← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 242

Sashe 66

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kira ya danna tare da kara wayar a kunnensa, bugu É—aya aka É—aga call É—in cikin sauri. Daga É—ayan side É—in Sharifat ta ce. "Hello wanenen?".

Wannan wayar tasa Bilal, Dr Raj, Rizwan sune kawai suke da phone number, shiyasa Sharifat bata ma san wanene bane, wayarta kuma ba irin nasu bane da in sun kira zai baka suna da location É—in in da mai kira ya kiraka haÉ—e da gajeran bayanai a kan mai kiran.

Shiru ya yi kamar na minti ɗaya. Yana jinta ta kara faɗin wanene? Bai yi kamar zai amsa ba, ta sake tambaya na uku, nan ma shiru. Ranta ne ya ɓaci, dama ga damuwar rashin lafiyar Leesharh, sai abin ya kara yi mata yawa, dan haka cikin faɗa ta ce. "Wannan wani irin iskanci ne a kira mutum kuma ba za'ayi magana ba? To koma wanenen kada a kara kirana".

Sai da ta kai aya a zazzaga masifar tata zata katse kiran ne ta tsinkayo sexy voice É—insa cikin nitsuwa ya ce. "Ki kawo mun cappuccino yanzu".

Ai tana daga zaune a bakin bed ɗin Leesharh bata san time da ta miƙe tsaye haɗe da ciro wayar daga kunnenta ba, bata taɓa zaton Yah Ramish bane. Innalilahi wa inna ilahir rajiun shi word ɗin da ta rinƙa maimaitawa babu kakkautawa, gabanta sai faɗuwa yake yi, ƙoƙarin tinano abubuwan da ta faɗa cikin masifar da ta zazzaga ta fara yi ko Allah zai sa ta tina komai ta ji ta yi zagi a ciki ko bata yi ba, yau ta shiga uku shi ne abin da zuciyarta yake faɗe.

Shi kuwa yana gama faÉ—ar abin da ya yi niya ya katse kiran, a hankali ya maido da kallonsa a kan Ummie dake tsayen mashi a bakin kofa, kamar dai akwai muhimmin abin da ya kawota É—akinsa, dan bata zuwa part É—insu sai dole.

"Zan iya sanin abin da ya kawoki nan?". Ya jefa mata tambayar tare da kawar da kallansa daga kanta.

"Da gaske ne wai ka saki Leesharh? And da gaske ne wai ba ita ta yi maka laifi ba?". Shi ne tambayar da Ummie ta jefa mashi, daga ganin face ɗinta kasan bata ji daɗin dawowar Leesharh ba, ta haɗe rai kamar hadari, ranta a ɓace matiƙa. Ta tsani Leesharh, bata so ace sun saketa ba, ta so ne su kasheta, amma sai Sharifat ta ce mata an dawo da ita, ta tambayi Dr Raj meyasa aka dawo da ita ya ce mata ta tambayi Yah Ramish, tana shakkar tinkararsa saboda baya ba da fuska, hakan yasa ta tambayi Bilal, shi ma ya ce ta samu Yah Ramish a wajensa zata samu amsa, tin jiya take san tamnayarsa, amma tana tsoron tinkararsa, da kyar yau ma ta samu kwarin gwiwar zuwa garesa da abin ya dameta, wannan ma sai da wannan friend ɗinta mai kibar nan ta kara mata kwarin gwiwar a kan ta je ta tambaya kada ta damu.

Idan baku manta ba a baya ita da kawar tata sun haÉ—a baki zasu kashe Leesharh ai, to shi ne da Ramish ya kamata sai suka ce ya hutasshesu, sai murna suke yi, rana tsaka kawai murna ta koma ciki, gaza jurar hakan suka yi har sai da suka zo dan tabbatarwa.

"Abin da kika zo tambaya kenan?". Ya jefa mata tambaua.
Wlh Ramish ya tsani Ummie kamar me, babu abin da ta yi mashi kuma, haka kawai bai yarda da ita ba wai.

"Shi ne abin da ya kawoni". Ta bashi amsa.............. Gyarawa ya yi ya kwanta abinsa, ya janyo bargo har zuwa saman jikinsa. "Zaki iya tafiya dan bani da alaƙa da wannan magana da kika zo mun da ita". Shi ne amsar da ya bata, yana gama maganar kuma ya jawo remote ya kashe wutar ɗakin tare da kunna lamps, sannan ya kara gudun Ac.

Tsaye ta yi tana kallansa, ta ƙasa tafiya. A hankali ya lumshe idanunsa kamar mai barci, zubawa face ɗinsa idanu ta yi tana kallo, nan take shaiɗan bakin azzalumi ya fara ƙawata mata kyansa da surarsa, take a wajen ta ji ta kamu da muguwar sha'awarsa. Tashin hankali!!.

Zuciyarta ne ya fara azalzalarta, kun san mutumin fa ba dai kyau ba, jinin Zuhair ai ba wasa ba, ƙasa kawar da kallanta a kansa ta yi, ji take yi kamar ta tafi ta faɗa jikinsa, shaiɗan sai kara rura wutar wannan bakin al'amari yake yi a ranta, ta yi matuƙar kwaɗaituwa da surarsa a wannan dare, dama ita ma idan ba iskanci ba me zai kawota ɗakin santalelen saurayi a cikin wannan dare? Bayan kuma shaiɗan yana nan a tsakani yana yawo tsakanin karya da gaskiya tsinanne.

