← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 242

Sashe 135

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Obaid sarkin zafa ne ya daka mata tsawa cikin harshen larabci. "Zaki faÉ—a mana wacecce ke da abin da ya kawoki part É—inmu ne ko sai na tashi na kakkaryaki?". Yana magana yana kara É—aure fuska.

Sarai ta ji wannan magana da ya faÉ—a, kun san bata barin ko ta kwana, jin zai daketa da ya faÉ—a yasa ta sanya hannu ta rike waist É—inta da kyau, kallan up and down ta bisu da shi kafin cikin tsiwa ta ce.

"Tun da kai ka halicceni ba sai ka dakeni in gani ba! Kana tinanin ma barinka zan yi ka taɓa ni ne? Wlh baka isa ba, ramawa zan yi". Tana jajjagen masifar tata kuma tana kallon kofar fita, ta gama yin ready kis take jira ta yanka waje a miliyan.

Kun san Obaid dama shi baya da hakuri ko kaɗan, aikuwa ransa ya gama ɓaci, a gabaɗaya kingdom of power babu wanda yake yi masu nasiha cikin ruwan sanyi ma ya zauna lafiya sai Jaish bayan Momma, amma saboda tsabar aljanun kanta na guguwar bishiyar kuka ce zata tsaya a tsakiyar parlournsu, su tambayi meya kawota har ta ce zata faɗa masu magana, wlh yau sai dai wata ba ita ba koma ƴar uban wanene ne.

Sai huci yake yi ya miƙe tsaye, Omaid ne ya yi saurin rike hannunsa yana faɗin. "Kai mezaka yi mata?". A fusace ya amsa da. "Mekake tinanin zan yi mata? Ni ka sakeni dan Allah hai".

"Obaid kana tinanin in ka taɓa wannan tsinken tsintsiyar zata rayu ne? Ka rabu da ita kada ka je ka yi kisan kai, ka ganta fa kamar sandar mopa...........".

Ana ƙoƙarin bashi hakuri a taushesa amma yarinyar nan tun Omaid bai gama rufa baki ba ta cafke zancen da cewa. "Tun da dik cikinku babu ɗan iskan da ya yi mun halitta sai ku rufe babin batun halittata, da kake ce mun sanda kai ya kake? Da shegen idanunka manya manya kamar na shaiɗan"......... Kai jama'a ko a ina Mahreen ta taɓa ganin shaiɗan har tasan idanunsa manya ne? Omaid kai ma ka shiga layin littafin Mahreen.

Ai sake Obaid Omaid ya yi, wato ya je ya lallasata kenan tin da ita bata san mutunci ba. Tana tsaye ya nufota cikin zafa, sai da ta bari ya kusanta sai ta yanka waje a miliyan. Ai da gudu ya rufa mata baya, shi kuma Omaid ya cigaba da yin wayarsa abinsa.

Kai tsaye part É—in momma ta nufa da gudun gaske. Tana sanyo kai suka ci karo da guyson da ya fito daga bedroom É—in momma zai koma nasa dare ta yi. Karo suna yi a in da ya É—an yi baya yana dafe goshinsa da ta bugesa.

Ita kuwa da yake tasan abin da ta tsokano sai bata tsaya ba, a guje ta raɓa gefensa zata wuce, da sauri ya riko hannunta, cikin natsuwa ya ce. "Lafiya kike gudu haka a cikin daren nan?".
Ƙoƙarin kwace hannunta ta yi dan ta ruga da gudun ta karisa ciki.

Shi kuma bai gama rufe baki ba sai ga Obaid ya iso wajen da gudu. Da karfi ya sanya hannu zai fisgota daga rikon da guyson ya yi mata yana wani huci. A hanzarce guyson ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Ku dakata mana, lafiya Obaid ka biyota? Me ta yi maka?".

