← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 242

Sashe 88

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskar Fanan, cikin murya mai ban tausayi ta amsa da. "Mammie wlh mutuwa zan yi idan har na ce zan hakura da Yah Jaish, wlh ina sansa so mai tsanani, ban taɓa san wani abin kwatankwacin jin sautin muryarsa kawai bama.........."

Katseta Sarina ta yi cikin tsiwa. "Ke dallah ki dai'na jero mana wasu sambatu, ni natsani jin kalaman soyayya a bakin mace, idan kin ga dama ki dafa shi ki cinye, amma kada ki faÉ—a mun, kina son shi e kina son shi ya wadatar, ba sai kin kara mana da yadda kike ji a ranki ba"........... Wai Sarina sai shirin Allah, wannan yarinya da ba dan ma jinin Akka na gudu a jikinta ba wlh ina ga shaiÉ—ancinta sai ya wuci yadda ake tinani.

Shiru Fanan ta haÉ—iye sauran maganganunta tana shessheka haÉ—e da kawar da kallanta daga kan Sarina.

Mammie kam shiru ta yi kamar wadda ruwa ya cinyeta, ta rasa abin faɗe, iya abin da ta sani shi ne lallai a wannan gaɓa ba zata taɓa taimakawa Queen Zarina ba, tun da Fanan ta kamu da san Jaish dole yarta ce zata mallake shi............ Bala'i can, kai my people's me kuke tinanin zai faru? Jaish shi kaɗai mata uku, dik bama wannan ba, ya mammie zata kaya da Queen Zarina?.

Riko hannun Fanan Sarina ta yi. "Zo mu je ɗaki in baki lecture yadda zaki yi maganain Yah Jaish ya dawo tafin hannunki, a wannan karon bama buƙatar Mammie, dan ita bata san salan zamani ba, na da can ta sani, Mammie ke kuma mun baki aiki kawar mana da matar da aka aura mashi ɗin koma wacece".

Tana magana tana janyo hannun Fanan har ta sauko kasan gadon. Cikin shessheka murya a hanzarce Fanan ta ce. "Aunty Sarina bafa wata matar azo a gani bace, wlh tantagaryar Æ´ar kauyece wadda bata da banbanci da dabbobi, kuma kin ganta yar datti, amma kuma wlh tana da kyau sosai, dan ya fini kyau".

Ɗan taɓe baki Sarina ta yi tana ɗaure fuska. "Kin san matar tasa ce? Kin taɓa ganinta ne?".

Da sauri ta amsa da. "E jiya fa a ɗakina momma ta kawosu suka kwana, sai kin gansu wasu kucaku da su ƴan datti, ɗakina ya yi ta wari sai da nasa aka kwashe bedsheet da suka taɓa da dik wani abin da suka yi amfani da shi aka zubar da su, na sa aka zuba tirarika sannan na iya kwana".

"What?!!" Sarina ta faÉ—a cikin É—aga murya. Jinjina kai Fanan ta yi alamar tabbatarwa.
"Muje in gansu". A gadarance ta yi maganar.

Banda idanu babu abin da Mammie take binsu da shi, ta rasa abin faÉ—e, tinanin balai'n dake tinkarota kawai take yi a kan wannan case É—in.

"Aunty Sarina yanzu kam sai dai mu je mu tambayi Neesha ta bamu labarin in da matar tasa take, dan Haulat ta zo da safe ta É—aukesu". Cewar Fanan.
A ƙagare da san ganin Mahnoor Sarina ta amsa da su je wajen Aneesa ta basu labarin ina Mahnoor take. Da wannan shawara suka nufi waje hannunsu cikin najuna, har wa yau dai Sarina tana cikin wannan ɗan iskan shigar tata mai tada hankalin maza.

Mammie da ta afaka duniyar tinani sam bata san lokacin da suka fice daga É—akin ba, mafita kawai take tinawa kanta.

