← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 242

Sashe 173

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin motar ya shigo shi ma, a natse ya tada ita ya danna waje. Suna fita can ƙasa ƙasa cikin natsuwa ta ce. "Meyasa kake san fita kai kaɗai ba tare da tsaro ba bayan kasan aikin da ya kawoni gidanku a kanka? Kasan masu farautar rayuwar kusan sun fi masu kaunarka yawa". Tana damuwa sosai a dik lokacin da ya fita shi kaɗai, sai taga kamar ba zai dawo ba, kamar za'a kashe shi a hanya, dan tasan haɗarin masu nikaf. Yana driving a natse ya ce. "Kin damu da ni ne?"....... Shiru ta yi bata amsa mashi ba, bata ma da niyar amsa mashi ɗin.
"Aesh meyasa kike shiga damuwa a kan rayuwata?". Ya sake jefa mata tambaya. Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta amsa mashi da. "Babu komai, kawai dai dan nasan ana farautanka ne, and masu nemanka ɗin da alama sun fi yawa a kewaye da kai"......... "Ba gaskiya bane Aesh, dole kina da dalilin damuwa da rayuwata, meyasa zaki ɓoye mun?".......... Ya yi maganar dai'dai zai fita daga ainahin main gate na arear tsadaddiyar unguwar tasu ya sake ce mata. "Allah kuma yana kewaye da mu gabaɗaya daga ni har masu farautar rayuwar tawa".

Lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya, ai shikenan ya gama magana tin da ya ce Allah kuma babu wani sauran gyara ko ja in ja, dole a yi shiru. Securitys dake tsaran main gate É—in nasu ne suka dakatar da motarsa, saboda basu san motar ba, sabuwa ce ba normal motocinsu da ya saba shiga unguwar da su ba, sannan basu ga face É—insa ba, sai suka dakatar da shi dan bincikarsa, sai da ya saukar da glass É—in motar sannan suka gansa. Cikin girmamawa suka sara mashi haÉ—e da tambayar dama shi ne?. Kai ya jinjina masu tare da mayar da glass É—in ya rufe, dama tinted ce, ya ja motarsa kawai suka cigaba da tafiya yana dannawa securitys É—in horn alamar gaisuwa kenan.

Sai satar kallan juna ta kasan idanu suke yi dikkansu biyu, gabaɗayansu suna yunwar san kallan juna, saboda su kansu sun san sun yi kyau matuƙa, suna san bawa idanunsu abinci amma kamar suna tsoron haɗa idanu da juna.

"Aesh yaushe zaki bani haÉ—in kai wajen bincikena? Ki bani cikakken bayani dan kama mutanen can". Ya jefa mata tambayar tare da dawo da kallansa a kanta........ "Anytime". Ta faÉ—a tana sauke ajiyar zuciya. "Are you sure and are you serious?"........ Kai ta jinjina mashi alamar e ta tabbatar. Sosai ya ji daÉ—in amsarta, dan yana san cigaba da abin da yake yi, yana burin kama masu nikaf, and yana san tambayarta wasu tambayoyi a kan abin da ya faru a tsakaninsu a wancan ranar, amma yana shakkar tambayarta saboda har yanzu bata yarda ba da gangan ya yi mata ba, da ta aminta da shi ne he has a lot of question for her, amma babu dama, dan haka sai ya shanye wannan tambayoyi a ransa zuwa time da zai samu dama.

Shiru motar ta kasance na ɗan wani lokaci, yana tuki yana tunanin abin da yakamata ya fara yi. Da yake yana sharara gudu sai cikin ƙanƙani lokaci suka isa wani haɗaɗɗen wajen cin abinci na masoya mai bala'in tsari, tsada da kuma haɗuwa, gabaɗaya yankin wajen ice ne kewaye. Ya lura in dai a gida ne Leesharh ba zata taɓa cin abinci ba, amma in suka fito waje ko dan idanun jama'a ba zata kunyata shi ba, komai ya ce ta yi a waje yana da yakinin zata yi dan kada ta bashi kunya, shiyasa dik da baya cin abincin waje yau ya daure zai jarraba saboda ita ta ci ta ƙoshi. A katafaren parking space ɗinsu ya tsaida motar tasa, cike da kulawa ya ce. "Muje ko?".

Ai ta shagala da kallan kyau da tsaruwar wajen, kai Dubai ba dai kyau ba wlh, ga komai nasu cikin tsari, bata taɓa kallan irin wannan gidan cin abincin ba ko a mafarki, ba abin da ya fi ɗaukar hankali ma irin abubuwa sky blue da suka yi amfani da shi a wajen, ga golden da ya ji light mai haske, gaskiya ne wannan gidan cin abincin ya ci sunansa paradise ɗin kamar yadda yake a rubuce da manyan baki. Buɗe motar ya yi ya fito, ganin ya fita yasa ta yi gaggawar bin bayansa, dakatawa ya yi yana jiranta, tana ƙarisowa in da yake yasa hannu ya riƙo hannunta, ai a miliyan ta ɗago da kallanta a kansa, sai taga sam ba ita yake kallo ba, da gangan kuma yaki kallan nata, dan baya san ta hana shi yin abin da ya fito da shi, ya fito da ita ne domin ya samu ta rage damuwar da yake a ranta, yau dai ɗaya ta yi farinciki sosai.

