← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 242

Sashe 105

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu tsaya tambayarta me yake faruwa ba, dan tun dq suka ganta a nan da wannan lokaci sun san ba lafiya ba, dan haka suka yi zafin namar nufar part É—in Abbie. Already dama shi Ramish da bai tsaya kulata ba can ya nufa, saboda ya saba zuwa wajen Abbie da asuba su tafi masallaci a tare, so sai ya nufi can.

Wani irin daÉ—i ta ji ganin sun nufi part É—in Abbie, har da tsalle ta daka tana murmushi, sai kuma lokaci guda ta nitsu tare da wucewa da sauri ta rufa masu baya tana ayyana yadda zakunan samarin Abbie zasu yi kaca kaca da Leesharh, dan in dai suka sameta a haka kasancewarsu musulmai ne kawai zai hana ba zasu cinye namarta É—anya ba.

Suna shigowa suka tsaya cirko cirko kamar waÉ—an da aka dasa, kallan Abbie suka tsaya yi, Ramish yana rike da hannunsa yana tambayar meyasame shi jikinsa dik jini haka?. Abbie zai yi magana ganinsu Bilal da Ummie sun shigo yasa ya yi shiru, Ramish ya lura da Abbie baya san yin magana a gabansu dan haka sai ya ce masu su je masallaci zasu biyosu daga baya.

Ummie kuwa hankalinta a tashe t fara bin gadan Abbie da kallo tana zaro idanu, babu Leesharh babu alamarta a saman bed É—in, abin ya bata mamaki. Abin da bata sani ba shi kansa Abbie mamaki yake yi haÉ—e da tambayar kansa ina Leesharh ta shiga, domin kuwa lokacin da ya bi bayan Ummie domin ya bata hakuri kada ta kira su Ramish, kafin ya dawo ne Leesharh ta bar bedroom É—insa, da y dawo É—akin bai sameta ba.

Tambaya ɗaya yake yi shi ne ina take ya aka yi kuma ta bar bedroom ɗinsa? Yana shigowa da bai sameta a saman bed ba ya fara nemanta har cikin toilet, sai dai da gaske babu ita babu labarinta a cikin ɗakin, hankalinsa ne ya yi mummunar tashi, dan yana ganin kamar waɗan da suka yi ƙoƙarin cutar da ita a farko ne suka zo suka ɗauketa, abin da zai sanar da Ramish kenan, zai sanar mashi da ya biyan Leesharh bedroom ɗinta ya duba mashi menene ya sameta, bai kai ga yin hakan ba su Ummie suka shigo, shiyasa ya yi shiru?.

To ina Leesharh? Waye ya É—auketa?.

"Babu wata matsala?". Cewar Bilal. "Yeah babu zaku iy tafiya zamu biyoku daga baya". Ramish ya faÉ—a idanunsa a kan Abbie yana kallan tashin hankali a cikinsu.

Dr Raj ne ya ce. "Yah Ramish jini ne fa a jikin Abbie kuma ka ce mu tafi?". Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Juyawa suka yi suka nufi hanyar fita, É—akin ya rage daga Ummie da ta yi mutuwar tsaye, sai Abbie and Ramish.

Da wutsiyar ido ya wurgawa Ummie kallo, nan take ta sha jinin jikinta, tin bai yi magana ba ta yi saurin wucewa ta fita waje tana mamakin da al'ajabin ɓacewar Leesharh a ɗakin haɗe da bakincikin burinta bai cika ba, ta so su Bilal su yi kaca kaca da ita, amma Allah ya tsallakar da ita, ciza laɓɓanta ta yi tare da furta akwai gaba ai, wato bata janye kudurinta ba kenan.

Me Abbie zai sanar da Ramish? Me zai faru? Ina Leesharh? Waye ya É—auketa? Dik a gaba zaku ji.

Magana suka yi na tsawon 30 mins, sannan Ramish ya fita daga bedroom na Abbie ya nufi bedroom É—in Leesharh. Da shigarsa bai fi 10 mins ba ya fito ya koma part na Abbie. Jim kaÉ—an suka fito a tare da Abbie suka nufi masallaci.

Yau saɓanin kowacce rana da suke dawowa da wuri, yau sai karfe 9 na safe Abbie da Ramish suka dawo cikin gidan, koda suka dawo kuma part na Abbie suka wuce, nan suka zauna suka cigaba da tattaunawa, da alama wani bincike suke yi a sirrance, ko Ummie basu bari ta sani ba.

After some hours. Da misalin karfe 4 na yamma, katafaren hall ɗin da zasu yi taro ya cika makil da jama'a, taro ake gudanarwa bisa ƙaida, doka da girma, dik wasu manya masu ji da kansu a faɗin Dubai sun hallara a cikin wannan taron. Abbie yana zaune tare da Ummie a saman wani haɗaɗɗun kujeru da aka tanadawa familyn King Badeen, su Dr Raj dik suna gefensu except Ramish da yake saman stage yana speech cikin harshen larabci.

Sharifat tana zaune a tare da Leesharh waje guda, sun yi shiga iri É—aya, bakin Leesharh ya É—an kumbura haka zalika goshinta ma ya É—an kumbura, tana sanye da face mask a face É—inta, sannan yi rolling veil É—inga har ya rufe mata ciwon nata da aka sanya mata white bandeji a wajen.

Waye ya yi wa Leesharh dressing na ciwukanta? Ya aka yi hakan ta faru? Me Abbie da Yah Ramish suke shiryawa? Dik kada ku damu zan warware maku komai, ku dai mu je zuwa.

