Sashe 132
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kara yin ƙasa da murya sosai ya yi, cikin salo mai tafiya da imani sosai ya ce. "Har da ni baki sha'awar yin soyayya ko kuma ban da ni?". Ya kai karshen maganar tare da ɗaga mata gera guda saboda yaga tana kallansa............... Ya subhanallah, Zee bata san lokaci da ta kara waro idanunta haɗe da afkawa duniyar tinani ba.
Hannunsa dake saman wall glass É—in ya dawo da shi saman face É—inta, a hankali ya É—an goge mata hawayen da ya yi saura a face É—inta, wato Dr Raj ba iya Dr bane kawai, shahararren É—an love ne, kawai dama bai samu wadda ta sace zuciyarsa bane yasa yake wani jiji da kai, yanzu ba ga shi ya yi la'asar har da rarrashi ba.
"Answer me mana, har da ni baki sha'awar yin soyayya?". Yadda ya yi mata maganar cikin wani irin salo sai da yasa Zee ta yi saurin girgiza mashi kai alamar a'a ban da shi, shi kam za'a iya yin soyayya da shi, bata san ta girgiza mashi kai É—in ba, kawai salon maganarsa cikin natsuwa mai kwantar da hankali yasa ta bashi wannan amsa.
Wani irin sanyi ya ji ta ratsa zuciyarsa. Matsawa kusa da kunnenta sosai ya yi, cikin raÉ—a yana rike da hannunta yana kuma kallan face É—inta ya ce. "Kina so na?". Ya yi maganar yana kashe mata idanu É—aya yana É—an canza yanayin face É—insa, dan yana fargabar amsar da zata iya bashi, ba zai iya É—aukar ta ce bata san shi ba, dik da yasan mawuyacin abu ne ta ki yin accepting É—insa, dan jinin Akka fa sai dai mata su kawo kansu garesu, basa tambayar soyayya su, a karon farko ya roki soyayya a hannun Æ´ar Nigeria, yo to mu Nigerians dama wasa ne? Haba dole ka roki soyayya malam Dr Raj, dan mu É—in na daban ne malam.
Shiru Zee ta yi ta kasa magana, da alamu kamar suman tsaye ta yi, wato a duniyar nan idan Allah ya kaddara ga mijinka fa shikenan babu wanda ya isa ya canza, idan ba wata kaddara ta Ubangiji ba fisabilillah ina Zee ina Dr Raj? Mutanen da ƙasa ba ɗaya ba, babu abin da ya haɗa, babu dangin iya bare na baba, kaddara kawai ya kawo ƙasar, shi kansa Dr Raj kun san suna shafe shekaru 6 zuwa sama basu leƙo kingdom of power ba, amma da Allah yasa dole a kaddararsa akwai haɗuwa da Zee sai ga shi ya zo ta sanadiyyar ciwon guyson, wato komai yana da sanadi, jama'a kawai ku bawa Allah zaɓi ku koma gefe ku haɗe hannayenku ku jira iko na Allah ku ga me zai faru.
Shiru ta tsaya ta kasa bashi amsa, dan bata da abin faÉ—e, shi ma shiru ya yi yana jin zuciyarsa na harbawa da karfi yana jiran jin amsarta....... Kuna tinanin Zee zata amsa soyayarsa kuwa?.
••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥
RangaÉ—a kwalliya Sarina ta yi cikin wannan É—an iskar shiga tata na fidda tsiraici, ta yi kyau a idanun Æ´an iska kam, amma a idanun masu koyi da Manzon raham tabbas a shaiÉ—aniya zasu kalleta. Ta É—aura silky-c a kanta, ta zubo jelar gashinta har gadan baya. Sai kuma ta É—auko alkyabba ta sanya a jikinta saman kayan, sai zuba kamshin wani shu'umin perfume da Mammie ta bata ta sanya take yi.
Na ce ba, mu faÉ—awa Sarina cewa kafin ta yi irin wannan shigar domin nunawa Smart surar jikinta Heleena ta rigata yi ne ko dai mu bari shi da kansa ya bata gurbi irin wanda ya bawa Heleena?
Kai tsaye family part ta nufo, tana taku tamkar wata hawainiya, kamar bata san taka ƙasa, ga wani shegen takalma high heel da take sanyawa. Kai tsaye part ɗin momma ta nufa cike da yauki da yanga haɗe da duniyanci.
A tinaninta Smart yana part na momma, sai da ta shiga taga akasin haka, momma kawai ta samu zaune a saman bed ta buga uban tagumi tana tinanin yadda zasu karkare da King yadda ya É—auki zafa haka, tana san zuwa part É—insa amma tana shakkar abin da zata tarar a can.
A fakaice Sarina ta bita da kallan banza da harara a cikin zuciyarta tana saƙa ta tsani mommar nan kamar me. (Amma kuma suna san jinin momma kamar su mutu, ni narasa wannan bala'i wlh.)
Cike da makirci ta ce. "Momma barka da dare".
Da yake yau momma bata a cikin mood mai daÉ—i sai ta amsa mata da yauwa kawai. Zama ta yi a saman sofa, tana san tambayar ina Smart yake tana kuma fargabar amsar da momma zata iya bata.
"Sarina kira mun Omar ko Omaid su zo su kaiwa yayanku cappuccino kada dare ta yi". Cewar momma. A hanzarce ta ce. "Wani yayan namu?". A takaice momma ta amsa da. "Babban yayanku". ...... Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, a ƙagare da san ganinsa ta ce. "Momma kawo kawai in kai mashi".
