← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 242

Sashe 72

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nitsuwa ya sake sanya Scalpel ya yanka namar ciki in da jinin ya taru. Nan take jini bakin kirin ya fara zuba, kurawa namar wajen ido ya yi, sai yaga wajen ya yi wani irin dark brown haka alamar kamar ya samu matsala, ya taketa sosai ne wlh.

Ajiyar zuciya ya É—an sauke, dan ya gano dole ya yanke namar dake wannan wajen, dan haka sai ya É—auko electrocautery bayan da wannan bakin jinin ya gama zuba. Amfani da shi ya yi ya yanke namar dake wajen haÉ—e da tsotse jinin tas.

Dik da tana sume sai da ta tsuke fuska alamar azaba. Tsab ya fitar da jinin kafin ya kara sa cotton fari tas mai tsabta ya kara tsabtace wajen. Sannan ya É—auko needle holder da zaren tiyata dan É—inka wurin.

Ko kaÉ—an babu tausayi a ransa, haka ya É—inke mata wajen tas ya kuma sanya plaster, daga nan ya tattare dik wasu abubuwan dake wajen ya mayar da su mazauninsu, ya É—auki s-z ya matsar da shi kusa da shi, sannan ya zare hands gloves dake hannunsa. Ya yi amfani da s-z a hannun nasa dan tsabtaceta. Cikin kwanciyar hankali ya É—auki remote ya kashe A.c dake É—akin mai gabaÉ—aya.

Sannan ya cire coat dake jikinsa. Yana cirewa wani Robbot ɗaya daga cikin masu yi mashi aiki ya matso ya karɓi coat ɗin, shi kuma ya nufi waje da sauri cikin zafa abinsa.

A ɓangaren Ronnie kuwa, tun da ya yi wannan barci na dare jiya sai da rana ta take sannan ya iya farkawa. Da sunanta a bakinsa ya farka, a razane kuma. Sai dai kuma da kyakkyawar fuskar yayansa ya fara yin tozali ba ita ba.

Hankali a tsananin tashe ya ce. "Yaya where's Sweetie?".
Black Tiger yana zaune a gefen bed É—in yana kallansa, yana sanye da kayan shan iska da suka kara bayyanar da kyakkyawar surar jikinsa, shi kuma ya kara haska kayan yadda yakamata.

Miƙewa tsaye ya yi ya bar wajen. Cikin Zafa Ronnie ya miƙe zaune a saman gadon, hankalinsa a tsananin yashe ya ce. "Please big bro where's Sweetie? Talk to me please and please". Hankalinsa a tashe ya yi maganar.

Black Tiger bai goge mashi tinanin kwakwalwarsa bane kawai saboda Sweetie tana raye, a tinaninsa ta mutu shiyasa ya yi niyar shafe mashi brain, ganin tana raye yasa bai yi hakan ba, ya É—aga masu kafa.

Ƙasa Ronnie ya diro, da sauri ya bi bayan yayan nasa yana cigaba da bashi hakuri da ya faɗa mashi ina Sweetie take, har kuka sai da ya yi, ya cigaba da magiya.

Dik kaunar da Black Tiger yake yi mashi yaki faɗa mashi in da take har tsawon sati biyu cir, har zazzaɓi Ronnie ya yi amma Black Tiger yaki kula shi ya faɗa mashi ina yake, shi da ya yi mata aiki dai yana zuwa ya dubata ya canza abin da yakamata a canza, amma yaki sanar da Ronnie har sai da ta farfaɗo cikin ƙoshin lafiyarta, sannan ne ya faɗa mashi tana cikin wannan ɗaki.

ÆŠakin ma a cikin bedroom É—insa take ta wata hanyar sirri da aka yi ta da da glass. Ni kam na ce ko ba komai Sweetie ta ciri tuta tun da ta shiga wannan É—aki da iya shi da Ronnie kawai suke jinya a ciki, É—aki na musamman, amma saboda Spender sai ga shi ita ma yau ya kasance a ciki, É—akin da da ace mutuwa tana da magani to da tabbas za'a iya samun maganinta a cikin wannan É—aki, saboda kwarewarsa a iya aiki.

