← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 216 OF 242

Sashe 216

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗauko school back ɗinta ta yi tare da wurga mashi ta wuce gaba tana harararsa. Capke jakar ya yi, a hanzarce ya rufa mata baya. Yana isota ya riƙo hannunta. "Yau sai ɓata rai kike yi? Na yi maki wani laifi ne?". Kin kula shi ta yi, wasa wasa har suka shiga mota, sai magana yake yi mata taki amsawa har suka isa school, motocinsu na parking a parking lot na school ɗin bata jira sun buɗe mata kofar motar ba ta ɓalle ta fito abinta. Da ido Ronnie ya bita yana mamaki, jikinsa dik ya yi sanyi, a cikin ransa ya ce ko dai Black Tiger ne ya hanata yin magana? Haƙiƙa ya shiga damuwa sosai da bata kulasa ba.

Ya yi nisa a cikin tinanin nasa, sam bai san time da ta ɗauki jakarta ba, sai ji ya yi ta manna mashi hot sumbata a kumatu tana faɗin. "So much love my lovely bro". Ta faɗa tana murmushi haɗe da juyawa ta nufi hanyar tafiya. Ai bai san time da ya saki ƙayataccen murmushi game da sauke ajiyar zuciya ba, da ya ɗauka fushi take yi da shi.

"You're the only my brother that making me happy anytime, I really love you my pleasure". Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba, tana cigaba da tafiyarta.

Tin da ta fito idanun gabaÉ—aya student a kanta, su kansu sun shaida da ta yi fitina yau É—in nan, kalar kyanta ma na daban ne. Dik kyan mutanen birnin sun jinjinawa nata. Kasa hakura ya yi da jin kalamanta, da gudu ya fito ya bi bayanta. Sai da ya kamota ya manna mata sumbata a kumatu, sannan ya juya ya koma mota yana yi mata fatan alkhairi tare da fatan ta kula da kanta kuma ta yi karatu sosai. Da okey ta amsa tana yi mashi bye bye, ji ya yi kamar kada ya tafi ya barta, amma haka ya daure suka juyo suka dawo gida.

Dik sai ya ji gidan babu daÉ—i da bata nan, dan haka wunin cikin É—aki ya yi, ya takure kansa har zuwa lokacin tashinsu school, tin da sauran lokaci ya tsara wanka tare da shiri cikin sport wear É—insa ya nufi school É—in nasu. A lokacin da suka iso school É—in tana zaune ita da wasu Æ´an'mata kyawawa guda biyu da ita uku, zaune suke a garden na school É—in nasu suna hira, basu komai a class ne suka fito waje. Yana zuwa kuma aka buga tashi. Fitowa wajen motar ya yi tare da jingina bayansa a jikin motar yana jiranta. Tana jin an buga tashi ta yi saurin yiwa Æ´an'matan sallama tare da wucewa, dan tasan already ya zo, baya lattin zuwa É—aukarta.

A tare ƴan'matan suka ce zasu rakata, kowa son ta yake yi, suna san yin ƙawance da kyakkyawa, ita kuma very friendly take, bata da matsala. Amince masu ta yi suka rakota wajen motar, yana tsaye tin daga nesa yana kallonsu, sun nufo shi, tamkar wata a cikin taurari haka ta kasance a cikin waɗan nan ƴanmata, dik ta haskesu, ta dishashe haskensu da nata. Tin bata ƙarisa isowa ba ya buɗe mata hannu, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana murmushi.

Kallan juna ƴan'matan suka yi, lokaci guda suka sha jinin jikinsu tare da komawa gefe suka tsaya shiru, sun gane Ronnie sarai, dik wanda yake cikin birnin dole ya sansa. Basu taɓa zatan Sweetie daga Black Tiger Empire ta fito ba, lallai yanzu ta kara samun girma da daraja a idanunsu fiye da a baya, dole su yi respecting ɗinta sosai, tab ai ta wuce class na ƙawance da su, dama tin da yake kawota baya fitowa shiyasa basu san mai kawota da kuma mai ɗaukarta ba sai yau.

"Bro this is my friends Loosi and Rose". Ta faɗa tare da raba jikinta da nasa, sannan ta ce. "Rose this is my brother". Ta yi maganar tare da nuna shi da hannu!. Cikin girmamawa suka zube gwiwowinsu a ƙasa game da yin ƙasa da kai suka fara zuba irin gaisuwar da suke yi wa manyansu a birnin, wato dik wanda ya fito daga cikin Empeir ɗin haka suke gaida shi.

Ɗan ɗaure fuska ya yi kafin ya yi masu alama da hannu a kan su miƙe ba tare da ya yi magana ba. Ba musu suka miƙe tsaye, da hannu ya yi masu alama da su tafi. Cikin hanzarin suka bar wajen suna sake waigosa, Allah ya gani Ronnie burin dik wata yarinya dake cikin wannan birnin ne, har manya kwaɗayinsa suke ji.

Riƙo hannunta ya yi, ya shige cikin mota yana janta ta shigo. Tana ƙoƙarin shiga daga bayanta sai ta ji an ce. "Omaish O Mutallab ka book ɗinki". Da sauri ta juyo, shi ma Ronnie ɗan leƙowa ya yi dan ya ga wanenen?. Wani matashi ne da a kallah zai iya kai 19 to 20 haka, uniform na seniors ne a jikinsa, a Ss3 yake, ta mance da book ɗinta ne a set ɗinsu wajen small library ɗin nasu, shi ne ya biyota da shi, dama burinsa ya samu wani abin da zai haɗa shi magana da kyakkyawar nan, shiyasa yake yawan bibiyarta, dik in da take sai ya je wajen, sai Allah ya yi yau ya samu damar yin magana da ita, ta hanyar ta kammala karatu ta bar book ɗin a wajen saboda sauri!.