Har lokacin ƙoƙarin kwace kanta take yi ta gudu. Ɗaure fuska sosai Obaid ya yi, cikin ɓacin rai ya zayyana mashi dik abin da ya faru, daga karshe ya ce wlh idan bai karyata pieces ba ba zai iya yin barci ba yau. Dik da guyson yana rike da ita yana ƙoƙarin kashe wutar da ta kunna bakinta bai rufu ba, dan kuwa tana jin Obaid ya ce sai ya karyata cikin tsiwa ta ce.

"Ka karyani tun da ni itace ce, da wani shegen ido kamar na shaiÉ—an na faÉ—a na kara faÉ—a".
Me guyson zai yi idan ba murmushi ba, shi ya rasa wace iriyar yarinyace, ji fa, ana ƙoƙarin kashe wuta tana kara kunna wani.

A fusace Obaid ya matsota yana faÉ—in. "Yah Omar dan Allah ka kyaleni in karya yarinyar nan".
"Dakata dakata Obaid, wai baka ga mace bace? Me zaka daka a wajen? Su mata ai babu gurbin duka a jikinsu ko?...........".

Guyson bai gama rufe baki ba ta capki zancen da cewa. "Kai kana tinanin kana da karfin dukana ne da kake wani tadada jijiyoyin wuya? Wlh ni na ci dubu sai ceto, kuma kai ma ka sakeni tun da baka da wani karfi mai kukan ciwo kawai". A karshen maganar tata da guyson take yi, wai bashi da karfin tare mata faÉ—a tin da yana kukan ciwo, larabcin nata ne a karkace.

Sarai Guyson ya fahimci kalamanta, ya fahimci zaginsa ta yi, amma da yake shi É—in damone sarkin hakuri, sai ya yi kamar bai ji ba, yasan idan ya barta da Obaid wlh ko momma ba iya kashe wannan wuta zata yi ba, dan ko an bashi hakuri ya tafi sai ya sakar mata kunama ko kwari, basa yafiya ai, dan haka solution kawai ya kashe wutar a nan mai gabaÉ—aya.

Capka Obaid ya kai mata da karfi zai shaki wuyarta Guyson ya yi saurin janyeta da karfi sai ta tafi ta faÉ—a saman kirjinsa, a hanzarce ya ce. "Obaid ka kyaleta mu yi magana mana".

"Ni Yah Omar ka barni in take bakin yarinyar nan sai hakwaranta sun cire gabaÉ—aya". "Aa Obaid, ba za'ayi haka ba, ka bari za ta baka hakuri..........". Bai kamala kai karshen maganar ba ya dakata sakamakon turesa da karfi da ta yi har ya yi baya kamar zai faÉ—i. Cikin tsiwa ta ce. "Kai É—an iska ne ashe? Allah ya isa da ka rungume ni". Tana magana tana galla mashi harara.

A zabure Obaid ya nufeta yana dunkule hannunsa É—aya zai kai mata duka a baki, damo sarkin hakuri bai gaji ba ya sake shiga tsakaninsu, bai damu da kalamanta ba, dan yasan yarinya ce, kuma girman kauye ce, fin haka ma zata aikata, kuma shi wlh burgesa take yi sosai, yana san mace mai confidence kamar Aunty MieMiensu, hakan yasa in dai ya shigo bai ganta a wajen momma ba sai ya tambayi ina take, tun da suka sha gyara suka fito a Æ´an gayu take burgesa take kuma yi mashi kyau, shiyasa ya zage ya tsaya rabata faÉ—a da Obaid.

Ran Obaid ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, dan haka sai ya sakar mata kunama guda biyu. Tana ganinsu ta zunduma ihu tare da daka sufa ta ƙanƙame guyson, kamar ba yanzu ta turesa tana kiransa da ɗan iska dan ya janyeta daga capkar Obaid ba, sai ga shi yanzu da kanta ta rungume shi tana ihu kamar zata tashi gidan da kuka, tana faɗin ya taimaka mata.

