Sashe 73
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin san na faÉ—a maki ina kaunar annabi Isa sosai, to shi ne fa na duba cikin litattafan addinin Kiristanci wato Bible dan na duba tarihinsa da Æ´an uwansa, a nan ne na duba tun daga kan Annabi Ibrahim wato daga tushensa kenan, tsawon sati ina bincike ina karantawa, sai da na zo kan Æ´aÆ´an Annabi Ibrahim É—in ne na rikice, abin ya tsaya mun a rai ina san sanin gaskiya".
Ko kaÉ—an bata yi mamakin jin maganarsa ba, kuma bata so ta ji me ya rikita shi ba, dan a tarihin Annabi Ibrahim akwai abin mamaki, tasan bai wuce batu a kan Annabi Isma'il da Annabi Ishaq bane, dama su tarihinsu yana da ban mamaki da É—an rikitarwa, sai ka yi karatu mai zurfi zaka iya ganewa, shi kuma bai zurfafa ba dole ya É—an rikice.
"Kin san me ya rikitar da ni?". Ya katse mata tinani ta hanyar jefa mata tambaya.
Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba..
"Abin da ya rikitar da ni shi ne, ance Annabi Ishaq shi ne rushen bani Isra'ila, shi kuma Annabi Isma'il shi ne tushen larabawa, kuma naga dikkansu ubansu É—aya ne wato Annabi Ibrahim kenan, to ina san ki babbance mun ya aka yi zuri'arsu ta banbanta bayan kuma iyayensu guda ne, basu taso dikka a matsayin tushen larabawa ba, ya aka yi bani Isra'ila suka fito a tushen larabawa kuma?".
Ɗan gyran murya ta yi, wuyarta ya fara ɗan yi mata zafi, saboda jimawa da ta yi tana magana, bata gama samun sauki ba. Abin mamakin kuma shi ne Ronnie fa bai samu damar ganin ciwon wuyar nata ba, sam bai gani ba, shi a tunaninsa ma zazzaɓi ko ciwon kai ya kawota wannan ɗakin, shiyasa kuka ga hankalinsa bai wani tashi sosai ba, da ya gani ai da tashin hankalin da zai shiga abin zai sha gaban tinani, sanin zai shiga damuwa yasa Black Tiger ya yi amfani da magic wajen rufa mashi ciwon ya hanasa gani.
Kuma da ya ga ciwon na zai sanyata yin surutu dayawa ba.
Cikin nitsuwa da sanyin murya ta fara faÉ—in.
"Haƙiƙa Annabi Ishaq da Annabi Isma'il Alaihimus Salam sun kasance ƴaƴan Annabi Ibrahim (AS) ne, amma sun bambanta ta fuskar zuriyarsu da yadda aka danganta su da al'ummomi. Ga bayanin yadda suka banbanta da dalilin da ya sa Annabi Isma'il (AS) ba a danganta shi da Bani Isra'ila ba ya kasance shi ne tushen larabawa".
Ɗan jan dogon numfashi ta yi kafin ta ɗaura da cewa. "Annabi Isma'il (AS) ɗan Annabi Ibrahim (AS) ne daga mahaifiyarsa Hajara, wacce ta kasance daga ƙasar Misra. Zuriyar Annabi Isma'il kuma ta yi ƙaura daga Misra zuwa yankin Makkah, inda aka kafa zuriyar Larabawa ta asali keman, wato Larabawan Adnaniyya. Annabi Muhammad (SAW) fiyayyen halitta kenan shi ma ya fito ne daga zuriyar Annabi Isma'il (AS)".
"Annabi Ishaq kuma, É—an Annabi Ibrahim (AS) daga mahaifinsa Sahra, wacce ta kasance matar farko ta Annabi Ibrahim (AS). Zuriyar Annabi Ishaq ta ci gaba da rayuwa a yankin Sham (Palastine a yanzu kenan) daga cikinsu ne Bani Isra'ila suka fito, waÉ—anda suka hada da Annabi Ya'qub (AS) mahaifin Annabi Yusuf kenan".
