← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 242

Sashe 108

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

X-ray Machine ya ɗauko, komai da zafa yake yi duba da halin da take ciki na zuban jini sosai, wannan machine yasa ya fara bincikar dik wasu jijiyoyi da gaɓaɓɓan dake kusa da in da aka harbeta ɗin, dan ya tabbatar da in da bullet ɗin yake ya kuma tabbatar da cewa bai taɓa wata jijiya ko wani joint or kashin jikinta ba.

Da sauri Dr Raj ya nufosa domin ya taimaka mashi, hannu ya ɗagawa Dr Raj alamar baya buƙata, shi ma zai rama cetan ransa da ta yi ne da kansa, zai yi iyaka ƙoƙarinsa dan yaga ya ceceta. Sharifat sai shessheƙar kuka take yi tana rungume da Abbie, Ummie dai taki biyosu nan, ta wuce part ɗinta. Abu Abdussalam yana cikin tashin hankali, da kaga face ɗinsa zaka san yana cikin tashin hankali bawan Allah.

A hankali Ramish ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya kalli tabbas bullet ɗin bai taɓa koɗaya daga cikin abin da yake gudun ya taɓa ba, bullet ɗin yana tsakiyar namar kirjinta, sai dai saura kaɗan ya huda ƙashinta.

Cikin zafa ya ajiye X-ray machine É—in. Sannan ya É—auko Antiseptic Solution, a hanzarce ya fara tsabtace wajen da bullet É—in ya fasa namar ya shiga ciki. Yadda kuka san computer haka yake yin aiki.
Tsab ya tsabtace wajen, sannan ya É—auko Local Anesthesia don rage mata zafi.

Dik da idanunta a datse sai da ta ɗan ciza laɓɓanta a lokacin da yake gudanar da aikinsa, alamar tana jin azaba, the way take jin azaba the way take kara datse idanu.

Lokacin guda tausayin Leesharh ya ratsa zuciyarsa, dan yasan azabar bullet, su da suke matsayin jami'ai, zaratan jaruman maza ma bata sauki suke iya jure azabar bullet ba bare ita da take mace kuma yarinya, ai dole dik wani mai zuciya a kirjinsa ya tausaya mata.

Scalpel ya É—auko. Shi kansa sai da ya É—an datse idanunsa a lokacin da yake buÉ—a namar kirjin leesharh da wannan Scalpel É—in dan ya samu damar iya zare bullet É—in. Yana aiki cikin zafa, amma kuma dik wata karfe da zai É—aura a jikin Leesharh a hankali yake yi mata cikin tausayawa.
Yana buÉ—e namar wajen jini ne ya kara bulbula da karfi tamkar ruwa ya fasowa kansa hanya.
Da sauri ya É—auko Irrigation Syringe da É—ayan hannunsa ya fara tsabtace jinin yana sharesa. Sannan ya É—auko Suction Machine ya yi amfani da shi wajen toshe jinin dan ya samu saukin yin aikinsa. Abin ku da jami'i, ya kware a wannan fanni na cire bullet.

Retractors ya É—auko, cike da kwarewa ya fara amfani da shi wajen rage tsokar dake ta cikin fatar in da bullet É—in yake. Bayan ya rage sai ya É—auko, Chlorhexidine, ya yi mata amfani da shi dan ya kara tsabtace wajen harbi saboda da ya yanke namar wajen an samu zubar jini.

Ajiyar zuciya ya sauke ganin cewa komai ya daidaitan mashi yadda yakamata. Forceps. Wannan kayan aiki ne mai kama da almakashi, ana amfani da shi don kama bullet ɗin cikin sauƙi, cikin nutsuwa da tausayawa ya sanya forceps ɗin, a hankali ta kama bullet ɗin. A hankali hankali ya fara jan bullet ɗin yana zaro shi waje.

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ciro bullet ɗin, cikin wani kwano mai ɗauke da ruwa mai sanyi da Dr Raj ya kawo mashi ya jefa bullet ɗin, sannan ya yi hanzarin ɗauko sutures ya fara ƙoƙarin haɗe wajen ya ɗinke mata.