Ƙarisowa ya yi in da take, miƙa mashi hannu ta yi ya miƙe mata book ɗin. "Thank you". Ta faɗa tare da juyawa. "Am baki ji ba Omaish". Ya faɗa cikin sanyin murya. Juyowa ta yi tare da ɗaga mashi gera irin alamar lafiya?.

"Seriously you're so cute and pretty". Ya faɗa yana ɗan shafa kansa. Ɗan sake face ɗinta ta yi kafin ta ce. "Thanks". Ta faɗa zata sake juyawa sai ya katseta da cewa. "My name is Michael, can we be a friend?". Ya yi maganar tare da miƙo mata hannu wai su yi musabaha, daga haka sai sun zama abokai, dik abin da yake yi bai lura da Ronnie dake kusa da su a cikin mota yana kallonsu ba.

Yana miƙo mata hannu Ronnie ya zuro nasa hannun ya capki nasa tare da fitowa waje daga cikin motar. Ai yana ganin Ronnie a zabure ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta tare da buga hannunsa a kirji, sannan ya risinar da kai kasa alamar girmamawa. Ɗaure fuska sosai Ronnie ya yi, yanzu yasan darajar mata, saboda musulunci ta ratsa shi matuƙa.

"Michael I don't want to see you close to my sister again!!". Ya faɗa with harsh voice, cikin bada umarni, babu wasa a tattare da shi, da alama ya san kishi a yanzu!!. Da ido ya yi mata alama da ta shiga mota, da sauri ta faɗa ciki tana ɓoye murmushin dake san kwace mata bayan taga yadda ya ɗaure fuska. Bata san me da me ya faɗawa Michael ba tana daga ciki ya shigo ya sameta bayan ya gama kenan, ta so jin yadda zasu kare, sai dai ina, tana ciki! Haka ya shigo ya sameta suka nufi gida, a hanya ya daka mata zazzafar warning a kan kula maza, ya ce babu ruwanta da su, ko matan ma bai ce ta saki jiki da kowa ba, bai dai hanata ƙawance da mutane ba, amma nesa nesa, dan matsayinsu ba ɗaya ba!!.

Okey ta amsa mashi da shi, yarinya mai jin magana, (Ba irin Pretty abokiyar faÉ—an Smart ba, wai ke ka ce ba Pretty ba, kai Pretty duniya!!)

Sai ta ce mashi harta matan ma bata buƙatar kowa a kusa da ita, shi kaɗai ya isheta. Ya matuƙar jin daɗin kalamanta a in da ya manna mata sumbata a goshi. Haka suka isa gida. A tare suka fito daga cikin motar suka nufi cikin gida, kai tsaye bedroom ɗinsa suka nufa tana faɗa mashi ya zo ya yi mata home work, da okey ya amsa mata suka wuce ciki.

Abinci yasa aka kawo masu kamar kullum, a tare suka yin lunch bayan ya jirata ta yi wanka, ta tsantsara kyau cikin wandon jeans baki mai kwalliyar pink a jikinsa, and pink long sleeve shirt, ta yi matuƙar kyau, ta sanya headband baki a kanta, wannan sarka da Big bro ya bata yana nan a wuyanta sai kyalli yake yi, a school ɗinsu babu wanda bai yi magana a kan sarkar nan ba, uncles ɗinsu ma sai da suka yi magana, saboda haɗuwarsa, dik wanda yasan abu mai tsada dole ya jinjinawa wannan sarka, dan dubabbannin miliyoyi ake magana a wajen. Wato Big bro wuyarta tana burgesa, shi ne ya kara kawata mata shi yadda zai ji daɗin kallo, wlh Black Tiger ɗan duniya ne!!.

Kafin ta gama wanka ya shirya masu komai, tana fitowa ta yi sallah suka yi lunch, sai suka yi karatu na awa biyu a in da ya koya mata Home work ɗin nata da aka bata, ta ji matuƙar daɗi sosai da sosai, sai murna take yi. Hira suka zauna yi har la'asar ta kawo kai, sannan ne suka miƙe, a lokacin Black Tiger baya nan, yana fada, hakan yasa suka wuce bedroom ɗinsa suka yi sallarsu a can, sannan suka zauna ta ɗan koyawa Ronnie karatun addini dai'dai gwargwado, bayan sun kammala around 4:30, sai ya ce su je trainin, su ɗan motsa jiki kaɗan kafin su shirya zuwa church kamar yadda ya yi mata alkawari.

Cike da murna ta ce. "Muje amma zuwa church ka bari sai zuwa gobe". Cike da mamaki ya ce. "Why?". Kashe mashi ido É—aya ta yi kafin ta ce. "Akwai dalili, akwai abin da nike san kammalawa ne". "Sisterrrrrrrr". Ya faÉ—a yana É—an jan sunan alamar kamar warning yake yi mata. "Don't worry ba zan yi abin da zai kawo mana problem ba". "Are you sure?". Sure ta bashi amsa tana wucewa gaba!. "To please kada ki yi magana sosai, and komai zaki gani ki yi shiru kin ji?". Jinjina kai ta yi alamar ta yarda.
Chapter 216 · 0% Book details