A lokacin momma ta tafi wajen King ta je ta rarrashesa ko zai sauko, so bata nan. Part na su Jaish kuma ba kusa da na momma yake ba shiyasa basu ji ihunta ba.

Da gudu Omaid ya iso wajen dan ya ji ihun, a tunaninsa lallasata Obaid yake yi yasa take kuka haka, so gudun kada ya kasheta yasa ya biyo bayansu da gudu.

Riketa sosai guyson ya yi yana ƙoƙarin kare mata kunamar. Obaid yana tsaye yana kallansu, a tinaninsa kunamar ba zata yi wa guyson komai ba tun da Mahreen ya sakarwa, sai dai bai ankara ba sai gani ya yi ɗaya ya sakewa guyson harbi a kafa, dai'dai lokacin kuma Omaid ya iso ɗin.

Azaban zafi yasa ya yi gaggawar saketa tare da tsugunnawa ƙasa yana ƙoƙarin riko kafar nasa. Ita kuwa yana saketa ta yanka a miliyan sai bedroom na momma.
Kusan a tare Omaid and Obaid ɗin suka zube gwiwowinsu a gaban guyson ɗin tare da kai hannunsu a kan kafar nasa, hankalinsu ne ya yi mummunar tashi, ga shi Jaish and Omerish suna gida, yau sun shiga uku, sun san idan brothers ɗin nasu suka samu labarin kunama suka saki ya cutar da guyson yau ba mai karɓarsu, dama Jaish ya jima da hanasu sake kunamar nan, amma basu dai'na ba.

Hankalinsu a tashe Obaid ya fara bawa guyson hakuri kamar zai yi kuka, Omaid kuma miƙewa ya yi tare da zura wayarsa a aljihun wandon sleeping dress ɗin jikinsa, sannan ya tattare karfinsa dikka ya ɗauki guyson cak, sai sorry suke ce mashi, kai tsaye cikin bedroom ɗin momma suka wuce da shi, tuni fuskarsa ta wanke da hawaye, rago a ciwo ba. Sosai yake kuka ga harbin kunama da balai'n zafi.

Abin mamaki, ko da suka shigo bedroom ɗin momma basu ga Mahreen ba, kuma tabbas nan ta shigo, sai dai ɓuya ta yi a wani wajen dan kada Obaid ya biyota ya kamata, ita bata wani damu da kunamar ya harbi guyson ba, ita dai ba ta samu ta tsira ba ai shikenan kuma.

Saman bed suka kwantar da guyson, a gaggauce Omaid ya fara ƙoƙarin cire mashi dafin kunamar, shi kuma Obaid ya ɗaura kan guyson ɗin a saman cinyarsa ya hau rarrashinsa yana goge mashi hawaye yana kara bashi hakuri da ya yafe mashi. Hankalinsu a tsananin tashe matuƙa.

Wlh Mahreen sai shirin Allah, haka kawai ta ja bawan Allah ya samu tsarabar harbin kunama, har wajen ya kumbura sosai, ita kuma ta gudu abinta, wlh idan aka bar Mahreen da su Obaid su kaÉ—ai sun isa su tada kingdom É—in nan, zasu tada zazzafar yaki wlh.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

SARINA.

Tana shiga parlon Jaish ta zare alkyabbar jikinta ta ajiye saman sofa, wai dan Smart ya kwaÉ—aitu da kyakkyawar surar jikinta...................... Yarinya, wai mu faÉ—a mata daga cikin masu jajayen kunnuwa masu yawo kusan tsirara ya fito ne ko dai mu yi shiru?.

Zuciyarta na shakkar tinkarar bedroom É—in, amma burin da take da shi a kansa ya fi wannan yawa, san nan Mammienta ta kara mata kwarin gwiwa tare da ce mata yana shakar wannan kamshin perfume É—in shikenan ba zai iya yi mata musu ba, dan haka sai ta ji ta kara samun kwarin gwiwar tinkarar bedroom É—in tun da babu abin da zai yi mata.
Chapter 135 · 0% Book details