← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 242

Sashe 118

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin zafa ya nufi sauka kan stage ɗin ya ƙarisa gaban Hoorain sai ji ya ji an rike hannunsa ta baya, cikin zafa ya juya dan yaga wanenen?. Yana juyawa suka yi ido huɗu da Aunty MieMie, ƙara ɗaure fuska sosai ya yi yana wani huci yana san kwace hannunsa, shi kuwa Hoorain yana tsaye a kan kafafunsa ya sunkuyar da kansa ƙasa zuciyarsa tamkar zata yi bindiga.

Cikin dakiya King ya ce. "Abbas kama shi ku tafi".......... Matsawa uncle Abbas ya yi yana riƙosa suka tafi, ba dan King ba da bai ga abin da zai sa yau ya kyale Hoorain ba.

Kallan Aunty MieMie King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan commander Zafar, tsab King ya gama fahimtar soyayya ce take a tsakanin Hoorain da Zunaira, wannan bakincikin ita ta hana shi yin magana, dan ya fahimci Zunaira tana san Hoorain sosai, shi kuwa ko mutuwa zasu yi bai ga dalilin da zai sa ya bawa Hoorain Zunaira ba, dan bai shirya ganin yarsa a matsayin karamar bazawara ba, kowa dai yasan mayaƙa rayuwarsu babu tabbas, a kowani lokaci suna iya mutuwa, kuma ko da King ya ƴanta Hoorain ɗin ya zama ɗan ahali ba zai taɓa zama mai ƴanci da rayuwarsa ba, saboda ya riga ya tarawa kansa tarin makiyan da ba zai iya faɗa dasu domin ƙwatar kansa ba, dik in da ya je masu san ɗaukar fansa a kansa suna kewaye da shi, dan haka shi King yasan me matsalar, dole kuma ya dakatar da wannan soyayya cikin sauri tin kan abin ya yi nisa ya fi karfinsu.

Hmmm King a ganinsa soyayyarsu bata yi nisa ba kenan, my people's mu gaya mashi wannan soyayya ta fi shekaru 8 ne ko dai mu barshi su masoyan su nuna mashi karfin soyayyar dake zuƙatansu?.

Tsit fada ya yi kowa idanunsa a kan King, jiran word É—insa kawai suke yi, saboda babu wanda ya isa ya yi magana idan ba ya yanke abin da ya dace a kan wannan case É—in ba.

Commander dai ji ya yi ƙafafunsa sun gaza ɗaukarsa, hakan yasa ya koma saman sofa ya zauna tare da sunkuyar da kansa ƙasa, domin shima ya rigada ya gane Hoorain ya fahimtar da Zunaira abin da yake ransa, idan baku manta ba dama commander yana hana shi kusantar Auta, ashe dik irin wannan yake gudun mashi, so yanzu ya fahimci soyayya suke yi da Auta, kuma ya fahimci King Zuhair ma ya fahimci hakan, Allah sarki yasan ko mutuwa Hoorain yake yi ba za'a taɓa bashi auren Auta ba, saboda ba kowa ma yake yarda ya bawa mayaƙa yayansa ya aura ba bare ita da take matsayin gimbiya, tab ai abune wanda sai in Allah ya ƙaddara akwai aure a tsakaninsu ne Allah zai kawo sanadi, amma kam akwai matsala.

Good 10 mins King ya É—auka shiru yana binsu da kallo kafin ya É—an yi gyaran murya, with sharp voice ya fara magana kamar haka.

"I think ka fahimci abin da na fahimta a tsakanin yaran nan ko Zafar?".
Dum dum commander ya ji kirjinsa ta buga, dan ya fahimci in da King ya dosa. Da kyar ya iya jinjina kai cikin girmamawa ya amsa da ya fahimta.

