← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 242

Sashe 87

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina mata kai Zee ta yi alamar yeah uncle Jahiz kyakkyawa ne. Wani irin kallan up and down Aneesa ta watsa mata kafin ta ce. "Haka ne kam, gaskiya kyakkyawa ne, amma kuma kada ki bari zuciyarki ta yaudareki a kan hakan, dan shi É—in ba zai iya dai'daita kansa da kowa ba, amma menene a tsakaninku da shi da ya ce kina da mahimmanci a rayuwarsa? Dan dai nasan a familynmu gabaÉ—aya babu irinku koda na nesa ne!". Cike da shegantaka da rai'nin wayo ta yi maganar, tana wani binta da matsiyacin kallo.

Zee ta fuskanci kalaman cin mutuncin a juye Aneesa take aiko mata da shi, dan haka sai ta yi shiru bata sake amsa mata ba, amma tabbas ta ji babu daɗin hakan, a tinaninta Aneesa zata karɓeta hannun biyu tun da basu wuce mate a shekaru ba, sai taga akasin hakan.

Jin bata amsa mata bane yasa ta wuce gaba tana faÉ—in. "Ki karisa ciki akwai toilet, ki yi wanka, sai ki duba dressing room É—ina akwai wani part da na ware zaki ga a jikin glass É—in na rubuta n-n, ki buÉ—e glass É—in ki É—auki kayan da suka maki a ciki, ni ina da abin yi". Ta kai karshen maganar tare da ficewa.

Bayanta Zee ta bi da kallo har ta fita daga cikin É—akin, sannan ta dawo da kallonta a kan alatun dake makare a cikin É—akin, one after the other ta fara bin komai na cikin É—akin da kallo, ita kanta a yanzu ta yarda lallai su Aneesa ba sa'anta bane, sun wuce da class É—inta, irin wannan Daula haka? Ga yaran gidan dikka kyawawa gaske, Æ´an gayu, kamar su suka yi kansu, ga iya wanka da tsabta, sai balai'n shan kamshi da jiji da kai suka iya.

Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata kimai ba sai ta wuce ta nufi in da take zatan shi ne toilet na room ɗin, tana tafiya tana zuba ƙauyanci.

Ita kuwa Aneesa tana fita kai tsaye ɗakin kuyangun da suke yi mata hidima ta nufa, ko sallama babu ta shige ciki. Ƴan mata guda biyu ne suke zaune saman katan bed ɗinsu suna hira.

A takaice ta ce. "Ina da bakuwa a ɗaki, idan ta gama wanka ku wanke mun toilet da P.Z, sannan ku bisa da toilet perfumes kamar kala goma haka, dan bana san in ji wani iska ya canza daga na kamshi da na saba shaƙa, ku kara gyra mun ɗaki, kada ku bari na dawo na ji wani abin in ba kamshi ba". Tana kai karshen maganar bata jira amsarsu ba ta yi wajen.

Sun risinar da kai suna ƙoƙarin ɗaga mata gaisuwa, amma ina har ta wuce ta fita abinta. Da kallo suka bita suna kara jinjina halin ƴaƴan King, yaran nan babu mai iya masu sai iyayensu.

Tana fita bata zame ko'ina ba sai room É—in Fanan. Tana shiga ta isko Fanan na zuba barci, ta wani baje a gadanta tana barci cikin nitsuwa, kai ba É—an'kwali arab hairn nan nata a watse har face É—inta. Hayewa saman bed É—in ta yi tana É—an turo baki.

Ƙaramin pillow ta ɗauko, duka ta kaiwa Fanan a tsakiyar baya tana faɗin. "Aunty Fanan tashi ki ji wani labari".

Miƙa ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, murya cike da barci ta amsa da. "Kai Neesha me kuma na yi maki fisabilillah? Ki barni in cigaba da barci na mana, jiya momma ta kawo mun wasu darty girls sun hanani barci, sai hauka suke mun"................... Gyarawa Aneesa ta yi, ta manna bayanta da jikin headboard na bed ɗin, sannan ta ce.

"To cigaba da barcin za ayi maki kafa kuwa".

Waro idanunta waje ta yi, cikin magagi ta ce. "Ban gane za'ayi mun kafa ba, me kike nufi?".

Cikin halin ko in kula ta amsa mata da. "Ina da tabbacin waÉ—an nan dirty girls da aka kawo maki daren jiya É—aya daga cikinsu ce kishiyarki, renon kishiya kika yi jiya".

A zabure Fanan ta miƙe zaune, har ji ta yi barcin nata ya watse, tana zaro idanunta ta ce. "Wai me kike nufi? Ban gane kishiya ta ba?"........... Kunna wutar screen ɗin wayarta Aneesa ta yi, cikin halin ko in kula ta cigaba da cewa. "Na zo yi maki mummunar albishir ne, Yah Jaish dai ya yi aure, kuma waɗan nan ƴan kauye da momma ta kawo ɗaya daga cikinsu ce matar tasa..........."

Ai katse maganar ta yi ta ƙasa karisawa saboda wani irin capka da Fanan ta kai mata a wuyar rigarta, a haukace ta kai mata capkar, bata ma san ta yi hakan ba, kun san larabawa da balai'n kishi kamar me, tuni hankalin Fanan ya bar jikinta, har wani juyi taga ɗakin nata ya yi mata kamar fanka saboda tashin hankali, sai ta ji kamar kunnuwanta ne suka sharara mata karya.

