Sashe 46
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bappa da ya gama sanin Mahreen bata karya ne ya jinjina kai, ya ji kuma zuciyarsa ta yarda da Mahreen É—in, dan balai'n Nenne sai ita, Allah mai sakayya a lokacin da bawa bai zata ba, shi ya kasance masifaffe kuma bala'i ga mahaifiyar Mahnoor, shi kuma Nenne ta kasance kwatankwacin hakan a garesa, shiyasa dayawan lokuta baya kula Nenne idan tana yin wannan abin nata, yana kallan hakan a matsayin shi da maman Mahnoor.
A kan Mairo ya tsayar da kallonsa, cikin nitsuwa ya ce. "Taimaka mata ta canza kaya".
Yana gama faɗar hakan ya wuce ɗaki ba tare da ya sake bi ta kan Nenne ba, ba komai ya sa bai kulata a yanzu fa face dan su Mahreen suna wajen, baya san su rinƙa samun saɓani har suna sa in sa a idanun su Mahreen, hakan zai gurɓata tarbiyar da suke da shi sosai, kuma hakan yanasakawa yara su rage ganin girman iyayen nasu, idan baku dai'na ba a hankali hankali dik wani mutunci da girma ƴaƴan zasu dai'na ganinku da shi.
Daga nan sai raini ya shigo tsakani, kana yi wa yaro magana yana kallanka yana cigaba da abin da yake yi, kunga ai hakan ba daɗi, to sai ku kiyaye, faɗar iyaye a gaban yara bama iya rai'nin kawai yake haifarwa ba, zaku saka mashi sha'awar faɗar, idan macece ba zata rinƙa jin shakkar ta gaggayawa mijinta maganganun ba idan ta yi aure, in namiji ne ba zai rinƙa shakkar zagin mata kai har da duka ba idan ya yi aure, akwai abubuwa da dama wanda faɗar iyaye a gaban ƴaƴansu yake haifarwa, kome za'ayi maki ki danne a gaban yara sai kun keɓe nan kam in kin ga dama ɗaga shi ki maka da kasa..........................😒🙄😅
Ajiye bokitin hannunta Mairo ta yi, ta karisa in da Mahnoor take sanyi ya gama lallasata, hannunta ta riko suka koma cikin ɗakin nata, Nenne muguwa ta jiƙa mata mattress ɗinta sosai.
Bayansu Mahreen ta bi, Nenne na kiranta ta bawa banza ajiyarta ta shige É—akin Mahnoor.
Bokitin ta ajiye kamar zata bi bayansu, sai kuma ta fasa ta wuce cikin ɗakinta rai a matuƙar ɓace, da ta so ne bappa ya ci mutuncin Mairo, ya yi mata tas, amma bata samu hakan ba.
After some minutes.
Mairo ta fito daga ɗakin Mahnoor ta wuce cikin kitchen dan yin abin da ya fito da ita dama, ƙoƙarin fara hura wuta ta yi, sannan ta ɗauko bokitin ta cika shi da ruwa ta kawo kusa da murhu, tana ƙoƙarin ɗaura sabon tukunyarta a wuta sai ga Mahnoor ta shigo cikin kitchen ɗin.
Ta canza kaya izuwa dogon rigar da bappa ya saya mata a lokacin bikinta. Tana sanye da hujabinta kamar kullum.
Cikin girmamawa ta ce. "Daddi ina kwana".
Fuska É—auke da fara'a Mairo ta amsa mata da lafiya ta tashi lafiya. Ita ma da lafiya ta amsa kafin ta É—aura da cewa.
"Bari in tayaki Daddi".
"A'a Mahnoor, jeki ki kwanta kawai, ba sai kin tayani ba, ai ba wani aiki mai wahala bane, tuwo zan yi sai sanya maku ruwan wanka".
"Ayya Daddi ki bari in tayaki kin ji?". Yadda ta yi magana murya a marairace, Allah sarki barci fa take ji, amma kuma ba zata iya kwanciya ta yi ɗin ba, dan yanzu tana jin tsoron Nennen ta sake zuwa ta jiƙata da ruwa.