"Ba sai na faÉ—a maka hukuncin da ya dace da Hoorain ba, ka fi kowa sani tin da tare da kai aka kafa waÉ—an nan dokoki da hukunce hukuncen, dan haka ina mai baka umarnin da ka hukunta shi yadda yakamata, daga karshe ka datse alakar dake tsakaninsa da Zunaira bana san sake yin magana a kan hakan!!".

Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, haba King, wani irin zalinci ne wanna? Ta ya za'ayi kace uba ya hukunta É—ansa bayan kasan hukuncin yana da tsauri da tsanani sosai? Wannan babban zalinci ne wlh.

Tamkar commander zai yi kuka, idanunsa sun tsananta ja sosai, kansa a ƙasa cikin girmamawa ya ce. "Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, dan girman Allah ina neman alfarman da abawa wani daga cikin mayaka damar su hukunta Hoorain, ba zan iya hukunta shi ba".

Wlh dik taurin zuciyar Aunty MieMie na jinin Modarawa sai da ta ji zuciyarta ya karaya a wannan gaɓa, saboda abin da ciwo ace uba ya hukunta ɗansa hukunci mai azabtarwa, kuma dole ya yi yadda hukuncin take a rubuce idan ba haka ba dikka a azabtar da su, innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, wannan abin akwai taɓa zuciya.

"Amma dai kasan bana magana biyu ko Zafar?". Cewar King. A tinanin King fa idan ya sanya commander ya hukunta Hoorain to tabbas Zunaira zata fita a ransu gabaÉ—ayansu, dan uba da É—a ba wasa ba, shiyasa ya yi masu irin hakan, burinsa kawai ya yanke alakar Hoorain da Auta. Hmmm akwai matsala.

Shiru commander ya sunkuyar da kansa yana jin wani irin raɗaɗɗi na ratsa zuciyarsa, haƙiƙa bai taɓa yin danasanin zamansa da su King ba sai yau, ya ji da ace shi ba musulmi bane bai san girman Allah ba da babu abin da zai hana ya kashe kansa a kan ya yi wa Hoorain wannan hukunci, amma bashi da zaɓin da ya wuce ya yi mashi ɗin, dan haka sai ya miƙe jikinsa na kermar tashin hankali. Da kyar ya iya taka kafafunsa ya isa in da Hoorain yake tsaye. Guyson ne ya juya da sauri ya bi bayan uncle Abbas da ya fita da Jaish, dan kun san guyson akwai tausayi, ya ji bashi da kwarin zuciyar kallan commander Zafar a halin da yake ciki.

Aunty MieMie ce ta yi saurin juyowa ga King da nufin ta taushesa ta bashi hakuri wani ya hukunta Hoorain ba mahaifinsa ba. Sai dai tana ƙoƙarin buɗe baki King ya ɗaga mata hannu fuskar nan tasa babu alamar wasa, ya ɗaureta tamau kamar hadari, ya ɗaga mata hannu alamar ta yi mashi shiru.

Zuciyoyi dayawa sun karaya a cikin fada, dayawan jama'ar dake ciki sai da idanunsu ya tara ruwa mai É—umi, dik mai imani sai ya tausayawa commander idan ya gansa.

Riko hannun Hoorain ya yi, jansa ya yi suka juya suka nufi hanyar fita, da kyar yake jan kafafunsa saboda rashin kwarin jiki.

Da kallo kowa ya bisu, warriors dake cikin fada kuwa daÉ—i suke yi suna faÉ—in Allah ya kama commander yau, ba ya iya hukunta Æ´aÆ´an mutane ba, to yau abin ya juyo ta kansu ai shikenan shi ma ya É—anÉ—ani yadda iyaye suke ji a lokacin da yake azabtar masu da Æ´aÆ´a.

"Ku shirya mana motoci zuwa hospital duba Zunaira, sannan ku ɗauki Taheer ma zuwa hospital". Shi ne abin da King ya faɗa kafin ya koma saman kujerarsa ya zauna yana jin wani irin kuna a ransa, wai Hoorain da Zunaira suna soyayya, wannan abin ya kona mashi rai matuƙa, har ji ya yi kansa na sara mashi.

