gefa mashi tambayar tana kawar da kallanta daga kansa, bata san sake ganin face É—insa.

"Wlh ranki ya daɗe ni ban kasheni ba, ban taɓa tinanin dede da second ɗaya na cutar dake ba, bani da burin da ya wuce in ganki a cikin farinciki, please ki saurareni".

"Amma kuma dik da san farincikina da kake yi hakan bai hanaka caka mun wuƙa a ciki ba ko?". A fusace ta yi maganar!.

Wani irin zaro idanu ya yi, sai a yanzu ya yi magana cikin É—aga murya.

"What!!!! Wuƙa a ciki kuma? Ni na caka maki wuka?". Cike da tashin hankali ya yi tambayar......... Ɗan siririn tsaki ta ja tare da juya mashi baya dan bata bukatar sake yin magana da shi.

To fa!! Wannan lamari akwai sarkakiya sosai wlh.

"Ban gane ni na caka maki wuka a ciki ba? Ki mun bayani".......... Yadda ya yi maganar sai da yasa ta yi saurin juyowa garesa, ko da wasa bata taɓa jin sautin muryar a haka ba, Allah sarki wato koma dai menene akwai tsantsar sansa a ranta har yanzu, tabbas ba bawa yake sanya kansa son wani a ransa ba, dan kuwa da mutum yake sanyawa kansa da Auta ta cire son Hoorain daga cikin zuciyarta.

Ganin yadda tashin hankali ya bayyana a tattare da shi ne yasa ta ji yana da kyau ta sauraresa, dan kuwa alamu sun nuna kamar akwai wani abin........... Cikin nitsuwa ta bashi labarin yadda aka yi ya kasheta tsab, yadda suka haÉ—u a bayan part É—in uncle Abbas da komai da komai har yadda ya caka mata wuka a ciki tana kallon kwayar idanunsa.

Ita dai Pretty ta yi tsaye hannunta rike da sanda tana kallansu....... Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hoorain bai san lokacin da ya zube gwiwowinsa a ƙasa ba, wani irin sara mashi ya ji kansa ta yi, da kyar ya fara maimaita kalmar innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil. Sai da ya maimaita sama da sau hamsin durkushe a wajen, ya kasa ɗago kai ya kalleta ma, idanunsa sun rikiɗe sun yi jakir gwanin ban tsoro, alamar ran maza ya ɓaci.

Ganin ya durkushe ƙasa ya sunkuyar da kai yasa Auta ta juya zata bar wajen. Cikin Zafa ya kai hannu ya riko hannunta. Da sauri ta juyo da kallanta a kansa.

Can ƙasa ƙasa ta tsinkayo muryarsa yana faɗin. "Bani bane, bani bane ranki ya daɗe, wlh bani bane, tabbas nayi waya dake, kuma tabbas kin ce mu haɗu a bayan part ɗin uncle Abbas a wancan ranar, kuma tabbas na je wajen, amma ko da naje ban sameki ba, na ɗauki good 1h a wajen, shiru baki zo ba, ni kuma ban san ya zan yi ba sai kawai na koma ɗaki na kwanta, tin da na kwanta barci ya ɗaukeni, lokacin da na farka kuma sai na ji gabaɗaya gida ya rikice ana nemanki, na tambayi su Ansar, sune suke bani labarin wai an saceki, dalilin barina masarauta na fito nemanki kenan, dan ina ganin dik waɗanda zasu je nemanki ɓata lokaci kawai zasu yi, ina ganin kamar ina fita zan ganki, na sha wahala wajen nemanki, dan Allah ki yarda dani".

Tin da ya fara magana idanunta a kan face É—insa, tsantsar gaskiya ce kawai take fitowa daga bakinsa, magana babu in'ina bare kwana kwana, zallar gaskiya! Kuma tabbas ta yi mashi shaidar baya karya!. Akwai cakwakiya fa, kenan idan ba shi ya kasheta ba wanene?.

Ji ta yi jikinta ya mutu sosai, dama ga ciwonta yana yi mata zafi, kafafunta ne suka kasa ɗaukarta, nan take ta ji wani jiri ya ɗebeta, kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ji ta yi ta tafi zata kifa kasa. Cikin zafa ya tarota ta faɗa jikinsa, wani irin kuka mai tsuma zuciya ta sanya.

Da gudu Pretty ta taho ta zube gwiwowinta a ƙasa kusa da su, ta kai hannu tana taɓa Autar tana ambatar sunanta.

Shi ma cikin girmamawa yake kiran sunanta yana faɗin. "Ranki ya daɗe dan Allah ki yarda dani, wlh bani bane, bata yadda za'ayi in cutar take! Hakan ba zai yiwu ba! Na tabbata da kin san matsayinki a raina da kwata kwata ba zaki taɓa yarda da cewa zan iya cutar dake ko da da cizon cinnaka ba ne, dan Allah ki fahimceni".

Allah sarki, bai taɓa shiga ruɗani irin na yau ba, bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba, ya shiga damuwa mara misiltuwa, sambatu kawai yake yi ba tare da yasan abin da bakinsa ke fitarwa ba.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E..............16

Tari sosai Auta ta fara yi, kuka ya ci karfinta, ta rasa me zata yi, idan ta ce ta yarda da shi ba shi ya kasheta ba, to kenan wanene? Akwai mai kama da shi ne a kingdom ɗin? Kai ina hakan ma ba zata taɓa yiwu ba, dole shi ne dan kamanninsa ba zai taɓa ɓace mata ba.

Idan kuma taki yarda da maganarsa wani ɓangare na zuciyar tata yana faɗa mata zata cutar da zuciyar bawan Allah, zata cuceshi ta sanya shi a damuwa bayan ita kanta tasan baya karya, iya gaskiya yake faɗe, to ita yanzu ya zata yi da ranta?.
Chapter 62 · 0% Book details