Dik cikin ɗakin sai da suka tausayawa Leesharh, harbi a kirji namiji ma yaya aka cika bare kuma a kirjin mace, ai abin da ciwo matuƙa wlh.

Ramish bai fita daga ɗakin na sai da ya tabbatar da ya kammala komai, sannan ya nufi waje da sauri. Cikin zafa Bilal ya rufa mashi baya, kai tsaye h-q suka nufa a tare. Shi kuma Dr Raj ya matsa kusa da Leesharh dan ya ƙara dubata, lallai ba shakka shi ma ya ji yana kaunarta yadda ta bada ranta ta cetan mashi ɗan uwansa, a yadda Ramish yasa harbi ba sau ɗaya ba sau biyu ba da ace wannan harbin ta samu zuciyarsa ai shikenan sun rasa shi, amma ta tare mashi, a gaskiya yazama nauyi a wuyansu da su tsaya tsayin daka wajen ganin sun ceci rayuwarta ita ma.

Matsawa kusa da bed ɗin Abbie da Sharifat suka yi domin su dubata, baiwar Allah ta ji wahala har face ɗinta ta kumbura sosai lokaci guda, ta zama kamar ba ita ba. Shi dai Yah Rizwan baya nan, ya ɗan yi tafiya zuwa ƙasar China dan bunƙasa kamfanoninsa.

To Leesharh sai dai mu ce Allah ya tashi kafaÉ—unki kawai, Allah yasa kina da rabon shan ruwa a gaba, Ramish kai kuma Allah yasa ka kama masu nikaf mu ji dalilinsu na bibiyar rayuwarka da suke yi mu kuma ji maciya amanar da suke cin amanarka.

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Sweetie ta samu lafiya cikin yardan Allah, sai kuma sabon walaƙanci da ta karo yarinyar nan, sam bata da tsoro, ya battaba dai jikin sarauta ne da gaske yake gudu a jikinta, akwai ta da karfin hali da jajircewa.

Zaune suke a saman bed ɗin Black Tiger a bedroom ɗinsa ita da Ronnie tana yi mashi bayanin kan yadda ake gudanar da sallah dallah dallah, Black Tiger ya tafi fada, kun san dama sun ce idan za su yi karatun addini a part ɗinsa zasu rinƙa yi dan a nan ne ba zai iya ganin abin da suke aikatawa ba ko?

To hakan kuwa aka yi, tana ta yi wa Ronnie bayani yadda zai yi sallah, tana sanye da doguwar riga irin shigar mutanen birnin Black world, ta yi balai'n kyau, ta saki wannan kyakkyawan golden white hair nata sai sheki yake yi, ya sha gyara, Ronnie ya ce kayan basu taɓa yi wa wata mace kyau irin yadda suka yi mata ba, ta ji daɗin yaba kyanta da yake yawan yi, ranta na sanyaya sosai.

Dik abin da take koya mashi yana rikewa sosai a cikin kwakwalwarsa, saboda akwai brain shi ma, ga shegen san karatu kamar me.

Suna zaune suna fuskantar juna, kamar wasu yaya da kanwa, gwanin birgewa, yana sanye da hoodies milk color a jikinsa. Sai wani binta da Koreans eyes É—insa yake yi.

"Sweetie ina san ki faɗa mun a in da zan samu ainahin Ingila in karanta, dan ina san sanin ainahin saƙon da yesu ya zo da shi". Cewar Ronnie kenan, yana magana yana ɗan murza mata ƴan yatsun hannunta dake rike cikin nasa. Sun bajewa Black Tiger a saman bed ɗinsa kamar nasu ne. Floris dai tana can wajen Angela, yanzu Floris ta fara yarda da zugin da master Devil yake yi mata, shiyasa ta ja baya da su sosai, amfani yake san yi da yarintarta ya kama Ronnie, ce mata ya yi idan ta taimaka mashi zata mallaki Ronnie, ita kuma sai ta yarda.