Cikin natsuwa ya fara takawa ya nufi cikin wajen, ga mamakinta sai gani ta yi ƴan'mata da samari masu class da ji da kansu sun tsaya sai ɗaukarsa hoto a wayoyinsu suke yi, saboda kyan da Allah ya yi mashi, kun san su kyawawa dik in da suka shiga ko sun shirya ko basu shirya ba sai mutane sun yi ta ɗaukarsu hoto, wai a hakan ma ya sanya p-cap a kansa fa, basu wani ga face ɗinsa da kyau ba, amma haka suka rinƙa kashe mashi hotuna ta ko'ina babu kakkautawa. A nan ne wasu suka ɗauketa ita da shi a tare, and a media suka ɗaura hotunan, shi ko a jikinsa, in da yasa kai kawai yake tafiya cikin natsuwa, ita kuma ta damu sosai, dan tana tsoron abin da zai iya faruwa, tana tsoron masu nikaf su gani saboda suna bibiyarsa ta kowacce hanya.

My people's me kuke tinanin waÉ—an nan hotuna zasu haifar?.

Sosai ta waro idanu tana kallan yadda cikin wajen ya yi bala'in haɗuwa, sofas masu bala'in kyau, laushi da kuma tsada, waje ne na manyan kai. Zama suka yi saman sofar da ya zaɓa masu, sannan ya saka oder abin da yake ganin zasu iya ci, online oder ake yi, sannan sai ka biya ta online ɗin ka yi komai za'a kawo maka, sp kana ci zaka tashi ka tafi babu wani tsayawa yin payment, haka tsarinsu yake. Yana oder bai fi da mintuna uku ba sai ga shi an fara shirga masu abin da ya buƙata a gabansu saman table, dik a takure take saboda kallansu da jama'a suke yi, dik ta in da ta juya idanun jama'a a kansu, ga uban hotuna da ake kashe masu light ta ko'ina. Zuba mata idanu na ƴan sakanni ya yi kafin ya ce. "Ɗauki chopping stick or spoon mu ci abinci".

ÆŠago kai ta yi ta kallesa da nufin ta yi mashi gardama, amma sai ta gagara yin hakan saboda idanun jama'a dake a kansu, kuma ya yi mata wani irin kwarjini, yau idanunsa a kaifafe suke sosai, dan dole ta É—auki spoon dan da shi ta saba, shi kuwa sai ya ciro wayarsa ya fara latse latse dan baya jin kamar zai iya cin wannan abinci, bai saba da waje ba. Tana jin yunwa over to over, dan haka sai ta fara cin abincin a natse, sai dai kaÉ—an kaÉ—an take ci. Dik abin da take yi attention É—insa yana a kanta, bcoz ta ci ta koshi ya zo da ita tun da taki ci a gida.

Ya lura ɓata masu lokaci zata yi, dan sai su wuni a wannan waje bata gama cin wannan ɗan abinci ba, ɗan kaɗan kaɗan take ɗebowa kamar bakinta na ciwo, sai ya ajiye wayarsa a saman table ɗin ya kai hannu ya karɓi spoon ɗin nata, cikin natsuwa ya ɗebo abincin mai ɗan yawa ya kai mata saitin bakinta. Ɗago kai ta yi ta kallesa, while shi ma ita yake kallah ta cikin glass ɗin nasa, bata san disga shi a cikin mutane sai ta buɗe baki ya fara bata dai'dai san ransa, har lokacin hotuna ake ɗaukarsu.

Yana tsaka da bata abincin ne gabaɗaya yankin gidan cin abincin nan ya karaɗe da jiniya ta ko'ina, tamkar za'a tashi garin. Yana zaune bai motsa ba, ita kuwa hankalinta ya tashi sosai, dan idan ba a gidan Abu Abdussalam ba bata taɓa jin jiniya irin haka ba, a gidan Abbie kawai tasan idan za'a fita ko za'a shiga wannan jiniya yake tashi, to waye ne kuma ya zo a yanzu?. Bata kammala tambayar kanta ba sai ganin wasu jiga jigan jami'ai sun danno cikin restaurant ɗin a guje ta yi, ba dan tana tare da shi kuma taga bai motsa ba da ba abin da zai hanata tashi ta gudu. Gabaɗaya big girls and big boys dake wajen babu wanda hankalinsa bai tashi ba, babu wanda bai ji tamkar ya tashi ta gudu ba, bare ma yanda jami'an nan suke muzurai tamkar zasu ɗauki rayuka nan take.

Ko'ina tsit kake ji, jami'an gabaɗaya sun yi tsayuwa jarumta sun kewaye wajen gabaɗaya, shi dai Ramish tamkar bai san da zuwansu ba, yana cigaba da bata abinci a baki, ya lura ta tsorata sosai, dan haka sai ya yi ƙoƙarin ɗauke mata hankali daga kansu ta hanyar tambayarta a ina ta haɗu da masu nikaf har suka bata contacts na kashe shi?.

Tana ƙoƙarin bashi amsa wani very handsome jami'i ya danno kai ciki, he was so cute, handsome and gorgeous, sai dai shi chocolate color ne ba balarabe bane, and zubin Nigerians ke garesa, cikakken namiji ne mai rai da lafiya, kyakkyawa ajin farko, very hot guy, yana da tsawo dai'dai misali, Ramish ya fisa tsawo da kaɗan. Sanye yake cikin kakinsa, wasu zaratan jami'ai guda huɗu suna take mashi baya, kai tsaye in da su Ramish suke ya nufo. Yana isa wajen waɗan nan jami'an da suka rakosa suka yi gaggawar kewaye kowani angle na table ɗin da su Ramish ke kai, shi kuwa guy ɗin haɗe kafafunsa ya yi cike da jarumta ya ɗaga hannu ya sarawa Ramish. Ajiye spoon na hannunsa Ramish ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye, hannu ya bashi suka yi musaba cike da kulawa yana faɗin. "Saukar yaushe my guy?".
Chapter 173 · 0% Book details