← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 242

Sashe 144

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya kasa yin magana har sai da sake cewa. "Baby baka jina ne?"....... Sarkafewa voice É—insa ya yi, da kyar ya É—an yi gyaran murya kafin ya amsa da. "Ina jinki". Kamar zata yi kuka ta ce. "Kana jina amma shi ne ka yi shiru?".
A wannan karan jinjina mata kai ya yi tamkar yana a gabanta, sannan ya amsa da. "Sorry yanzu ina jinki yi magana".... Fuskarta cike da ƙayatattcen murmushi ta cigaba da cewa. "To yanzu baby na samu wanda nike so kuma yake sona, yanzu haka ya zo nan gida kawo mun ziyara kazo ku gaisa..........".

Katseta ya yi cikin tsawa yana huci. "Waye ya bashi izinin ya zo gidan?". Yadda ya futar da words ɗin sai ya baka dariya, dan a harxuƙe ya yi maganar.......
"Baby ai kai kace idan na samu mai sona na kawo shi zaka aura mun, to naga ina son shi shiyasa nace ya zo ku gaisa da kai and kuma wlh yana......." Tsawan da ya daka mata cikin kakkausar murya ne yasa ta haÉ—iye sauran maganganunta, bata yi zatan zai É—auki zafi har haka ba.

Cike da ɓacin rai da fusata a fili ya ce. "Ya jirani gani nan zuwa, sai na ji uban waye ya bashi izinin yin magana dake, kema wait for me tukun nan, bari na zo". Yana kai karshen maganar ya katse kiran ba tare da ya jira reply ɗinta ba....... Cikin zafa ya wuce ta ɗauki key ɗin motarsa, kamar ba shi ne ya gama cewa ba zai samu damar zuwa gidan yana aiki ba, tuni ya mance da aiki ya figi mota sai gidan Ammo.

Ita kuwa, yana katse kiran ta miƙe a zabure, lokaci guda ta ji tsoro ya kamata, yanzu ya zata yi idan ya zo? Ta jefawa kanta tambayar. Da gudu ta diro kasan bed ɗin ta nufi waje. Bata zame ko'ina ba sai wajen Ammo, a lokacin ta koma cikin bedroom ɗinta.

Tana zuwa ta sanar da Ammo wautar da ta tabba kuma ga baby nan zuwa. Siririn murmushi irin nasu na manya Ammo ta yi, cikin natsuwa ta fara faÉ—a mata yadda zata yi idan ya zo ta kwantar mashi da hankali har ya fahimci wasa take yi mashi, daga karshe ta gargaÉ—eta da kada ta sake yi mashi irin wannan wasa, domin zata iya sanyawa ya shiga wani hali, yanzu in da ya É—auko mota a fusace ya biyo daren nan idan wani abin ya faru fa? Irin wannan wasa yana da kyau ta san lokacin yinsa. Sosai ta ji shawarin Ammo tare da yi mata godiya.

Suna tsaka da hakan suka ji wani irin horn da aka rinƙa bugawa a gate ɗin a haukace, da gudu baby ta diro ƙasa ta nufi waje, da kallo Ammo ta bita tana tausayawa rayuwarta, saboda already baby ya faɗawa Ammo ɗin dalilin da yasa baya san kowa yasan matarsa ce, saboda familynsa, shi ɗan babban ahali ne masu ji da karfi da izza, so yasan abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa su yi accepting baby a matsayin daughter in low ɗinsu ba, wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ya ɓoyeta, shi kansa ba shi da kwarin gwiwar iya tinkarar familynsa da ita a matsayin mata, tsawon shekaru ya rasa yadda zai yi, ga shi yana santa kamar ya mutu, ba zai iya rabuwa da ita ba, musamman mahaifiyarsa da yasan ko zai mutu ba zata aminta da marasa asali ba, ya auri baby tun bata wuci 10 years ba a duniya, amma har yanzu ya gaza samun kalaman da zai iya tinkarar familynsa da shi wajen sanyasu su aminta da ita. Uhm babbar magana!!.

Bedroom ɗinta ta nufa da gudu, tana zuwa ta haye saman bed tare da shigewa cikin bargo tana sauke numfashi da sauri sauri kirjinta na ɗan bubbuga mata da ɗan karfi karfi. Da karfi ya banko kofar bedroom ɗin nata ya shigo, har sai da yasa gabanta ya faɗi sosai, da ta yi niyar yin pretending kamar tana barci, amma turo kofar da karfi yasa ta zabura ta miƙe zaune tana zazzara idanu. Fuskarsa babu annuri ko ɗigo a kanta ya afko cikin ɗakin, ransa a matuƙar ɓace sosai, numfashinsa ma kama yake yi da mai huci. Cikin kakkausar murya ya ce. "Waye ya baki izinin yin magana da wani har ki kawo shi cikin gidan nan?".

Sosai ta tsorata da ganin yanayinsa, jikinta na rawa ta diro kasan bed É—in, dik sai ta ji ta kasa yin magana. Cikin kakkausar murya ya sake cewa. "Ina mutumin yake and ina Ammo da ta barki kika kawo wani cikin gidan nan"......... Cike da tsoron abin da zai iya aikata mata ta amsa mashi da. "Baby to ba kai kace dama in kawo dik wanda nike so zaka aura mun ba?".

Hmmm a lokacin da ya yi mata wannan magana fa bata wuci 9 years ba a duniya, amma tsabar iyashege wai bata manta da zancen ba. Kuma shi cikin wasa ta yi maganar fa.
"Ina mutumin yake na ce?!!". Cikin tsawa ya yi maganar. Satar kallan kofar fita ta yi, kafin ya ankara sai ganinta ya yi ta watso da gudu zata nufi waje. Ai cikin zafa a miliyan ya kai mata capka a ciki. Ihu ta so kurma mashi saboda tsorata sai kuma ta danne, shi kuwa tsabar yana cikin ɓacin sai sai ya yi wurgi da ita a saman bed tare da kara daka mata tsawar ta faɗa mashi ina mutumin da ta kawo ɗin yake?.