Basu zame ko'ina ba sai part É—in King, É—akin Aneesa kai tsaye suka nufa. A lokacin ta fito daga wanka É—aure da towel a kirji, tana tsaye a gaban mirro, sai tashin kamshi É—akinta yake yi.
Zee tana zaune a saman sofa ta buga uban tagumi tana bin Aneesa da kallo, tana cikin shigar abaya mai bala'in tsada na Aneesa launin ash colar, ta yi matuƙar kyau sosai, ta yi rolling veil a kanta.

Tun sako kafarsu a cikin ɗakin Sarina take bin Zee da wani matsiyacin kallo da in aka yi wa mutum sai ya ji kamar shi ƙasƙantace ne. Ganin haka yasa Zee ta kawar da kanta daga kallonsu, ga shi kuma tana bala'in san kallan nasu, saboda larabawan ainahi suna da tsananin kyau sosai, amma ta lura kamar gabaɗaya familyn King daga mazan har matar dikka tacaccun ƴan duniya ne masu jiji da kansu, babu mai saukin kai da za'a ɗaga idanu a gani ya ɗan tarbi mutum da fuska mai sauki sauki koda ba fara'a ma, gabaɗayansu daga matan har mazan fuska kamar an aiko masu da saƙon mutuwa. Allah sarki bata samu Zunaira da Chuchu bane shiyasa take wannan tinani.

Sarina na ƙoƙarin ambatar sunan Aneesa dan ta tambayeta sai Aneesa ta yi saurin katsesu da cewa. "Aunty Sarina nasan bai wuce amaryar Yah Jaish kuka zo tambayata ina take ba, ai dama nasan sai kin so ganinta, to ba fa wata shegiya bace, ku kwantar da hankulanku, yar kauye ce mara gata wanda ko a ƴar aiki ba zan ɗauketa ba, banza ya fi mun ita muhimmanci, dan haka ni ban ga abin da zaku nemi gani a wajen bama, sai dai fa tashin hankalinku ɗaya ne"....... Dakatawa ta yi da magana tana wurga masu kallo ta cikin mirror.

Aneesa wlh karshe ce yarinyar nan, wannan idan Allah ya taimaketa Yah Rizwan ya shiga hannunta shikenan kuma sai abin da ta so, yarinya ta iskance tun bata kai ko'ina ba, Allah ya ceci Yah Rizwan.

Cike da fadanci Sarina ta amsa da. "Mecece matsala gudan?"..... Shiru Aneesa ta É—an yi na kamar one min, sannan ta amsa da. "Momma, momma tana bala'in kaunar yarinyar dik da take kazama maras gata".

Siririn tsaki Sarina ta je. "Wannan ba matsala bane, ke dai yanzu faÉ—a mana in da take?".

Cikin halin nuna ko in damu Aneesa ta faɗa masu Mahnoor suna ɗakin gyara. Sai dai tasan su Sarina basu isa faɗa da momma ba, dole su gama dik iskancinsu su dawo lallaɓa momma kam, dan ta gagari kowa a gidan, kafun Allah ce ita.

Sai binsu da kallo a sace Zee take yi, dan kyansu take san kallansu ba dan komai ba.

Juyawa Sarina ta yi, har lokacin hannunta rike da Fanan dake ta sauke ajiyar zuciya saboda kukan da ta sha. Har sun kai tsakiyar ɗakin zasu nufi waje Sarina ta dakata, juyo da kallanta a kan Zee ta yi. Wani irin kallan walaƙanci ta watsa mata up and down kafin ta ce.
"Neesha wacece kuma wannan?".

Aneesa na cigaba da gyaran gashin kanta ta amsa masu da. "Bakuwar second dad ne".

"Wannan kucakar? Daga ina ya samota?".Sarina ta sake tambaya........... Tara gashin kanta Aneesa ta yi ta É—aure, sannan ta juyo garesu da kyau, ta É—an jingina bayanta da jikin mirror kaÉ—an, sillent talk ta yi wajen cewa.

