← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 242

Sashe 97

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akka kuwa hankalinta gabaɗaya ta mayar a kan Mahnoor, like wow, she was so surprised seen her beautiful face, abin ta bata yi expecting ba, ita kanta ta shaida Mahnoor kyakkyawa ce, ga gyaran da ta sha, skin ɗinta har wani yellow yellow ya yi yana wani glowing, wlh komai sanin da ka yi wa Mahnoor ba zaka taɓa ganeta a yanzu ba, dan ta haɗu iya haɗuwa, ko makiyi sai ya jinjinawa haɗuwar da ta yi sai dai idan ba zai faɗi gaskiya ba saboda kiyayya.

Gabaɗaya su King zuba mata idanu suka yi suna kallanta, a cikin zuciyarsa King ya ce. Dama shi yasan dik abin da Rahilarh zata zaɓa ba abin yasarwa bane, lallai ba shakka wannan yarinya ta dace da jaish.

Cike da matsuwa da san jin amsarsu momma ta ce. "Gwaggo (Akka) ya kuka ganta? Ta yi?".

Shiru Akka ta yi tana cigaba da karewa Mahnoor kallo, baiwar Allah mai innocent face. Kun san Akka fa babu ɓoye ɓoye, dan haka sai ta ce. "Wannan yarinya anya ba zata iya zama green snake under green grass ba kuwa?".

ÆŠan zaro idanu suka yi gabaÉ—ayansu, sai dai babu wanda ya iya tambayar Akka dalilinta.

Cigaba ta yi da cewa. "Yanayin fuskarta ya nuna shiru shiru sosai ce ita, kun san masu irin wannan fuskar munafikai sun fi yawa a cikinsu".......... Akka tamu ta amana.

Shiru parlourn suka yi, dan idan Queen mother tana magana ba'a katseta sai ta gama.

Hannu ta kai ta ɗan ɗago haɓar Mahnoor, abinku da kaka, ko kunya bata ji ta fara yi wa Mahnoor leke leke har da gane mata girman tula tulanta, tana yi tana magana kamar haka. "Ni jikokina dik lafiyayyu ne, dan haka suna da buƙatar cikakkun mata, sannan suna san komai ya ciko sosai, saboda gujewa zinace zinace dole mu bincika da kyau mu samo wadda zata iya ɗaukarsu, dole na bincika masu komai".

(Nace yanzu kun gane qualities ɗin da King ya zage yake ta cewa sai mace tana da su sannan zai aurawa ƴaƴansa ita? Kun gane irin qualities ɗin ko sai an maku karin bayani? Su kansu sun san abin nasu na gado ne, to dai ga Akka ta buɗe komai mun ji irin qualities da ake nema😅🥱)

Tana magana tana sassaukewa Mahnoor alkyabbarta izuwa saman shoulder É—inta.

(Kam bala'i, jama'a Akka duniya ce, a lallai gara ta duba masu, kai aima dole ta duba dan tasan sun yi gadon abin,🤭 tasan wanenen King Abdul Malik kakansu kenan, e dole ta duba aga Mahnoor zata iya ɗaukan Jaish ne ko yaya? Kai wlh wannan tsohuwa duniya ce.)

"Shekarunki nawa?". Ta jefawa Mahnoor tambaya. Momma ce ta yunkura zata yi magana, hannu ta É—aga mata alamar ta yi mata shiru.

"Kada na ji bakin kowa a nan, bincike nike yi tukun nan"........ Tsit suka yi suna sauraronta.

Baiwar Allah kanta a ƙasa cikin sanyin murya ta ce. "Ban san takamaiman shekaruna ba, amma dai tsakanin 15 da 16 ne". Larabcin Mahnoor yana gargada,.bata kware sosai ba.

Jinjina kai Akka ta yi, sannan ta sake cewa. "Mahaifiyarki ta sanar dake abin da ake nufi da aure ko kuma ta barki a sake tana jiran ni in sanar dake? Kin san menene aure? Kin san yadda ake kula da miji? Kin san kalan mijinki kuwa? Kin shirya iya É—aukarsa?". ........ Yau ga ikon god wajen Akka, tsohuwa zata buÉ—e komai fa.