ÆŠago kai ta yi suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ta ce. "No need ka karanta ingil a yanzu Ronnie".......... "But why?". Ya jefa mata tambayar da alamar damuwa a face É—insa, da alama da gaske yake yi yana san sanin ainahin abin da annabi Isa ya zo da shi.

"Saboda ingila ba zata dawo duniya ba, Annabi Isa zai dawo duniya, sai dai idan ya dawo shi ma ba zai yi amfani da ingila ba, zai dawone yana mai bin bayan Annabi Muhammad (S.A.W) so dik hukuncin da zai yanke a yayin dawowarsa zai yanke ne bisa amfani da kalamul lah, wato Alqur'ani mai girma".

ÆŠan zaro idanunsa ya yi, cike da mamaki ya ce. "Kenan dama yesu zai dawo duniya?".......... Jinjina mashi kai ta yi alamar e, sannan ta É—aura da cewa.

"Tabbas zai dawo duniya, wannan magana tana da asali daga hadisan Annabi Muhammad (SAW), wanda ya tabbatar da dawowar Annabi Isa (AS) a ƙarshen zamani. Daga cikin hadisan da suka zo kan hakan akwai. Hadisin Abu Huraira (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) ya ce. Ina rantsuwa da wanda raina ke hannunsa, haƙiƙa zai sauko maku da ɗan Maryam a cikinku a matsayin mai hukunci na adalci, zai kashe batun cin alade, zai hana haraji, kuma kuɗi za su yawaita har ba wanda zai karɓa, hadisin yana nan a cikin Sahih al-Bukhari hadisi mai lamba 2222, sai Sahih Muslim hadisi mai lamba 155".

"Sannan Abu Huraira (RA) ya sake ruwaitowa. Annabi (SAW) ya ce. Ba wani annabi da zai kasance a tsakanina da Isa, wato bayan manzan Allah babu wani annabi da za'a sake yi sai Annabi Isa da zai dawo. Lallai Isa zai sauko duniya, kuma zai yi hukunci da shari'ar Musulunci. A cikin Sahih Muslim hadisi mai lamba 2365. Ma'anar Wadannan Hadisan shi ne, Annabi Isa (AS) zai dawo a ƙarshen zamani, amma ba a matsayin sabon annabi ba, sai dai a matsayin mai bi ga shari'ar Annabi Muhammad (SAW) Zai yi hukunci da shari'ar Alqur'ani da Musulunci, ba da Injila ba. Zai tabbatar da adalci, ya kawar da shirka, ya karya gicciye, ya hana cin naman alade, kuma ya hukunta duniya bisa dokokin Musulunci. Wadannan dalilai sun nuna cewa Annabi Isa (AS) ba zai zo da sabuwar shari'a ba, ko ya yi amfani da littafin da ya zo da ita a baya wato ingil, sai dai zai zama mai bin shari'ar Annabi Muhammad (SAW). Wannan yana daga cikin alamomin ƙarshen duniya da kuma tabbacin cewa Musulunci shi ne cikakken addini har zuwa ƙarshen zamani, dan haka ba sai ka wahala wajen neman karanta Ingila ba, ka karanta Alqur'ani mai girma dan ma ka kara sanin girman Allah ka ji ko?".

Shiru ya yi yana tinanin lallai ba shakka Annbi Muhammad fiyayyen halitta É—in ne da gaske kamar yadda Sweetie ta faÉ—a mashi, lallai zai yi biyayya ga Annabi Muhammad iyaka iyawarsa, tabbas zai karanta Alqur'ani mai girma zai kuma yi haddarta.

Ganin ya yi shiru yasa ta ce. "Baka gamsu bane in kawo maka wasu hujojin masu karfin da dole ka gamsu Ronnie?".

Da sauri ya girgiza mata mai alamar a'a ya gamsu, sannan ya ce. "Dan Allah ki bani tarihin Imam Mahadi ko kaÉ—an ne yau kam, kullum sai na tambayeki amma baki faÉ—a mun".
Chapter 108 · 0% Book details