"Wannan suna na bani Isra'ila yana nufin zuriyar Annabi Ya'qub (AS) shi Annabi Yaqub É—im shi ne Isra'ila, ainahin sunansa kenan Isra'ila, waÉ—an nan Æ´aÆ´ansa goma shabin nan da suka cutar da kaninsu Annabi Yusuf su ne suka ci sunan bani Isra'ila, wato yayan Isra'ila kenan. Dan haka dik manzannin da suka fito daga cikin zuriyar Ya'qub, irin su Annabi Musa, Annabi Dauda, Annabi Sulemanu, Annabi Isa (AS), duk daga zuriyar Annabi Ishaq (AS) suka fito, kuma sunan bani Isra'ila ya shafesu".
"Annabi Isma'il ba ya cikin zuriyar Isra'ila saboda shi ba É—an Annabi Ishaq ba ne, kuma ba daga zuriyar Ya'qub yake ba. Dan haka Annabi Isma'il (AS) shi ne asalin zuriyar Larabawa waÉ—anda suka rayu a yankin Makkah".
"A taƙaice yadda zaka fi ganewa shi Annabi Isma'il (AS) ya yi rayuwa a Makkah, kuma an kafa al'adar ibadar Hajji tare da mahaifinsu Annabi Ibrahim (AS). Annabi Ishaq (AS) ya rayu a Palastine kuma ya zama tushen addinin yahudawa da kiristoci, ta hanyar zuriyarsa Isra'ila. Saboda haka dik wanda ba ya cikin zuriyar Annabi Ya'qub, ba a kiransa Bani Isra'ila, to kaga Annabi Isma'il (AS) ba shi da alaƙa da zuriyar Ya'qub saboda shi wani reshe ne na zuriyar Ibrahim (AS) wanda ya yi rayuwarsa a yankin Larabawa".
"Alqur'ani mai girma ma ya ya yi magana a kan, cikin Suratul Saaffaat, aya ta 112 zuwa ta 113, Allah ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (AS) ya kasance asalin dukkan Annabawa, amma Allah ya sa zuriyarsa biyu daban daban, haka cikin suratul Maryam Allah ya bayyana Annabi Isma'il a matsayin manzo ga Larabawa, ka fahimta ko akwai sauran abin da baka gane ba?". Ta yi maganar tana kallansa.
Sosai Ronnie ya fahimci dik abin da ta faɗa, kuma hakan tasa ya kara ganin girman Allah matuƙa, ya samu karin ilimi, yanzu yasan cewa ga daga zuriyar da Annabi Isa ya fito, ashe da Annabi Isa da Annabi Muhammad dik kakanninsu guda ne, ɗaya dai ya fito ta gefen Annabi Ishaq ɗaya kuma ya Annabi Isma'il, amma dikkansu kakansu ɗaya ne wato Annabi Ibrahim, lallai Allah da girma sa hikima yake.
Ganin ya yi shiru bai bata amsa bane yasa ta ce. "Ko dai baka gamsu bane Ronnie?".
A hanzarce ya girgiza mata kai haɗe da faɗin. "Sosai na gamsu, jinjinawa girman lamarin Ubangiji nike yi shi ya ja hakan, amma kema ai kinsa ba zai taɓa yiwuwa ki yi wa mutum bayani bai fahimta ba ko? Dole ya fahimta dik toshewar ƙwaƙwalwarsa, magana cike da hujoji yadda yakamata, kai ke dai kin ji daɗi".
Ajiyar zuciya ta sauke, a nitse ta ce. "Kana burgeni Ronnie saboda son neman iliminka, kana san sanin dikkan abin da baka sani ba, ina addu'ar Allah ya kara buɗa maka ƙwaƙwalwarka, ka cigaba da bibiya kana tambaya ta dik wani abin da baka sani na, In Sha Allah idan na sani zan sanar da kai".
Jinjina kai ya yi alamar to, sai ya ji tamkar ya kwace dikkan ilimin dake kanta ya zuba a nasa kan, baya gajiya da neman ilimi shi dai a rayuwarsa.
Cigaba da jefa mata tambayoyi dangane da addini ya yi tana bashi amsa, haka suka kasance cikin farinciki har time da barci ya É—auketa, kin fita daga É—akin ya yi ya zauna yana ya kallanta cike da farinciki, Allah sarki har yanzu kuma bai san da ciwo a wuyarta ba.
