Sashe 167
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune take a saman sofa mai zaman mutum uku a cikin parlonsa, ta yi shiru tare da buga uban tagumi tana tunanin irin rayuwar da ta sha, ta fuskanci challenges dayawa baiwar Allah nan, yanzu kuma ɗan mutumcin da take ji da shi ɗin ma babu, tinaninta ɗaya shi ne waye zai aureta a haka? Shikenan ita ta zo duniya a wahalce kuma zata koma a wahalce babu wani gata?. Kanta a kasa tana kallan yatsun kafafunta da suka ɗan ya fayau, dik ta yi rama sosai saboda bata cin abinci, kullum tana cikin tinani. Size ɗin kayan da take sakawa a da yanzu sun yi mata yawa, sai dai ƙasa da su, saboda rama, sai idanu kawai zaka gani.
Sleeping dress doguwar riga ce a jikinta launin maroon color, ta sanya ɗan ƙaramin hijabi a kanta, rabonta da abinci tin daren jiya da ta sha tea, bakinta sam babu ɗanɗanon komai, bata sha'awar cin komai kamar wata mai ƙaramin ciki.
Ko kaɗan bata ji motsin shigowarsa cikin parlourn ba, dan ta yi nisa a cikin tunanin da take yi, har ya shigo ya wuceta ya nufi kitchen, ta luluƙa duniyar tinani. Haka zalika bata ji dawowarsa ba sai ganinsa ta yi ya zauna a saman sofar da take zaune hannunsa ɗauke da cup and small chop a cikin plate, yana sanye cikin sleeping dress riga da wando launin milk color, ya yi kyau sosai, sai dai shi ma ya rame sosai alamar yana cikin damuwa, dik wanda ya yi complain a kan ramansa sai ya ce aiki ne ta yi mashi yawa. Har Smart ya yi complain a kan ramansa, amma sai ya ce zai rinƙa kulawa yana ragewa kansa pressure dan ya maida jikinsa.
Yana zama ta zabura ta miƙe zata bar wajen. A hanzarce ya ɗaura plate na small chop a saman table dake kusa da su ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun, in a low voice sosai ya ce. "Please Aesh, ya isa haka gudun nawa da kike yi, dan Allah ki ji tausayina, ko iya haka ya kamata ki fahimci ba da gangan na yi maki hakan ba, idan da da gangan ne ba zan kwashi up to one month ina kula dake ina kuma yi maki magiyar da ki yafe mun ba, ki mun magana ba, dan Allah".
Jikinta ne ya hau kerma, dan a duniya tsoronsa take ji matuƙa, murya na rawa ta ce mashi. "Tabbas da gangan ka ci mun mutumci, ka mun tabon da ba zai taɓa gogewa a cikin zuciyata ba, ka zalinceni, dama a lokacin da ka kamani ka sakeni ka ce mun in ka yi bincike ka ga da sa hannuna a abubuwan da suke faruwa zaka mun abin da ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata, ga shi kuma ka mun ɗin kamar yadda ka faɗa, tabbas ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata! Ka cuceni ka zalinceni! Dan Allah ka kashe ni in huta da wannan rayuwa". Ta kai karshen maganar zafafan hawaye suna zubowa a saman kumatunta.
Shiyasa aka ce ka rinƙa tauna magana kafin ka faɗeta, baka san me gobe zata haifar ba, ga shi maganar da ya taɓa faɗa mata na in ya kamata da laifi zai yi mata abin da ba zata manta da shi ba ta riki maganar a ranta wanda kuma shi ba hakan yake nufi ba, jama'a ku tauna magana kafin faɗinta dan gudun abin da gobe zata haifar, shawara ce daga alkalamina!!.
Kalamanta sun kara narkar mashi da zuciya, shi dai burinsa ɗaya shi ne ta yafe mashi, amma taki sauraronsa ma. Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya saki hannunta ba, cike da tausayawa da kulawa ya ce. "Dik abin da zaki faɗa a kai'na na yarda na kuma ɗauka, yanzu dai dan Allah zauna ki sha tea, ni dai ki rinƙa cin abinci koma me zaki ce a kai'na ki faɗa, lafiyarki shi ne fata na kawai". Ya kai karshen maganar yana miƙo mata cup dake hannunsa, tea ne mai zafi sai tiriri yake yi.
Allah sarki, a jikinta tana jin ba da gangan ya yi mata hakan ba, sai dai zuciyarta taki yarda da hakan, wani lokaci har tausayi yake bata yadda yake neman ta yafe mashi, amma ta gaza yarda da shi, ta kuma rasa dalilin kin yarda da shi da zuciyartata ta yi.