"Ke Aunty Fanan, bafa ce maki na yi nice kishiyar taki ba, mai da wukar, ni mai kawo labari ne kawai". Ta kai karshen maganar tana zare hannun Fanan daga wuyar rigarta. Ta gama aikinta sai ta sauko kasa gadan ta nufi waje abinta. Wato wlh Aneesa yar ikka ce, kawai ta kawo labari ta tafi ta bar Fanan da tafasar zuciya.

Lallai ba shakka safiyar yau bata yi wa Fanan daɗi ba, kuma na tabbata ba zata taɓa manta wannan safiya ba, Allah sarki soyayya, ba laifinta bane.

Da gudun gaske ta yaye bargon da ta lulluɓa, ƙasa ta diro, wani irin kuka mai karfi ne ya zo mata, da sauti ta saki kukan tare da watsawa a guje sai waje. Bata zame ko'ina ba sai part na uncle Abbas wajen Mammie ɗinsu. Tana shiga kai tsaye bedroom ɗin Mammienta ta nufa.

Nan ta isko Sarina da Mammiensu zaune a saman bed, Sarina ta tada kai da cinyar Mammie suna shirya muguntarsu.

Ai a haukace ta shigo tana ihu, har ta razana Sarina ta yunkura zata gudu. Saman bed É—in ta haye ita ma, Mammiensu ta rungumo tana faÉ—in. "Na shiga uku Mammie, shi kenan rayuwata ta zo karshe, ki taimakeni kada na mutu Mammie".

Sarina dai baki ta saki galala tana kallon ikon god.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=======🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Rungumeta Mammie ta yi tana faÉ—in. "Ya isa haka, yi shiru ki faÉ—a mana menene yake faruwa?".
Ƙasa yin shiru ta yi, sai ma wani irin shessheka take yi tamkar zata haɗiyi zuciya ta mutu.

A kule Sarina ta ce. "Ke bama san hauka, dalla rufe mana baki ki faÉ—a mun me yake faruwa?". ........... Sanin bakin halin Sarina yasa ta haÉ—e malaman jikin waje guda ta nitsu, cikin muryan kuka ta fara kora masu bayanin yadda Aneesa ta kora mata.

Wata iriyar zabura Mammie ta yi, dan kuwa tasan da cewa Queen Zarina tana san Jaish, kuma tana san shi ne a matsayin saurayi ba wanda ya taɓa aure ba, in kuwa ya yi aure akwai matsala, dan haka dole su yi saurin kawar da Mahnoor tin kafin ya rasa samartakansa, samartakan nasa Zarina take so, shiyasa kuka ga a yanzu Mammie ta daina goyan bayan Fanan a kan soyayyar Jaish.

HMMM BABBAR MAGANA.

A baya ta so Fanan ta mallaki Jaish, amma da Zarina ta nuna kwaɗayinta a kansa sai Mammie ta janye, shiyasa kuka ga ta dai'na bawa Fanan dik wata gudunmawa, ita kuma Fanan lokacin da Mammie take matsa mata ta rinƙa zuwa wajen Jaish dan ta samu soyayyarsa, a lokacin bata wani feeling a kansa sosai, daga baya sonsa na gasken gaske ya shigeta, a lokacin ne kuma Mammie ɗinsu ta zare hannunta a lamarin,........................... Tashin hankali, lallai akwai cakwakiya.

Mahnoor ta ko'ina sai tarin makiya kike da su, Allah dai ya fiddaki, amma akwai matsala, Mahnoor zata yi kishi da Queen Zarina and Fanan, kai my people's shin kuna ganin wannan abu ne mai ɓullewa ga Mahnoor kuwa? Babban abin takaicin ma shi ne mijin da ake ta wannan bura uba a kansa ɗin ma bai san suna yi ba, hasalima dikkansu ba wanda ya ke kalla da mutunci, dik ya tsanesu, akwai bala'i a kingdom of power wlh, ga dai can Zarina ta tura a ɗauko mata shi, wayyo Allah Jaish yaron Mommarsa zaka yi bayani dan gidanku in ka jika a komar Zarina, ina dai Mahnoor ce baka so? Mu je zuwa zaka so Zarina dan dole ai.

Wani irin matsiyacin tsaki Sarina ta ja. A walaƙance ta dallawa Fanan wani tsinannen harara wadda sai da tasa Fanan haɗiyar yawu mai wuyar wucewa.

"Shashasha kawai, ke yanzu a kan namiji kike wannan kuka Fanan? Me aka yi aka yi Yah Jaish? To ko mata dubu zai aura cikin minti nawa zaki ci uban shegu ki kaÉ—asu hanyar yamma? Ke sai kace ba jininmu bane a jikinki! Ni kam anya Mammie Fanan Æ´ar ki ce kuwa?"........... Cewar hajiya Sarina almasifatu rasa kunya.

Bata jira amsar Fanan ba ta É—aura da cewa. "Ko Æ´ar autar sarkin aljanu ya aura karshe kenan ko? To ubanta zaki ci kawai, zan yi supporting naki ba dan komai ba sai dan kina sansa, dole in tayaki mu kwato maki shi". Tana magana tana dallah mata wannan makirin hararar.

Mammie cikin karayar zuciya ta ce. "Fanan da gaske son Jaish kike yi?". Yadda ta yi maganar zaku fahimci wlh zuciyarta ya karaya matuƙa, tana san ƴaƴan nata sosai, bata jin zata iya marawa Zarina baya ta mallaki Jaish in dai har da gaske Fanan tana san shi, kuma ba zata iya rabuwa da shi ba, ba zata cutar da ƴaƴanta ba gaskiya, dan tasan ya zafin so yake.

"Zaki iya hakura da shi?". Cike da tsoron amsar da zai fito daga bakin Æ´ar tata ta sake jefa mata wannan tambaya.
Chapter 87 · 0% Book details