Miƙewa Leesharh ta yi, cikin sanyin murya ta ce da Sharifat zata je toilet tana zuwa. Da okey Sharifat ta amsa mata, sannan ta ɗaura mata da cewa ta kula. Jinjina kai kawai ta yi.

Hall É—in cike yake da manya manyan jami'an tsaron, securitys ta ko'ina, tsaro ya yawaita sosai a wajen ne saboda Abbie da yake matsayin ministan tsaron sannan ga manyan jami'ai irinsu Ramish a wajen.

Wani keɓaɓɓen waje Leesharh ta je ta samu domin amsa call ɗin masu nikaf da suke ta kiranta tun ɗazun, dama ba wani toilet da zata je, call take san ɗagawa. Filin da ta je a cikin wajen taron ne, amma ta baya wajen wasu ɗakuna da babu kafar mutane a wajen.

Ciro wayarta ta yi daga cikin hand back dake hannunta kalar abayar jikinta wato maroon color, ta yi kyau sosai. Tana ƙoƙarin yin picking na call ɗin ta tsinkayo muryar mutane daga ɗaya daga cikin ɗakin dake bayanta suna magana kasa kasa. Fasa ɗaukar kiran ta yi a in da ta ƙasa kunne take sauraransu.

Zaro idanu sosai ta yi a lokacin da ta ji suna shirya shirin yadda zasu harbi Ramish, dik yadda aka yi sun riga masu taron shiga wannan hall É—in, sosai Leesharh ta yi mamakin jin maganganunsu, tasan dai a yadda wannan hall É—in yake wlh idan ba da wani na jikin family ba babu wanda ya isa ya shigo nan wajen, saboda tsaron da aka zuba ko tsuntsuwa bata isa ta gifta a wajen ba ba tare da an harbeta ba, to ta ina waÉ—an nan mutane suka shigo wajen?.

Yanzu ta kara tabbatarwa tabbas da sa hannun na gida a shirin kashe Ramish, tabbas dole da sa hannun na gida, to waye? Ta jefawa kanta wannan tambayar.

Taba tsaka da tinani ta ji ana ƙoƙarin buɗe kofar a fito. A a miliyan ta watsa ta bar wajen ta yi baya, a bayan wasu curtains dake wajen wasu windows kusa da wajen ta ɓuya, a hankali ta ɗan buɗe curtains ɗin tana leƙo kanta dan taga su wanene zasu fito daga cikin ɗakin, daga in da take tana iya gano kofar ɗakin.

Wasu maza ne su biyu suka fito cikin shigar three-piece suit launin ash mai haske, fuskokinsu dik sanye da face mask sannan hannayensu rike da sillent pistol gun, kafafunsu na cikin cover shoes na maza, sun yi shiga irin dai shigar dik wasu manyan baki da suka halacci wannan yaran, sun saje da mutane kenan.

Mamaki ne ya kamata ganin zanen dake wuyarsu na scorpio, shiru ta ɗan yi taba tinanin a in da ta taɓa ganin irin wannan zane a gidan Abbie, tabbas akwai mai irin wannan zane a gidan Abbie, to waye?.

Tana tsaka da tinani sai ta ga sun sa kai sun nufi wajen taron. A hankali ta lallaɓa ta fito ta rufa masu baya, tana tafiya kirjinta na dukan uku uku, a dai'dai wannan lokacin ƙwaƙwalwarta ya tunano mata tabbas wanda ya kawo mata hari daren jiya ma yana da wannan zane a wuya! And bayan shi akwai wani mai irin wannan zanen a gidan.

Cigaba da bin bayansu ta yi ƙwaƙwalwarta yana tinano mata abubuwa kala kala da ya danganci abin zargi a gidan Abbie. Tabbas Hajiya two seater ma tana da wannan zanen, hakan na nuni da zanen na kungiyarsu ce kenan? Ko dai yaya?. Sake tunawa ta yi Ummie ta taɓa yin wani bakon matashi mai irin wannan zanen a wuya, babbar magana.

Binsu ta yi har zuwa cikin hall É—in, tana ganinsu suka koma can baya wajen da ba mutane sosai, a nan suka zauna. Jikinta na rawa ta haura saman stage da Ramish yake, dik da tana shakkarsa tana tsoronsa amma ba zata iya bari a kasheshi ba, dole ta je ta sanar da shi, da sauri ta nufi in da yake.

Sai dai bata kai ga isa wajen ba wasu jiga jigan jami'ai guda biyu suka tareta, dama suna saman stage É—in suna tsaron Ramish É—in ta both sides É—insa dikka, so ganinta yasa suka bar wajen suka je suka tareta.

Sai maganarsa yake yi cikin kwanciyar hankali ba tare da ya kalli in da take ba, yana ji dai jami'ansa suka ce ta koma ƙasa ba zata samu damar yin magana da shi ba, ita kuwa saboda karfin hali sai ta ce masu ita dole tana san yin magana da shi yanzu, tana yi masu magana tana kallan waɗan can mutane su biyun.

Hankalin jama'a ne gabaÉ—aya ya koma kanta, ta jajirce wai ba zata bar wajen ba, kuma tsoronsu kamar ya kasheta, amma ta ce ba zata bar nan ba har sai sun barta ta isa garesa. Zaro idanu Sharifat ta yi tana kallanta, shi ma Abbie kallanta kawai yake yi.

Ganin hankalin jama'a dik ya koma kanta yasa waÉ—an can mutane suka ga sun samu damar harbin Ramish a yanzu, dan haka sai suka ciro bindigarsu cikin dabara, ga face mask a face É—insu saboda sun san akwai cameras a wajen.
Chapter 105 · 0% Book details