Da kyar Mairo ta yarda ta tayata É—in, dan haka sai ta ce to ta yi shara ita kuma bari ta É—aura ruwa sai ta haÉ—a kayan wanke wanke kafin nan Mahnoor ta gama shara sai su yi wanke wanke a tare.
A bisa ka'ida yau Nenne ce zata yi abinci ba amarya ba, amma da yake bappa yasan bata kwana a gidan ba sai ya ce da Mairo ta É—aura mashi girkin kawai, kunji dalilin fitowarta da sassafe kenan.
Tsintsiya Mahnoor ta je ta ɗauko, cikin nitsuwa ta fara shara hankalinta gabaɗaya yana a kan tinanin mijinta, Allah sarki yau ta kai kololuwa a kewarsa, ji take kamar ta yi ta kuka babu dakatawa, yau da yana nan yanzu warhaka tana kwnace a jikinsa bata fito ba, a gaskiya ta yarda ta yi babban rashi a rayuwarta wanda ba zata taɓa manta shi ba har abada.
Dai'dai wannan lokacin da take shara tana tinaninsa.......... Shi kuma yana tsaye a jikin window É—in É—akinsa, ya yaye labulen tamkar mai kallan wani abin a harabar kingdom É—in, a zahiri babu abin da yake kallo, tinani kawai yake yi, tinanin ma wanda bai san namenene ba, kawai a ransa ne yana jin tamkar akwai wani gurbi a ransa da yakamata ya cike wannan gurbin, ya rasa ganewa zuciyarsa, tana yi mashi babu daÉ—i, kamar akwai abin da ya rasa haka.
Hannunsa rike da cup mai É—auke da cappuccino, yana sha a hankali hankali yana tunane tunane, yanzu ba jimawa suka dawo saga masallaci sallar asuba, sanye yake da kayan barci masu bala'in kyau a jikinsa, sun haÉ—u da Jawad, amma a hospital ya je ya ga Jawad É—in.
Allah sarki tamkar su cinye junansu saboda so, sai dai Jawad bai faÉ—a mashi cewa ya yi aure ba, ya dai ce mashi Jannat ce bata da lafiya yake jinyarta.
And bai san guyson yana hospital É—in ba, Jawad kawai ya je dubawa, yana duba shi kuma ya dawo, dan dik baya jin daÉ—in jikinsa, baya san fita daga cikin É—akinsa, dama shi ba mai san fita bane sai idan ya zame mashi dole.
Yana cikin kuncin da ya rasa me dalili, while ita kuma tana cikin kuncin da ta san dalili. A haka ta gama sharan nan tas, suka yi wanke wanke a tare da Mairo, Mairo na wankewa ita kuma tana É—aurayewa ta sanya cikin baf, tas suka gama gwanin birgewa sannan Mairo ta kwashe tuwo a kwanikan.
Mahreen kuwa tuni ta kwnata a mattress na Mahnoor ta mayar da barci abinta.
Bayan Mairo ta sauke ruwan wanka, ta sirkawa bappa ta kai mashi banÉ—aki, sai ta fito ta shiga É—aki domin ta faÉ—a mashi, ita kuma Mahnoor ta fara kwasan kayan abincin ta fara kaiwa kowa É—akinsa.
Tamkar wadda aka koro haka Nenne ta fito daga cikin ɗakinta, tamkar wata ɓarauniya haka ta fara sanɗo, a haka ta nufi cikin toilet ɗin.
Jim kaɗan ta fito sai muzurai take yi tamkar an kama ɓera a tarko, dik alamar rashin gaskiya ne a tattare da ita, da alama wani mugun abin ta kullah.
Da gudu ta shige cikin ɗakinta, kamar ba ita ta fito yanzu ba, har da kwanciya ta lulluɓa da zaninta.
Bappa kuwa ya fito ya shiga banÉ—aki dan yin wanka. Ita kuma Mairo ta hau sharan É—akin, da alama Mairo tana da tsabta sosai.
