Sashe 128
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana rufe maki Smart ya dubi King ido cikin ido, talk without respect ya ce. "Me Zunaira ta yi maka ka daketa?".............. Subhanallah, idanun da jama'ar cikin parlourn nan suka zaro sai ya bawa mutum tsoro, hankalinsu ne ya kara tashi, ba'a taɓa yi wa King magana yadda Smart ya yi a yanzu ba, King fa, tab lallai akwai matsala.
Momma ne ta katse shi cikin É—an É—aga murya.
"Omerish daddynku ne fa! Meyasa zaka yi magana haka without respect?"........ ÆŠan waro idanunsa a kan King ya yi kafin ya ce. "Ko baki faÉ—a mun ba i already knew that she's my dad, bcoz of his face, yana kama da su Ramish, so ai already knew that, kawai ya faÉ—a mun dalilin da yasa ya daki Zunaira?".
Tashin hankali, King kuma daddyn Smart? To fa!! Ya aka yi hakan ta kasance? Daddynsa na Paris fa? Waye shi da har suke kama sosai?...... Tsit suka yi, gabaÉ—aya Mammie ta ji cikinta sai murÉ—awa yake yi, mama hankalinta ya kara tashi sosai, a tinaninta Ramish shi ne magajin mahaifinsa, tana jin daÉ—i itace mai power, har tana hasashen gaba kaÉ—an ita ce zata zama mai murza kambun power crown da ya fi kowani crown karfin iko, ta yi mulki san ranta, ta gama tsara plan É—inta rana tsaka kawai a wargaza mata komai a wani ce Smart É—an King ne? Tab aikuwa ba zai yiwu ba.
Auta dai ta kwanta shiru a jikinsa tana shessheƙar kuka, Omaid and Obaid da yake sun san ko waye Smart sai suka kara natsuwa suna kallan wannan tashin hankali da aka shiga. Ita kuwa Mammie burinta kawai a warware masu wannan cakwakiya dan tasan wani mataki yakamata ta ɗauka.
"Tambayarki fa nike yi Rahilarh, wanenen wannan?". Cewar King, dan hakurinsa ta fara kurewa, saboda ya zo har wuya yanzu, abin ku da jinin sarauta, basa É—aukar raini, maganar da Smart ya yi mashi without respect shi ne ya bakanta ransa yake san hukunta Smart, amma sai yasan wanene shi tukun nan, dan tin da ya É—aura idanunsa a kan Smart É—in ya ji wani irin kaunarsa ya ratsa mashi zuciya........ Babbar magana!!.
"Ɗan kane". Tashin hankali, momma ta bawa King amsa tana kallan cikin idanunsa. Zaro idanu King ya yi tare da sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, ɗana kuma?. Ya maimaita kalmar a cikin ransa. Lokacin guda ya ji wani irin sanyi ta ratsa zuciyarsa, dik da bai san ta ya aka yi Smart ya zama ɗansa ba, ba shakka ya ji sanyi a ransa, sai dai kuma ta wani ɓangare ya ji ransa ya sosu matuƙa, dan dik cikin ƴaƴansa babu wanda ya taɓa yin gigin yi mashi magana yadda Smart ya yi mashi, kowa respecting ɗinsa yake yi sosai.
Uncle Jahiz da ya ji zancen kamar a mafarki ne ya yi saurin cewa. "Momma how comes hakan zai kasance bamu sani na?". A ruÉ—e ya yi maganar.
Wani irin tsawa mama ta daka wajen cewa. "Ina hakan ba zai yiwu ba! Ta ya akayi ya zama É—ansa? Hauka ne abin?!!".
Kowa ya ji maganganun mama yasan meyasa take faÉ—in hakan. Ita dai mummyn Chuchu shiru abinta, amma dai ita ma ta ji babu daÉ—i a ranta dik da tasan cewa dama ba ita bace da mulki tin da Ramish ya girmewa Bilal, amma dai ranta ya É—an sosu kaÉ—an bayyanar Smart.
Mammie kuwa mutuwar tsaye ta yi, tabbas tasan momma ta ɓoye Smart a rikicin da aka yi a baya, amma bata taɓa zatan irin wannan bayyana Smart zai yi ba, yaro ya fi ubansa zafa, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, ya dame King a zafin zuciya da jiji da kai, ga shi da magana kai tsaye babu wata ɗar ɗar, kuma magana a kaifafe, ga uban kwargini. Sosai hankalin Mammie ya kara yashi over, tinaninta ɗaya ya za'ayi su ga bayan King ga wani zakin ɗan nasa ya kara bayyana, idan ma ta ce zata auri King ɗin wlh waɗan nan zakunan ƴaƴan nasa zasu iya cinyeta da ranta, kai ta ko'ina abin babu sauki a gareta.
"Ki yi mana bayani ta ya aka yi wannan ya zama É—ana?". Cewar King kenan. Jinjina kai momma ta yi kafin ta ce. "Kowa ya samu waje ya zauna".
Babu musu suka koma saman sofas da suka tattashi suka zauna suna jiran momma ta kora masu bayani.
"Omerish ka samu waje ka zauna bari mu yi magana ko?". Cewar Momma. Bai musa ba ya wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna tare da zaunar da Auta a saman laps É—insa, sannan ya ce Guyson ya taso ya zo ya zauna a kusa da shi.