"A'a bani da mama, babu kuma wanda ya taɓa faɗa mun menene aure". Tamkar zata yi kuka ta bada wannan amsa.

Cak Akka ta dakata da ƙoƙari cire mata alkyabba da take yi, da sauri ta dawo da kallonta a kan face ɗinta. "Ke marainiyace?". Murya cike da tausayawa ta jefa mata tambayar.

Da e ta amsa mata idanunta suna cikowa da kwallah, nan take Akka ta ji jikinta ya yi sanyi, Allah sarki suna da jin tausayin marayu sosai, haka zuciyarsu take, janyota jikinta Akka ta yi, sannan ta ce. "Ya sunanki?".

Mahnoor ta bata amsa. Kwnatar mata da kanta a saman gwiwowinta Akka ta yi tana É—an shafa bayanta, da É—an É—aga murya ta ce. "Princess Mahnoor mata ga Prince Jaish barkanki da shigowa familyn King Abdul Malik".

Haba wani irin ajiyar zuciya su King suka sauke, barema momma da ta fi kowa matsuwa da san jin amsar Akka, tun da ta kira Mahnoor da princess shikenan ta yi na'am da ita kenan.

Mummyn Chuchu ce ta rangaÉ—a masu guÉ—a, nan take suka hau farinciki mara misiltuwa. Sarina and Mammie bakinciki kamar zai kashesu, barema da suka ga fuskar Mahnoor, babu abin kushewa a tattare da ita, ga kyau kamar ita ta yi kanta, uwa uba ta fi Fanan kyau da komai nesa ba kusa ba, kai in short basu da wani abin da zasu nuna mata da shi, ta fi su komai, kamar Sarina zata haÉ—iyi zuciya saboda taya Fanan kishi.

Wato akwai cakwakiya wlh sosai.

Kallan su King Akka ta yi, cike da bada umarni ta sanar da su ta aminta da Mahnoor, suma tana basu umarni da su karɓeta a matsayin sirika. Cike da gimamawa suka amsa mata da sun karɓeta hannu bibbiyu ma kuwa.

Akka ce ta buƙaci jin yadda aka yi Jaish ya haɗu da marainiyar Allah da kuma me ya kaisa Nigeria?. Babu ɓoye ɓoye momma ta zayyana masu dik yadda aka yi. Sosai suka kara jin tausayin Mahnoor yakamasu, nan take ran Akka ya ɓaci ta ce wlh ita ba zata yafewa Nenne ba, dole su hukuntata azabar da ta ganawa Mahnoor, kun san basa yafe zalinci su ato.

A fili Sarina ta yi suɓul da baka wajen cewa. "Ashe ƴan gidan matsiyata ƴan kauye mara galihu ne ma". Bata san ta yi maganar ba har sai da taga kowa yana kallanta, sannan ne ta farga, da sauri ta miƙe ta nufi waje tana ɓata ran wai ta ɓata lokacinta a kallan ƴar gidan matsiyata.

Da kallo suka bita har ta fita, a nan ne King ya fahimci lallai akwai matsala idan har basu yi da gaske ba, dole ya zauna shi da momma su tsara yadda zasu kula da Mahnoor ba tare da wani abin ya sameta ba, idan ba haka ba zata fiskanci barazanar kanne miji.

In short a nan aka yi komai aka gama, momma ta buƙaci iznin zuwa Jimeta a kai kayan aure da komai da ake yi wa mace kafin a aureta. Akka da kanta ta bata izini. Suka gama tsara komai, sannan mummyn Chuchu da momma suka miƙe suka kama Mahnoor suka fita da ita, mama ma miƙewa ta yi ta basu waje. Mammie ce ta yi fitar karshe.

Parlourn ya rage daga King, uncle Abbas, uncle Jahiz sai Akka, tattauna suka fara yi a kan batun, dan su san ta yadda zasu tsara komai.