Ina kaunar addinina my people's, hakan yasa nake bala'in san part É—in birnin Black world da kuma Sweetie, dan addinina, wayyo musulunci duniya ce jama'a, Allah ka kashemu muna masu yi maka bauta babu gajiyawa, kasa kalmar shahada ta zama kalmarmu ta karshe a duniya.
••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥
KINGDOM OF POWER.
Alƙalamina ba iya nishaɗantarwa da faɗakarwa haɗe da ilmantarwa kawai ya tsaya ba, har da bawa ƴan uwana Sa'a da zai canza ya kuma inganta masu rayuwa, ba sai kin zauna kina ta bani bani bani, za'a yi taro a cikin dangi kece a baya dan baki da shi, miji ya gaji da baki kuɗin shiga ƴan uwa, kina zaune dirshan ba zaki nemawa kanki mafita ba. To Alhamdulillah Allah ya bamu ilimin sanin wasu abubuwa, dan haka na zaɓi sanar da mutane na dan ki fita daga jerin bani bani da kike ta famar ɗaurawa miji, kema ki nemi kuɗinki a dama dake, ko ke budurwace a gida zaki rinƙa yin saarki dan ki ragewa mama da baba wasu ɗawainiya, fatana dai kowacce ta kasance cikin farinciki a rayuwarta duniya da lahira, Allah yasa mu dace, bari in koya maku yadda ake yin sabulun wanke kaya, yana da riba sosai, zaku samu na kanku, kuma shi abu ne wanda ake saya kullum dan wanke dauɗa, a yadda komai ya yi tsada idan kika haɗa shi kika ɗan yi ƙasa da farashi wlh ba ƙaramin alkhairi zaki samu ba, ki jikan na kasa dake a dik abin da zaki sa a gaba sai Allah ya jikanki ya dafa maki kema, wlh zaki samu alkhairi sosai a wannan sabulu, makota zasu yi ta shigowa su saya hankalinki a kwance kina ajiye ƴan kuɗaɗenki ki huta da bin miji ya baki ya baki.
Ga abubuwan da zaki buƙata.
Sabulun wanke kaya yana buƙatar kayan haɗi masu wanke ƙazanta sosai, musamman sinadaran da ke yaki da maiƙo da datti. Ga yadda ake haɗa shi:
Kayan Haɗi. Caustic Soda shi wannan ana amfani da shi ne don samar da tushe (base) ga sabulun. Shi ne na farko. Sai ki samo soda Ash (Sodium Carbonate) Sai sulphonic Acid, wannan yana bayar da kumfa sosai. Sai STPP (Sodium Tripolyphosphate) sai Perfume don ƙamshi. Colorant Idan kuna son ƙara launi. Sai Ruwa don haɗin.
Yadda zaku haÉ—a.
Ki zuba Caustic Soda (10%) a cikin ruwa wanda ya danganta da yawan kayan haÉ—inki, sai ki barshi ya narke na tsawon awa 24.
Shi ma Soda Ash (5%) ki saka shi a nasa ruwan daban ya narke na tsawon awa 12 zuwa 24. Haka shi ma STPP (2-3%) ki narkar da shi a nasa ruwan kamar dai sauran na baya. Idan suka kai waÉ—an nan awanni sai ki É—aukosu, soda ash zaki juye cikin caustic soda, ki gauraya sosai, sannan sai ki juye sulphonic acid, shi ma ki gauraya sosai, sai ki zuba stpp shi ma, a cikin babban waje da zasu samu space zaki zubasu ki haÉ—e fa. Ki zuba ruwan dai'dai da yanayin kayan haÉ—inki, idan kinga ya yi kauri sosai zaki iya kara ruwa.
Ki tabbatar kin juya sosai ya haÉ—e jikinsa ko in ce sun haÉ—e jikinsu. Sai ki zuba perfume and colorant, sannan ki rufe ki barshi na awa 24 kafin ki yi amfani da shi, idan kina son fitar da shi shape by shape zaki iya sayan shapes É—in ki zuzzuba a ciki ki barsu su kame jikinsi.