Da sauri guyson ya taso, dama tin É—azun yake san yin magana amma ya kasa, dan shi ya fi kowa sabo da Smart, dik in aka yi karamar hutu a school sai ya je France, Auta kuma sai ta je Dubai Smart yake tura jirgi ya É—aukota karkashin kulawar Jaish ba tare da sanin kowa ba, wani lokaci kuma Jaish É—in ne yake É—aukarta daga kingdom of power ya ce sun tafi yawo sai su wuce wajen yayan nasu a Faransa É—in, in short dai guyson ya fisu sabo da shi sosai.
Shi kuma Smart ya fi shakuwa da Auta, dan kamar yadda take kama da shi a fuska haka jininsu ya yi matuƙar haɗuwa, tamkar ransa yake santa, yanzu haka dalilinta ya zo kingdom of power, dan tin kafin ya tafi duniyar wata yake san momma ta haɗa shi da ita, amma momma tana yi mashi kona kona, ba komai yasa ba kuma face Auta ɗin ta ɓata a lokacin, momma tana gudun faɗa mashi ta ɓata dan kada ya ce zai zo ko ya ɗauki wani mummunar mataki, shiyasa taki faɗa mashi, idan ya kira guyson ma ya haɗa shi da Auta shi ma ya yi ta yi mashi kwana kwana dan momma ta hanasa faɗa, haka Jaish ma, daga karshe da ya gaji ne yana dirowa daga tafiyar da ya yi ya ɗaga jirgi sai kingdom of power, kun ji dalilin zuwansa.
GabaÉ—aya parlourn tsit suka yi bisa umarnin King, sun zuba idanu suna jiran su ji me momma zata ce, kowa idanunsa a kanta. Akka ta lura Smart ya fita zafa sai ta natsu, dan ta lura shi ya gado ainahin zuciyar king Abdul Malik, su King Zuhair dik basu gada yadda yakamata ba, ga wanda ya fisu zafa, tsit kuke jinta a parlour kamar babu ita!!.
Gyara murya momma ta yi kafin ta fara jawabi dallah dallah kamar haka.
"Kamar yadda na faÉ—a Omerish É—anka ne to hakan ne babu shakka a wannan al'amari".
Kirjin mama and Mammie ne suka bada dum dum da karfi!!. Hankalinsu ne ya kara tashi, lokaci guda suka fara haɗa gumi, momma ta jiƙa masu aiki, mama kam kasa hakura ta yi har sai da ta ce. "Ta ya aka yi ya zama ɗansa shi ne zaki yi mana bayani!".
Momma bata bi ta kanta ba ta cigaba da cewa. "Dama ba mutuwa ya yi ba, a lokacin da ka kafe lallai sai na dawo maka da shi, na yi magiya kaki saurarona, dik kunki fahimtata, kun ki fahimtar abin da nike faÉ—e, har daddy a wannan karan bai fahimceni ba, su Yah Rahab kowa yaki fahimtata, Yah Muhammad ne kawai ya iya fahimtata, a wannan lokacin ne dan Omerish ya tsira da ransa ya kuma rayu sai muka haÉ—a baki da Yah Muhammad a kan mu shirya maka ya mutu sai ya tafi da shi kasar France in da babu wanda zai sake ganinsa domin ya rayu............"
Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon wani tsawa da Akka ta daka mata. "Rahilarh dama ba gaskiya bane mutuwarsa? Amma kika jefamu cikin tashin hankali? Kina ji kina ganin mahaifinsa ya rinƙa ciwo kaman zai mutu dalilin mutuwarsa, amma kika share kamar babu zuciyar tausayi a kirjinki, e lallai".
Kasa da kai momma ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Goggo ki yi hakuri, wlh a kullum ina kukan ciwon da Yah Zuhair yake yi a kan mutuwar Omerish, na shiga damuwar da ban taɓa shiga ba, har na karaya na yanke shawarar zan dawo da Omerish in yaso a kashesa da gaske kowa ya wuta, amma Yah Muhammad ya ce a'a in daure komai zai wuce, wlh goggo ina tsananin san Omerish shiyasa na yi hakan, amma dan Allah ki yafe mun, kai ma Yah Zuhair ka yafe mun, nasan na yi kuskure............"
Wai me ya faru a baya ne da yasa har aka so kashe Omerish É—in?. To mu je dai zuwa, wanda zata bada labarin abin ya faru a baya bata bayyana ba tukun nan, idan ta bayyana zaku ji komai.
Katse mata magana King ya yi da cewa. "Kin cuceni Rahilarh, kin cuceni wlh". Yana kai karshen maganar ya miƙe da sauri saboda wani irin zafi da zuciyarsa take yi mashi, yasan zai iya faɗuwa a wajen idan ya cigaba da tsayawa saboda zafin zuciya.
Bedroom ɗinsa ya shiga da sauri yana huci, da sauri momma ta miƙe ta bi bayansa, Aunty MieMie ce ta yi saurin sake miƙewa ta rufa mata baya. Nan fa parlon ya koma kallon kallo, su Mammie da suka san abubuwan da suka faru a baya sun gane kan maganar da momma take yi, su kuma su Sarina da basu san tarihin baya ba sai basu gane kan maganar momma ba bayan cewa Smart ɗan King ne.