← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 242

Sashe 92

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata san sake jefa mashi wata tambayar, dan tasan halinsa sam bai cika san tambaya ba, tana kaucewa abin da baya so, sai kawai ta amsa da okey tare da komawa ta zauna suka fara ciye ciyensu ita da Pretty.

After some minutes. Hannunsa É—auke da wasu itatuwa ya dawo wajen, wuta ya zo ya kunna masu sannan ya matsa gaba ya É—auro alwalarsa a wajen ruwan gudun dake kusa da su. Sallar mangariba da isha'i ya haÉ—a dikka ya yi, saboda matafiyi ne shi wanda babu abin ganin lokacin a tattare da shi, hasalima bai iya gane gabas ba sai dai ya kintata ya yi sallar kawai.

Bayan ya idar ya yi addu'a sosai, dik Zunaira tana ta aikin kallan motsinsa, a yanzu basa iya ganin face É—in juna saboda duhu, sai sun matsa kusa da wutar da ya kunna suke iya ganin juna.

Bayan ya kammala ya matsa kusa da wutar ya zauna tare da lankwashe kafafunsa yana kara wasu itatuwa a ciki dan wutar ta cigaba da ci har wayewan gari kada ta mutu. Auta and pretty kuma suka tashi suka gabatar da sallar isha'i bayan sun gama cin abin da suka ga zasu iya ci.

Shiru ya zauna yana tinanin irin kalubalen da zai fuskanta a kan soyayyarta, sai dai ya kudurta a ransa ko mutuwa zai yi ba zai janye ba tin da ya rigada ya sanar da ita cewa yana santa, sun kuma yi wa juna alkawarin ba gudu ba ja da baya.

Ya zurfafa cikin tinanin da yake yi, kamar daga sama ya ji saukar hannayenta a saman shoulders ɗinsa, ta zarosu ta gabansa ita kuma tana ta bayansa, tana durkushen a saman gwiwowinta, ta ɗan manna kirjinta da bayansa kaɗan, hannunta na rike da fresh apple jajir mai kyau da zaƙi.

Saitin ɗan bakinsa ta kawo mashi apple ɗin, a daidai saitin kunnensa ta tsayar da laɓɓanta, silent talk ta yi wajen furta mashi............ "My Hero kai fa baka ci komai ba, ni kwata kwata ban ga kaci wani abin na fa, ka karɓi wannan ka ci". Ta kai karshen maganar tare da kara matsar mashi da apple ɗin a dab bakinsa.

Rasa me zai yi ya yi, ya rasa a wace duniya yake, ya rasa a wani matsayi zai ajiye kansa, yau shi ne tare da abar da ya fi kauna sama da komai nasa, kuma ga su a ƙeɓaɓɓen waje, har da kulawa na musamman take bashi, bayan Abbonsa babu wanda ya taɓa damuwa da ya ci abinci ko bai ci ba sai ita, kai ba zai taɓa manta wannan rana ba a rayuwarsa.

Alhamdulillah ya rinƙa nanatawa a cikin zuciyarsa, ya ƙasa iya buɗe bakinsa ya karɓi kyautarta a garesa. Ƙasa sosai ta yi da murya, kamar mai raɗa ta sake cewa. "My Hero ba zaka ci kyautar da ya fito daga hannu na bane? Ko kuma sai na yi maka kuka ne? Da kaina fa zan baka".

Oh my god, wani irin nisawa ya yi, ajiyar zuciya mai daɗin gaske da bai taɓa sauke irinta ba ya sauke, a hankali ya buɗe ɗan bakinsa ta sanya mashi apple ɗin, kaɗan ya gutsira yana jin tamkar babu abin da ya kai wannan apple ɗin daɗi a duniya....... Oh soyayya ruwan zuma.

Sosai ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta na ganin ya gutsira, har ajiyar zuciya ta sauke, wannan ajiyar zuciya da ta sauke ji ya yi tamkar ta kara lulluɓe zuciyarsa da bargon farinciki ne. Ita dai Pretty sai sanya kananan itatuwa take ta yi a cikin wuta, sam hankalinta baya ma kansu baiwar Allah.