Mahnoor kuwa bayan ta gama, a kusa da Mahreen ta zo ta zauna tare da buga uban tagumi, a hankali ta fara jin faÉ—uwar gaba kaÉ—an kaÉ—an kamar wani abin yana shirin faruwa da ita, jingina bayanta da jikin bango ta yi, a hankali ta fara maimaita Hasbunallahu wani'imal wakil domin Allah ya saukaka mata koma menene yake shirin faruwa da ita!.
A wani irin haukace bappa ya fito daga cikin toilet É—in nan, ihun da yake kurmawa da karfi sai ya razana dik wanda kunnuwansa zasu saurara. Cike da tashin hankali da firgici ya faÉ—o tsakar gidan yana ihu.
Mahnoor tamkar bata ji su ba, sam bata fito ba, dan tasan shi da matansa ne, sai ma kifa kanta ta yi a saman gwiwowinta ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Da gudu Mairo ta fito daga cikin É—akin dan taga menene yake faruwa, Nenne kuwa sam taki fitowa tana ciki kamar bata ji shi ba, sai dai tana can tana zuba uban dariya kamar wata zararriya.Ta toshe baki da pillow dan kada sautinta ya fita tana ta tikar dariya.
Mario tana fitowa ta iskosa kwance rashe rashe a kasa yana ta birgima yana ihu kamar wani zararre, daga shi sai kajeran wando a jikinsa, ita ma bai gama sanyata da kyau ba, ga kuma ruwa a jikinsa, da alama ya fara wanka ne ya fito, dik kasa ta buÉ—e shi saboda ruwan dake jikinsa.
Ganin haka yasa Mairo ta fita waje da gudu neman taimako dan taga kamar wani mai ciwon aljanu ko farfaÉ—iya haka, so ba zata iya ba sai ta yi waje dan neman taimako.
Kai tsaye gidansu ArÉ—o Mairo ta nufa, ko mayafi bata É—auka ba, hankalinta ne a tashe.
Takuwa yi sa'a Ibrahim kawun Mahnoor yana nan, dan haka sai suka taho a tare da shi da ArÉ—o.
Dik ƙasa ya farfasa fatan jikin bappa, saboda yadda yake ta dirza jikinsa a kasa yana ihu, kafin Mairo ta dawo wlh har jiki ne yake fitowa daga fatar tasa, bawan Allah.
Ashe ƙarara Nenne ta je ta zuba mashi a cikin ruwan wanka, muguwa saboda tasan Mairo ce ta kai mashi ruwan wankan, kunga yanzu zai ce Mairo ce ta yi mashi mugunta, Allah sarki daga zuwan amarya bappa zai fara ganin laifinta. Wato wlh Nenne da gwaggo anya akwai shaiɗanu irinsu kuwa? Dik abin da Nenne take yi gwaggo take shirya mata shi dallah dallah yadda zata yi komai, shiyasa kuka ga ta dawo gidan bappa da confidence ɗinta.
Sun lura aikin bokaye baya kama bappa, shi ne suka dawo ta munafurci da kisisina, komai Mairo ta yi su ɓata, tin bappa baya ganin laifinta har ya zo ya fara gani ya fara jin haushinta, har ma ya saketa, shi ne burinsu, to yanzu Nenne ta fara fito da makaman yakinta, muje zuwa dan ganin yadda wannan wasa zata kaya.
Ƙoƙarin kama shi Arɗo dattijon arziki da Ibrahim suka yi dan su kai shi ko da ɗaki ne kada ƙasa ta cigaba da fasa fatarsa. Sai dai ina, sun kasa kama shi, saboda wani irin zillo da yake yi, burinsa kawai a sosa mashi jikinsa, wani irin bala'in kaikayi na musamman yake ji, Allah sarki bawan Allah.
Ga shi kararar ta damuna ce ba ta rani ba, irinta ta fi bala'in zafi, kaikayi kamar zai kashe mutum, ga zafi idan ka sosa, wlh Nenne muguwa ce ta karshe, tana É—aki tana ta dariyar mugunta hegiya.