Sai dai wani abin da baku sani ba, Black Tiger ya fahimci Sweetie ba zata bashi haÉ—in kai wajen mallakar Spender ba, dan haka ya fara tinanin zai yi mata aiki wajen zare tinanin kwakwalwarta ya sakawa wani daga cikin Robbot É—insa dan ya samu Spender.

Idan kuma ya yi mata wannan aiki to tabbas ba zata tashi ba, yanzu haka ya sanya a kowacce irin yanayi a shigo mashi da kayan aikin cikin kasarsa domin ya kaddamar da wannan aiki, saboda ya ga Sweetie fa ƴar a mutu ce, bata tsoron mutuwa bare ya yi mata barazana da shi ya ci galaba. Abu mai sauki kawai ya cire ƙwaƙwalwarta ya yi dashenta ga Robbot ɗinsa, sai dai kuma fa, in ya cire ƙwaƙwalwarta ya haura 30 mins bai yi saurin sanyawa robbot ɗin ba to zasu rasa tinaninta, dan kwakwalwar zata dai'na yin aiki kwata kwata......... Babbar magana. Akwai matsala fa.

Jin in da take yasa bai wani ɓata lokaci wajen kai kansa gareta ba, a lokacin ta kai sati da farfaɗowa, da yake ciwon ma ba wani babba sosai bane har ta samu sauki ba laifi, tana iya yin magana dik da ba wani sosai ba, kuma Allah ya taimaketa babu wani jijiya da ciwon ya taɓa.

Tana ganin Ronnie ta yi saurin miƙewa zaune, dama shi take dakon jira tsawon kwanaki, tun da ta farfaɗo bata ga kowa a ɗakin ba, dan Black Tiger ya daina zuwa tin da yaga ta farka.

Ta rasa ina zata sa ranta, ta kwana ta wuni tinanin ina Ronnie yake, bata tinanin a in da take kamar yadda take tinanin a ina Ronnie yake. Shi ne yasa tana ganinsa ta yi gaggawar miƙewa zaune, shi ma da sauri ya ƙarisa cikin ɗakin.

Yau satinsa biyu da musulta amma ko sallah bai taɓa yi ba, dan bai san yadda ake yi ba, ita da zata koya mashi gata a kwance bai ma san ina take ba sai yau. Dan haka yasa bai yi ba sam sam, kuma a ƙagare yake da ta koya mashi ya yi ɗin, dan addinin ta ratsa zuciyarsa sosai.

Tsabar farinciki yana zuwa saman bed É—in ya haye, cike da farinciki ya fara yi mata sannu yana kara bata hakuri, zuciya a karaye ya ce. "Sweetie yaya yafi karfinmu, ba zamu iya da shi ba, kawai ki barshi mu hakura". Ya yi maganar tare da riko hannunta yana murnar bata mutu ba.

Kai ta girgiza mashi, cike da kwarin gwiwa ta ce. "Bai fi karfinmu ba, kuma bai isa ya fi karfinmu ba, saboda mu Allah muka rike, da izinin Allah zamu canza yayanka, babu gudu ba ja da baya sai ya musulunta, dik azabtarwa da zai yi mana matuƙar ina numfashi ba zan janye kudurina ba".

Zaro idanun Ronnie ya yi sosai, cike da tsoro ay ce. "Sweetie kin ga abin da ya faru dake? Baki tsoron idan ya zo da ƙarar kwana ki rasa ranki?".

Ko a jikinta ta ce. "Tabbas idan na mutu a wannan hanya sai na fi kowa farinciki, a kan jahadi na mutu, a kan haryar isar da saƙon Allah da hidimtawa addini na mutu, dik wanda ya mutu a kan wannan hanyar ya yi shahada Ronnie, dik kuma wanda ya yi shahada makomarsa aljanna ce, dan haka babu gudu ba ja da baya, a da ina tsora ce da hakan, amma yanzun na kara samun kwarin gwiwar zan iya".