"Wannan ne kuma zaki iya tambayarsa, bani da alaƙa da hakan kuma bana san yin alaƙa da hakan shiyasa ban nemi sanin labari a kan meyake tsakaninsu ba". Tana kai karshen maganar ta wuce dressing room ɗinta.

Harara Sarina ta bi Zee da shi kafin tasa kai ta nufi waje, kai tsaye É—akin gyaran suka nufa. Sai dai ko da suka je mama Haulat ta hanasu shiga, saboda doka ce momma ta saka bata yarda ta bawa kowa daman ya shiga wannan É—aki ba har sai su Mahnoor sun fito.

Tatas Sarina ta yi wa mama Haulat, rashin kunya tas ta yi mata wanda ko kare ba zai sinsina ba, sannan ta ja hannun Fanan suka ta fi tana faÉ—i ko mama Haulat zata mutu yau ba sai gobe ba sai sun shiga É—akin nan sun ga Mahnoor, ta jira dawowansu a karo na biyu.

Ko sannu mama Haulat bata ce masu ba har suka fice, wucewa ta yi ta rufo kofar da Mahnoor suke ciki É—in, ta zo ta É—auko kayan marmari dan ta kai wa Jaish yana lambu.

Allah sarki mama Haulat baiwar Allah ƴar amana, matar nan tana da ƙoƙari sosai, ba ƙaramin fama ta sha da Mahreen ba kafin Mahreen ta yarda a shafa mata haɗin gyaran jiki a jikinta, har zagin mama Haulat ta yi, amma dik da haka bata tuna ta wani damu ba, sai ma hakuri da ta rinƙa bawa Mahreen ɗin.

Abin dariya kuma shi ne Mahreen bata taɓa yarda ta shiga toilet ita kaɗai har sai mama Haulat ta rakata, wanka ma ita ta yi mata yau, dan tsoron toilet ɗin take ji, sai su manne waje guda ita da Mahnoor saboda tsoro. Dik da haka mama Haulat ta jure bata wani damu ba.

A ɓangaren uncle Jahiz kuwa, yana barin wajen su Zee ya dawo in da momma take ya karɓi babyn Khadija wanda ya sanya mashi suna da Junior, haka yake kiran yaron, Allah ya saka mashi kaunar babyn nan sosai. Yana ɗaukansa ya wuce wajen King a fada da shi, a nan suka je rabon zakka.

Sai dai fa dik hankalinsa yana a kan Zee, tinaninta kawai yake yi, yana jin kamar ya tashi ya zo ya sake dubata, dan yana ganin kamar bata jin daÉ—in zama da Aneesa, saboda yasan halin Æ´aÆ´an nasa, haka dai yake ta sake sake ya kasa tsayar da abu guda.

Da yamma ta yi cikin nitsuwa ya yi wanka ya canza kaya, ya bawa mama Haulat junior ta yi mashi wanka ta shirya shi cikin shiri na musamman, sannan ya koma ya karɓesa, ya nufo wajen Zee a ɗakin Aneesa.

Babu kowa a cikin É—aki, ita kaÉ—ai, ta takure jikinta waje guda, tana kwance saman sofa barci ya yi awon gaba da ita. Ciki ya kariso, a gaban sofar ya tsaya yana kallan face É—inta, har sai da ya ji faÉ—uwar gaba lokaci guda, ji ya yi kamar kada ya tasheta, amma kuma ya tina tana san ganin Æ´ar uwarta, hakan yasa ya fara ambatar sunanta a hankali hankali.

Da yake bata da nauyin barci sai ta farka. Ganin shi a kanta yasa ta yi saurin miƙewa zaune tana janjayo kayan jikinta ta gyara. Ɗan kawar da kallansa a kanta ya yi yana faɗin. "Sorry na tasheki daga barki ko?".

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da ba komai. Sai wani gyara jikinta take yi tana takure kanta bayan komai nata a rufe yake.
Chapter 88 · 0% Book details