Sake matsar mashi da apple ɗin kusa da bakinsa ta yi, dan farinciki haka ya rinƙa gutsira yana ci har ya cinye ba tare da ya sani ba, cike da zumuɗi ta zame hannayenta daga shoulders ɗinsa, tana ƙoƙarin barin wajen tana faɗin. "Bari in karo maka wani my Hero".

A hanzarce ya ɗan juyo ya rike hannunta a cikin nasa. "Please ba sai kin karo mun ba, wanda kika bani ya wadatar, na ƙoshi sosai saboda albarkan dake tattare da hannunki".

Ƙayatattcen murmushi ta sakar mashi, wutar tana haskasu gwanin ban sha'awa, bata yi musu da shi ba ta yi na'am da zancensa, sannan ya saketa. A hankali ta dawo gefen damansa ta zauna suna fuskantar wutar, kanta ta kwanto da shi a saman damatsan hannunsa tare da kamo hannunsa guda ɗaya.

Sillent talk ya yi wajen ce mata. "Baki jin tsoron dajin nan?"........ Ƙara yin lamo a jikin hannun nasa ta yi. "Ni da nike tare da kai kuma my Hero tsoron me zan ji?". Ɗayan hannunsa ya kai saman hannunta da ta riƙo nasa.
"Kina ƙara mun kwarin gwiwa sosai my Hoonaira".
A ɗan shagwaɓe ta yi magana ƙasa kasa ta yadda ita kanta tasan ba zai ji me ta faɗa ba. "Ban ji me kika ce ba". Ya tambaya yana ɗan juyo da face ɗinsa saitin tata, irin mutum ya juyo ya kalli gefen shoulder ɗinsa haka.

Sake yin maganar ƙasa ƙasa sosai ta yi, still dai bai ji me ta ce ba, hakan yasa ya ɗan kwanto da kansa kusa da nata kaɗan ya kara tambayar me ta ce.

"Barci nike ji kuma san yi nike ji". Shi ne abin da ta faÉ—a. Tabbas akwai sanyi sosai a wajen, shiyasa ma ya kunna masu wannan wutar dan wajen ya É—an É—umama.

"Tashi in É—auko maki rigan sanyina na É—azun ko?". ............ Make kafaÉ—a ta yi. "Ni dai a'a, ba zan iya tashi ba". Kallan Pretty dake ta doka hamma ya yi, da yake ita ta saba yin barci da wuri baiwar Allah, har idanunta sun yi ja alamar barci.

"Pretty ɗauko mun rigan sanyina a wajen kayanmu, daga nan sai ki je ki kwanta dan naga kamar barci kike ji"............ Da okey ta amsa mashi tare da miƙewa ta isa ga kayansu.

"ko kema zaki je wajen da na tanada maku ki kwanta ne?". Ya jefa mata tambaya yana zame hannunsa daga kan nata....... "A'a ni dai zan kwanta kusa da wutar nan dan in rage jin sanyi". .......... Jinjina kansa ya yi alamar to. Kawo mashi rigan sanyin Pretty ta yi, karɓa ya yi ta wuce ya je ya kwanta a wajen nasu tana yi masu good night.

Cikin sanyin murya haɗe da tausasawa da lallaɓawa ya ce. "Ɗaga in saka maki rigan kin ji?".
Jiki dik kasalar barci ta ɗan ɗaga shi tana turo baki. Sorry ya ce mata kafin ya ware rigar ya sanya mata, sannan ta sanya shi dole ya miƙe mata kafafunsa ta tada kai da laps ɗinsa tana daka hamma, lamo ta kwanta a laps ɗin nasa, wutan yana ɗan ratsata kafin wani ɗan lokaci barci mai daɗin gaske ya yi awon gaba da ita.