Wlh ta ƙasa juyawa ta bar ɗakin, infact ta ƙasa iya dai'na kallansa, ga shi lamps suna haska fuskarsa da kyau, dan ta bakin bed ya kwanta, cikin dare ga fara kyakkyawar fuska haske na haskata ai kyau iya kyau, ni kuma na ce dik jarabarki wannan handsome guy na King ya fi karfinki In Sha Allah.

Sallamar da aka yi daga bayanta ne yasa ta yi wani irin razana tare da zare kallanta daga kan Ramish, jikinta har wani tsuma yake yi da sha'awarsa. Wajen da take tsaye a kwai É—an duhu hakan yasa Sharifat bata gane wacece ne a wajen ba, ta dai ga mutum, sai ta yi tinanin ko Yah Bilal ne, dan haka sai ta ce. "Yah Bilal good evening".

Shiru Ummie ta ƙasa iya amsa mata, sai ma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin tana haɗiyar yawun kyan Ramish.

Sam Sharifat bata kawo komai a ranta ba, bata san wacece bace, kawai ta wuce ciki dan ta kai mashi cappuccinon da ya buƙata.

A gaban bed ta durkushe gwiwowinta, kamar zata saka mashi kuka, murya a raunace ta ce. "Good evening Yah Ramish".

Sam bai amsa mata ba, bai ma motsa ba kamar ya yi barci, ita kuma tasan sarai bai yi barci ba, ga zara zaran eyelashes É—insa suna É—an motsawa alamar bai yi barci ba amsawa ce kawai ba zai yi ba, dan haka sai ta É—aura da cewa. "Yah Ramish dan Allah ka yi hakuri ka ji? Wlh ban san kai bane ka kirani a waya shiyasa na yi zafafan furuci".

Nan ma bai motsa ba, kamar babu shi a ɗakin. Miƙewa ta yi ta ɗaura mashi cappuccinon a saman table dake tsakanin sofar a cikin ɗakin, sannan ta nufi waje, dan tasan ko kwana zata yi ba zai amsa mata ba sai time da ya yi niya, gara mata ma ta tafi zai fi mata.

Tana tafiya tana waigosa cike da tsantsar kaunarsa, sansa ne yake kara ratsa zuciyarta, tana san cigaba da kallansa amma babu dama, dan haka ta wuce waje da sauri idanunta suna ƙoƙarin cikowa da kwallah.

Tana fitowa parlon ta ci karo da Yah Rizwan ya fito daga bedroom É—insa rike da cup a hannunsa, yana sanye da white arabs jallabiya, ya yi wani irin rama sosai, da alama daga jinya ya tashi, Allah sarki yana jinyar san Chuchu shi ma kuma Aneesa tana jinyar sansa.

"Lil daga ina kike a cikin wannan daren?". Cewar Rizwan.

Dakatawa ta yi da nufar waje, da sauri ta juyo garesa, bata yi zaton ya dawo gidan ba, dan bata gansa ba, rabonta da shi tin a kingdom of power ranar bikinsa, dik jinyar da ya sha bata sani ba, ba komai yasa hakan ba kuma face in dai ba wajen Ramish ba bata zuwa wajen kowannensu a part É—in, É—an gara ma shi Rizwan É—in da yana sakar mata fuska wani lokaci idan ta rasa abokin hira tana zuwa bedroom É—insa su zauna.

"Wajen Yah Ramish na je kai mashi cappuccinon". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Gyara tsayuwarsa da kyau Rizwan ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Yah Ramish É—in ya yi maki wani abin ne naga kamar kina kuka?".

Kai ta girgiza alamar a'a tana ƙoƙarin shanye hawayen dake san zubo mata. "Mayasaki kuka to?".
"Babu komai Yah Rizwan...........". Tana kai karshen maganar ta rushe da kukan da bata san daga ina ya fito ba, da karfi kukan ya kubce mata.

Da mamaki Rizwan yake binta da kallo, Sharifat kenan sarkin saurin kuka ga raunin zuciya. Da yaga da gaske take kukan sai ya matsa kusa da ita, a saman table na wajen ya ajiye cup É—in hannunsa, sannan ya janyota jikinsa ya rungumeta.

Ita ma rungunesa ta yi tana kara rushewa da kuka. Baya cikin yanayi mai daÉ—i sam, amma haka ya daure ya shiga rarrashinta yana bata baki.

A haka Dr Raj ya zo ya wucesu ya shiga É—akin Yah Bilal dan ya sanar da shi condition da Leesharh take ciki a yanzu, dama tin safe Bilal É—in yake jiran wannan amsa daga garesa.

"Ki yi shiru kinji our lil, kinga fa ke kaÉ—ai ce sistermu a cikin gidan nan, bai kamata ace wani abin zai sanya manake kwallah ba".

Kun san Yah Rizwan Allah ya yi mashi baiwar iya kalamai masu kwantar da hankali, dan haka koma yaya mutum ya kai ga ɗaukar zafi ko ɓacin rai cikin ƴan mintuna zai rarrashesa.

Haka ita ma Sharifat cikin ƙanƙanin lokaci ya rarrasheta har sai da ta yi shiru, sannan ya sanyata murmushi kafin ya raba jikinsa da nata, ya riki hannunta suka nufi bedroom ɗinta.

Sai da ya tabbatar ta kwanta tana farinciki sannan ya juya ya fito, kai tsaye ya koma bedroom É—insa shi ma.
Chapter 66 · 0% Book details