Dik wannan abin da yake faruwa a cikin gida babu wanda yake da labari sai Mammien su Sarina and mama da suke da c.i.d, kun san suna da masu saka masu ido a lamarin fada, so har sun samu information a kan abin da yake faruwa.

JAISH kuwa kai tsaye part É—insa uncle Abbas ya wuce da shi, sai huci yake yi, wlh ba dan King ba yau bai ga abin da zai hana shi yi wa Hoorain dukan mutuwa ba. Tab yadda Jaish fusata haka kuna tunanin ko mutuwa Hoorain yake yi zai yarda ya bashi auren Auta kuwa? Hmmm akwai dai matsala.

A bakin bed uncle Abbas ya zaunar da shi yana tausan shi a kan ya yi hakuri. Hannu ya É—aga tare da cewa uncle Abbas. "Second dad it is okey, zaka iya tafiya babu komai". Yadda ya yi maganar yana fitar da huci mai zafi zaka iya fahimtar har yanzu bai huce ba.

Kin matsawa daga kusa da shi uncle Abbas ya yi, dan ya fahimci komai zai iya faruwa idan ya tafi ya bar shi a haka. Dan haka sai ya zauna tare da shi ya cigaba da rareashinsa.

Shi kuwa guyson part É—in momma ya wuce kai tsaye dan ya faÉ—a mata abin da yake faruwa, zuciyarsa ba zata iya É—aukar hukuncin da King ya yankewa commander Zafar and Hoorain ba, abin akwai ciwo sosai, hukuncin ya yi masu tsauri sosai, ace uba ya kai É—ansa É—akin duhu dan hukunta shi, bayan ya gama hukunta shi da kansa kuma zai jefa shi a gidan yarin masarautar tare da horo mai tsanani bayan na É—akin duhu, wlh commander ba zai iya É—aukar wannan musifar ba, dole su momma su saka baki ko za'a samu sassauci.

Yana ƙoƙarin shiga part ɗin momma ciwonsa ta tashi, wani irin azabbabben murɗa mashi da cikinsa ta yi ne yasa ya dafeta da karfi yana sakin ihu mai ɗan sauti kaɗan. Wani irin numfashi ya fara fitarwa da zafi zafi yana kara dafe jikin bango, a hankali ya fara jujjuyawa ko zai ga wani a kusa ya taimaka mashi, dan ko motsawa ba zai iya yi ba.

Dai'dai lokacin Mahnoor ta fito daga part ɗin Jaish cikin shiga ta girma wato ta matar Prince wanda mama Haulat ce ta ƙawata mata shigar, so zasu je gaishe da Akka ce ita da Chuchu, shi ne ta ce bari dai ta fara duba momma kafin su je wajen tsohuwa.

Chuchu na can suna sallama da Yah Jawad zai tafi office, sai aikin rungume juna suke yi kamar ba gobe.

Ganinsa ya dafe bango yana hawaye yasa Mahnoor ta yi saurin nufarsa tana tambayarsa lafiya kuwa?. Riƙo hannunta ya yi ya kasa yin magana, da hannu ya nuna mata part ɗin monma a kan ta taimaka mashi su je can.

Daddagewa ta yi tasa karfinta dikka zata taimaka mashi, gabaɗaya ya sake mata nauyin jikinsa saura kaɗan su zube ƙasa, da kyar ta iya kamewa ta iya ɗaukar nauyinsa, sai kuka yake yi sosai yana cigaba da dafe cikinsa da hannu ɗaya.

Ya yi mata nauyi sosai, amma haka ta daddage ta tallabosa da kyar suka nufi part É—in momma. Allah ya taimaketa momma tana parlor zaune ita da Mahreen and Zee suna hira, momma kenan, mai farar zuciya, ta haÉ—e Æ´an'matan dikka ta rikesu abinta, babu kyara ko kyama.
Chapter 118 · 0% Book details