Sosai ya yi mamakin jin kalamanta, ya san da farko a tsorace take, to yanzu menene ya bata confidence har haka?.

"Kana mamakin menene ya kara mun kwarin gwiwa kenan ko?". Ta jefa mashi tambayar ne ganin cewa ya afka duniyar tinani.

Kai ya gyaÉ—a mata alamar e abin da yake tinani kenan. Nisawa ta É—an yi kafin ta ce. "Ba komai ne ya kara mun kwarin gwiwa ba face wasu abubuwa da na gano dangane da yayanka".

Like wow ya zaro idanu, a ƙagare ya ce. "Wani irin abubuwa kenan?". Ɗan girgiza kai kaɗan ta yi alamar ba zai gane ba kenan, sannan ta ce.
"Ba lallai ka fahimta ba, amma dai na gano cewa yayanka yana da bala'in saurin fusata, na biyu kuma baya saurin sauka idan ya yi fushi, na uku kuma tabbas bayan zuciyarsa fara ce, gaban ce aka dabaibayeta da bakar fenti, tabbas idan muka yi galaba a kansa mutane dayawa zasu ji daÉ—i su huta, ina da yakinin akwai abin da ya rikiÉ—ar da shi izuwa bakin mugu....."

Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Ai na faÉ—a maki tsananin kaunar mulki ya rikeÉ—ar da yaya izuwa mugu".

Kai ta girgiza mashi alamar a'a, sannan ta ɗaura da cewa. "Ba tsananin kaunar mulki bane ta rikiɗar da shi, akwai abin da ya saɓa, tabbas yana san mulki, amma bayanta akwai abu mai karfi da ya rikiɗar da shi, tabbas zan gano ko menene nan na da jimawa ba dan saukaka aikin mu". Babbar magana, amma me kuke ganin ya rikiɗar da Black Tiger izuwa azzalumi idan ba giyar kaunar mulki ba?.

"Sweetie zaki iya kuwa?". A tsorace ya jefa mata tambayar.

"In Sha Allah zan iya, samun kwarin haske da na yi a kansa ba ƙaramin taimaka mun zai yi ba, kaga yanzu zan san ta yadda zan gudanar da aikina a kusa da shi, zan san ta yadda zan guji ɓacin ransa da zai iya sakawa ya cutar da ni, sannan zan koyi yadda zan sarrafa ɓacin ransa a dik lokacin da Black heart ɗinsa zata motsa, yanzu ka koya mun yadda zan yi amfani da magic ɗina, dan shi ma zai taimaka mun wajen ganin na sarrafa Black heart na yayanka".

Shi kansa a yanzu ya samu kwarin gwiwa jin kalamanta, ya ji kuma kamar zasu yi nasara, dan haka sai ya ce. "Zan koya maki amfani da shi, amma yanzu dai ki bani wani amsa da tin last week nike ta san sanin shi, daga nan sai ki bani labari a kan bayyanar Imam Mahadi, sai ki koya mun yadda zan yi ibada".

"Yayanka baya kallanmu ko?". Ta jefa mashi tambayar cike da damuwa tare da addu'ar Allah yasa Black Tiger bai gansu ba, ta manta ne kwata kwata ta saki baki tana ta magana.

"Nan cikin É—akinsa ne, kuma na faÉ—a maki yana iya kallan ko'ina a cikin birnin nan amma ban da cikin É—akinsa, dan yana ganin wannan mallakinsa ne komai dake ciki sai da izininsa zai motsa".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙa godiya ga Allah da yasa a ɗakinsa suke, sannan ta ce. "Me kake san tambayata tin last week?".

MY BEST PART AGAIN💘🦋
Chapter 72 · 0% Book details