A hanzarce ta miƙe tsaye tare da dirowa kasan gadan, jikinta na kerma amma taki faɗa mashi gaskiyar cewa wasa take yi mashi, dan Ammo ta ce kada ta yi saurin faɗa mashi su bari kishin tasa ta ɗan zafafa. Kin yin magana ta yi tana kumbura kumatu. Kara hasala sosai ya yi, ya zo har wuya, gadan gadan ya nufota da nufin kai mata duka tun da taki faɗa mashi ina mutumin, ɓacin rai yasa bai tsaya tambayar mai gadi akwai wanda ya zo gidan ne ko babu ba? Hankalinsa dik a kanta shiyasa ita ya fara tinkarowa kai tsaye.

"Where's ur phone?". Ya faÉ—a cikin tsawa, ya yi maganar kuma yana kara tinkarota gadan gadan tana ja da baya har suka kurewa jikin bango. Rumfa ya yi mata da kirjinsa, yana huci ya sake tambayarta ina wayarta? Dan a tinaninsa yanzu kenan tana hira da maza ta wayar, dan haka a yanzu zai yi rugu rugu da wayar ba kuma zai sake saya mata wani ba, sai yanzu ya gane ashe kuskure babba ya tapka da bai sanar da ita cewa ita matar aure ce dan haka ta nisanci mazan waje ba, yazama dole yau ta san matsayinta.

Shiru ta ki yi mashi magana, hakan ya kara zafafa kunan da ransa yake yi, cikin fushi ya cire hannu zai ɗauketa da gigitaccen mari. A hanzarce tasa hannu ta kare fuskarta haɗe da fashe mashi da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Dakatawa da yunkurinsa ya yi yana huci sosai, ya ɗauki zafin da har zata kaisa ga aikata aikin danasani, shi da bai taɓa dukan mace ba yau ya kwantanta, kuma a kan wadda yake kauna fiye da komai, sai ya ji rashin daɗin hakan a ransa.

Cikin zafa ya juya zai je wajen Ammo ya ji dalilinta na barin baby ta kula wani namijin bayan ita tasan komai. Yana juyawa baby ta yi saurin riƙo hannunsa tana kuka. Ƙasa ta zube gwiwowinta a gabansa ba tare da ta saki hannun nasa ba, cikin kuka ta ce. "Tin da nike da kai ban taɓa ɓata maka rai ba a rayuwata sai yau, tabbas ba zan manta da wannan rana ba a rayuwata, ka yi hakuri baby ba zan kara ba, na tuba ka ji? Bana fatan wara rana ta zo wadda zan ɓata ran wanda na fi so sama da komai a duniya, wanda ya so ni ya kuma sanyani da farincikin da ban taɓa zata zan shiga ba a rayuwata, tabbas na yi kuskure".

So mugun abu ne wani lokaci, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta sanyaya, jin kukanta yasa ya ji zuciyarsa ta karaya, yana santa baya san kukanta. Dan haka a hankali ya juyo gareta yana sauke ajiyar zuciya. Ɗan duƙawa ya yi yasa hannunsa ya ɗagota, sai hawaye take ta shararawa. Rungumeta a jikinsa ya yi yana jin zuciyarsa ta sanyaya. Sai shessheka take yi, kukan gaske ta yi, dan bata taɓa tinanin ransa zai ɓaci har haka ba, sai dik ta yi nadamar abin da ta aikata.

"Baby ka yi hakuri ka yafe mun ka ji?". Ta faɗa tana kara shigewa jikinsa. Kasa ƙasa da kyar ya iya cewa. "Babu komai bab ɗin babynta, komai ya wuce, yanzu ki faɗa mun ina mutumin yake sannan meyasa zaki fara soyayya da wani ba tare da kin sanar da ni ba?". Wato dai har yanzu bai huce ba, buƙatarsa a faɗa mashi ina mutum yake kawai.
"Am so sorry my baby, wasa nike yi maka, ni babu wani da nike so a duniya sai kai". Wani irin ajiyar zuciya mai sanyin gaske ya sauke, cikin sauri ya ce. "Are u sure?". Kai ta gyaÉ—a mashi alamar yeah.

Ai bai san lokacin da ya rungumeta kam a jikinsa ba, bai ma san time da ya hau zuba mata ruwan albarka ba, cikin sambatun nasa ne yake haÉ—awa da. "Kada ki yarda ki kula kowa, ke É—in mallakina ni kaÉ—ai". ....... "Baby mallakinka kuma?". Ta faÉ—a irin like bata san komai ba.
Kai ya jinjina mata tare da amsa mata da e. "Baby to kenan ba zan yi aure ba tun da ni mallakin ka ce". Cikin shagwaɓa ta yi maganar dan ma ya ɗauka har yanzu yarinta na damunta bata san komai ba........ Wato ita ma baby yar duniya ce fa, tasan kan tsiya kala kala, wai ya ɗauka har yanzu yarinta na ɗawainiya da ita bata san komai ba.

"Babu wanda zaki aura sai babynki, ke É—in matata ce ni kaÉ—ai, dan haka kada ki kula kowa kin ji?". Da alama yana out of control yake wannan sambatu, dik dan murnar bata kula kowa bane fa, kamar ba yanzu ya gama bambami kamar zai tashi gidan ba.
Chapter 144 · 0% Book details