Shiru ya zuba mata idanu yana ta kallan face ɗinta, ya ƙasa zare kallonsa daga kanta, kamar yadda yaga rana haka ya ga dare. Tana kwance a kafarsa yana ta kallan face ɗinta har dare ya tsala, Pretty ta jima da yin barci abinta.

Asuban fari Auta ta farka, ta sha madarar mamakin yadda ta kwnata daren jiya ta barshi haka ta wayi gari ta same shi, cike da mamaki da tausayawa ta tambaye shi bai yi barci bane?. Kai ya gyaÉ—a mata almar e bai yi ba.

"Meyasa to?". Ta jefa mashi tambayar tana kallansa. "Tashi mu je mu yi sallah mu cigaba da tafiya, dan mu isa gida da wuri rana na ganin ido". Shi ne abin da ya faÉ—a a maimakon ya bata amsar tambayarta a garesa. "Ni sai ka bani amsata zan tashi". Kamar zata yi kuka ta faÉ—a.

"Kin manta jiya na faÉ—a maki cewa bana barcin dare? Kin kanta na faÉ—a maki gadin gimbiyata kawai nike yi ne?"............... Tina maganganunsu na jiya ta yi, abin ya kara bata mamaki, a tinaninta ya faÉ—a mata hakanne kawai saboda soyayya, bata san dik kalamansa hakikanin gaskiya ce wanda babu mix ba, baya faÉ—ar kalamai dan jin daÉ—in soyayya ko kuma daÉ—in bakinsa, dikkan abubuwan da yake faÉ—a gaskiya ne kuma yana iya aikata fiye da hakan a kanta.

Sai yanzu ta kara tabbatarwa da kanta lallai ta yi babban sa'ar da samun irinsa abu ne wanda zai bada wahala, lallai Hoorain one in million ne. "Tashi to tin da na baki amsa".

Ajiyar zuciya ta sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana". Da alama zuciyarta ta yi sanyi dayawa, dan ta fara yarda son da take yi mashi wasa ne a kan wanda yake yi mata. "Sai da aka gama jera mun tambayiyin ne za'a ce mun ina kwana?". Cikin zolaya ya yi maganar.
Siririn murmushi ta saki tana sanya tafukan hannayenta ta rufe face É—inta. Wani irin daÉ—i ya ji na ganin murmushinta, lallai wannan safiya tasa ta fara da kyawawan abubuwa.

Ta tafi da tinaninsa har ya sanya hannunsa ya kamo hannayenta da ta rufe, ya buɗe dan ya ji daɗin ganin kyakkyawan murmushinta, yarinya mai kyan gani, dik wanda ya ganta sai ya ji daɗi a ransa. Yunkurawa ta yi da sauri ta miƙe tana cigaba da murmushi. Zama ta yi kusa da shi suna fuskantar juna, har lokacin wutar bai mutu ba, a hankali ya saki hannayenta da ya rike yana kallan gefe.

"My Hero". Ta ambaci sunansa kallanta a kansa. Kin É—agowa su haÉ—a ido ya yi, amma ya amsa kiran. "Idan har da gaske kana sona, abu É—aya zaka mun in tabbatar da hakan".

Jinjina mata kai ya yi alamar to ba tare da ya yi magana ko ya yi wani motsi ba. "Kalli cikin idona sai mu yi magana"......... Kamar ba zai yi hakan ba, sai kuma ya daure ya É—ago da kallansa a kanta. Ya subhanallah, sarkafe juna da kallon kauna mai tafiya da imani suka yi, gabaÉ—ayansu sun lula wata duniya, dik sun kasa yin magana. Sun macewa juna a kallo, ita kanta ganin cikin kwanciyar idanunsa yasa ta rasa nitsuwarta bare kuma shi.

Sai da suka ɗauki good 5 mins a haka, sannan ya yi ta mazan lumshe idanunsa yana jin wani abu na mashi yawo daga tsakiyar kansa izuwa tafin ƙafarsa. Cool voice ɗinta ya ji a kunnuwansa tana faɗin. "Na yi fatan mu kasance ma'aurata da wuri".
Chapter 92 · 0% Book details