Shiru momma ta ɗan yi kafin ta ce. "Anya kuwa Sarina! Yayanku fa sha'aninsa yana da wuya ne, kada in turaki ya ɓata maki rai, da kin bari su Omar da suka saba da shi sun kai mashi". ........ A hanzarce ta fara girgiza kai kafin ta ce. "Momma babu abin da zai faru In Sha Allah, zan kai mashi, ai yayanmu ne". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye tana wani rawar kafa.
Momma kamar dai ba zata bata ba, amma sai ta ce kila tun da Smart bako ne a nan bari ta bata kila ba zai yi mata komai ba. Dan haka sai ta nuna mata in da cappuccinon yake ta kuma faɗa mata cewa Smart ɗin yana part na Jaish. A hanzarce ta wuce ta ɗauka tana sauke ajiyar zuciya, faɗi take a ranta buƙatarta ya biya, domin kuwa tana haɗa idanu da shi idan ya shaki kamshin perfume ɗin nan nata shikenan ya gama yawo, ya dawo tafin hannunta, turare ne mai karfin sihiri da in ya shaka sai yadda ta yi da shi kuma, shiyasa kuma ga take neman haɗuwa da shi a taren nan ta kowani hali, to ga dama ta samu.
ÆŠaukar cappuccinon ta yi ta nufi waje da sauri, sai wani rawan kafa take yi, ita a dole zata je wajen saurayi. Me kuke tinanin zai faru? Shin zata samu nasara a kan da kuwa?. Mu je dai zuwa.
•••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥
A ɓangaren mama kuwa, sun jima a parlourn kafin ta iya miƙewa jiki ba kwari ta nufi part ɗinta, uncle Taheer da karyayyar hannunsa shi ma ya miƙe ya nufi nasa bedroom ɗin, jinyar kansa fa yake yi, amma dan balai'n san jin gulma ya fito dan ya ji family dik sun haɗu a parlourn.
Miƙewa ita ma Aneesa ta yi ta nufi bedroom ɗinta dan ta je ta kwanta, ita ko ajikinta babu abin da ya dameta.
•••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥
A hankali hankali Mahnoor ta fara jin cikinta yana murÉ—a mata, É—an dafe shi ta yi tana tinani da fargabar kada ya fito toilet ya sameta kwance mashi a bed. Da kaÉ—an da kaÉ—an ciwon cikim nata ya É—an fara karuwa. Hakan yasa ta É—an juya domin ta kwanta ta É—ayan jefen nata, a tinaninta hakan zai sa ciwon cikin ya ragu.
Juyowa da zata yi suka yi 4 eyes da shi yana tsaye wajen mirror, tin ɗazun ya fito daga toilet ɗin bata lura ba, ya shafe jikinsa da mayika ya shirya cikin sleeping dress masu kyau da tsada, sai kuma me? Ya ƙasa manta surarta a ransa, ya zo zai haye bed ɗinsa ne ya sake yin kyakkyawan gani cikin wannan shiga nata, ga shi tana kwance a miƙe, dama ta ɗazun bata gama sakinsa ba, ga idanunsa nan jajir kamar wuta, so abar bata sake shi ba, sai ta kara ninkuwa sosai.
Shiaysa ya tsaya a wajen mirror ya kasa ƙarisawa wajen bed ɗin, dama da nufin ya zo ya korata ya fito daga dressing room ɗinsa, ganinta a irin wannan shiga yasa ya kasa ƙarisawa wajen, ya yi tsaye yana karewa jikinta kallo.
A zabure ta miƙe zaune tana kallansa. Yadda ta miƙe sai ji ya yi zuciyarsa ta motsa, ya ji kamar ya ce mata ta koma ta kwanta, amma ya ƙasa faɗe. Zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin ta yi tana kallansa ta kasa kawar da kallanta a kansa, dik kunyarsa da take ji ta kasa cire kallanta a kansa saboda kewarsa da ya addabama zuciyarta.
Tana ƙoƙarin miƙewa cikinta ya yi wani irin murɗawa da karfi wanda sai da yasa ta yi saurin dafe shi ta saki yar kara haɗe da komawa ta zauna ta fara miƙewa. Ai yana tsaye a lokacin da ta yi wannan yar kara ta dafe cikin nata tamkar jikinsa haka ya ji, har ɗan zabura ya yi.
Idanunta ne suka cicciko da kwallah tana cigaba da kallansa, shi ma ya ƙasa zare kallansa daga kanta. Ƙasa da murya ta yi, da yake tana jin ciwo sai muryarta ya yi kamar shagwaɓa take yi mashi. "Yah Jaish cikina ciwo yake yi mun". Tana gama faɗa hawayen da suka cika mata idanu suka zubo. Yanzu ita ma ta fara bin bakinsu Chuchu tana ce mashi yaya ba Hamma ba.
Shiru bai matsa daga in da yake tsaye ba sai da ya ga da gaske take kukan, sannan ne ya tako cikin natsuwa ya matso kusa da bed ɗin. Kamar zai taɓata sai kuma ya fasa, muryarsa tana ɗan sarkewa ya ce. "Tashi muje hospital sai a dubaki tin dare bai yi ba". Yana kai karshen maganar ya nufi keys set ɗinsa, key motar da yake da ra'ayin hawa ya ɗauka ya nufi kofar fita.
Yana gab da fita ya tsinkayo muryarta cikin kuka ta ce. "Yah Jaish ba zan iya tashi ba". Cak ya tsaya, dan yadda ya ji muryarta ta kara tada wani hatsaniya a cikin zuciyarsa. A hankali ya juyo, gabaÉ—aya ya rasa meyake damunsa, ya gagara yi mata faÉ—a ko tsawa, sai wani tausayinta da ya ji ya kama shi. A hankali ya tako ya dawo in da take zaune.