Mahnoor kuwa part ɗin momma suka wuce da ita dan su kara shiryata yau za'a kaita ɓangaren Jaish. Mahreen dai an barota a ɗakin gyara.

🔥🔥🔥BABY AND AMMO🔥🔥🔥

Zaune take a saman sofa tana fuskantar Ammo dake zaune a saman nata sofar, Ammo na kallan Tv ita kuma tana rike da cup mai É—auke da cappuccino tana sha, center table dake gabanta wani É—an madaidaicin laptop É—inta mai shegen kyau da tsada ne a kai, daga gefensa wasu takardunta ne tana karatun exams, na faÉ—a maku tana bala'in san karatu, kuma Allah ya bata ilimin both side.

Sanye take da kayan barci masu kyau, rigace mai laushi sosai mai karamar hannu, sai wani É—an madaidaicin wando da bai wuce singalalin kafafunta ba, bai kai har kasa ba. Wandan dai'dai da jikinta yake, shi kuma rigan yana da É—an faÉ—i kaÉ—an, tana da dirarren jiki sosai kamar dai su Pretty tamu, sai dai bata da wani tsawo sosai, tsayinta dai'dai da shekarunta.

Tana sipping cappuccino a hankali hankali tana duba takardunta, kanta na sanye da hular kayan barcin jikinta.

"Baby ni zan shiga in kwanta, karfe 9 ta yi, yakamata kema ki kammala karatun nan da wuri ki je ki kwanta tun da gobe exam kuke da shi kuma da wuri zaku rubuta ko?". Cewar Ammo.

"E exam muke da, yanzu zan kammala, saura kaɗan ne". Ta kai karshen maganar tana ɗaura cup ɗin cappuccinonta a saman table ɗin kusa da laptop ɗinta, sannan ta ɗauki takardanta ɗaya da take dubawa ɗin, ƙwaƙwalwarta ya ɗan ɗauki zafi, ta ƙasa gane wannan karatu, tinani take yi ko dai ta kira babynta a waya ta ce ya koyar da ita ne, in ya so su yi karatun ta Whatsapp kamar yadda suke yi a dik sanda wani karatu ya gagara mata.

Ita kuwa Ammo miƙewa ta yi ta nufi dakinta tana yi mata sai da safe, da yake ɗakinsu daban daban, sai idan baby ta yi ra'ayi ne ta je ɗakin Ammo su kwana.

Wayarta baby ta É—auko da nufin ta kira numbersa ta sanar da shi ya hau Whatsapp su yi karatu, sai dai bata kai ga kiranba kofofin hancinta suka jiyo mata kamshin perfume É—insa, hakan yasa ta yi saurin kai kallanta a bakin kofar shigowa.

Yana tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, kallanta kawai yake yi, sanye yake da wando three quter jeans white color, sai round neck polo shirts sky blue mai shegen kyau, ya yi kyau matuƙa, da alama fitan ba shiri ya yi, duba da yanayin dressing ɗinsa.

Zaro idanu ta yi, cike da mamaki mai ɗauke da farinciki ta miƙe tsaye, wani ƙayataccen murmushi ne ya kubce mata kafin ta ambaci baby.
Shiru bai amsa mata ba, ya dai kafeta da idanu, idan ka gansa zaka yi zaton gabaɗayanta yake kallah, amma bahaka bane, hankalinsa yana a kan kirjinta, da yake bata sa bra ba, and gasu masha Allah suna tsole idanun mai kallo.......... Anya baby ba barci ya ƙasa yi ba da ya biyo dare kuwa? To mutum dai shi ba karfe ba, kuma shi lafiyayyen namiji, ya kai 30 years, ya zayyi ba zai ƙasa barci ba ɗazun yaga kaya iya kaya? Kada ku ce na ce, tom gaskiya dai na faɗa.

"Baby daman zaka zo ne baka faɗa mun ba?". Cikin wannan shagwaɓa tata kamar ta Prettynmu dai ta yi maganar.
Chapter 97 · 0% Book details