"Ba zan iya cin komai ba, saboda ban san yanzu ina rayuwata ta fuskanta ba, dan Allah ka kyaleni ko yunwa zata kasheni in huta tun da kai ba zaka kasheni ba". Kanta a ƙasa ta yi maganar....... Nisawa ya yi kafin ya ce. "Babu abin da zai samu rayuwarki, zaki yi rayuwa kamar kowacce mace mai ƴanci, dan Allah zauna ki sha tea kin ji?". Cikin sigar rarrashin da ya koya dan dolensa ya yi maganar.
"Har abada ba zan taɓa yin rayuwa mai ƴanci ba, a rayuwar yanzu ka kai budurcinka gidan miji ma ya ka kare da walaƙanci da tozarci in baka samu miji na gari mai tsoron Allah ba bare ace ka zubar da mutuncin naka a titi ka shiga gidansa empty, me kake tinanin zai faru? Kana tinanin zan yi rayuwa mai ƴanci ne? Kana tinanin akwai wata daraja da ta rage mun wanda zai kalleni da ita ne?........."...
Katseta ya yi ya hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce. "Baki zubar da mutuncinki a titi ba, tabbas babu wanda zai ganki a matsayin mara daraja kin ji ko? Dan Allah Aesh ki yafe mun, ki yafe mun kin ji? Nasan na cutar dake, amma kin ki yarda ba da gangan na yi ba, kin ki yarda ba halina bane, da kin san yadda na tsani zina da baki yi ƙoƙarin danganta ta dani bama, kin san irin hukuncin da nike yi wa mazinaci wanda ya yi wa mace fyaɗe kuwa?". Cike damuwa a ransa ya kai karshen maganar............ Sai a lokacin ta ɗago da kanta ta kallesa, hawaye suna cigaba da gangaro mata masu ɗumin gaske, da kyar ta iya cewa.
"Babu ma wanda zai aureni da har zai ganni da daraja, ka kwantanta a kanka, shin zaka iya auren macen da wani ya lalata ya yi mata fyaɗe? Ko ka ɗaukeni a matsayin kanwarka na jini, ya zaka ji idan aka ce anyiwa kanwarka fyaɗe?"...... Dum!! Dum!!!! Shiru ya yi bashi da bakin bata amsa, dan yasan ko kusa ko alama ba zai iya ba, ba zai iya auren wanda wani ya lalata ba, haka zalika ba zai iya barin wanda ya yi wa kanwarsa fyaɗe ya cigaba da numfashi a duniya ba, ba zai kyalesa ba har sai ya yi mashi mummunar kisa, batun aure kuma, shi yaushe ma ya taɓa yin tinanin auren bare har ya yi tinanin irin macen da ta dace da shi, iya abin da ya sani dai shi ne ko soyayya da wani mace ta taɓa yi ba zai kulata ba bare har a kai ga aure.
Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ka gani ko? Kai kanka ba zaka iya auran ragowar wani ba, to taya kake tinanin ni zan samu wanda zai iya karɓar ragowarka?". Cikin zafin zuciya ta yi maganar, tana kai karshen ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata ta juya da nufin ta bar wajen da sauri....... Cikin zafa ya riko hannunta, kin juyowa su kalli juna ta yi, sai wani irin huci take fitarwa mai ɗimin gaske, kai ka zaci zata iya haɗiye zuciyarta a lokacin ko kuma ta kone saboda zafin da zuciyarta ya ɗauka, yana yi mata wani irin suya mai azaba, abin da ciwo matiƙa gaskiya.
"Idan na aureki shikenan zaki yafe mun?" Ya faÉ—a yana kallanta. Ai a miliyan ta juyo da kallanta a kansa, ido cikin ido suka kalli juna, wani irin faÉ—uwar gaba ta ji ya risketa, ta kasa iya magana, dan bata da abin faÉ—e....... "Ni zan iya É—aukar ragowata ai ko? Budurcin mace shi ne mutuncinta right?". Ya faÉ—a kamar ya jefa mata tambaya wanda yasan ba amsa mashi zata yi ba. Dan haka sai ya É—aura da cewa.
"Tabbas budrucin mace shi ne martaba da kimarta a idanun mijinta, dan haka ni zan aureki, dama ni na karɓi budurcin naki, dan haka zan kalleki da kima da daraja, kuma zaki yi rayuwa mai ƴanci kamar kowace mace ko ma in ce fin kowace mace tun da kema kin kawo mun budurcinki, kin aminta da hakan?". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar, tabbas saboda tausayinta da kalamanta na ta rasa gata yasa ya yarda zai aureta, domin kuma ta yafe mashi, ba zai so ya yi sanadiyar shigarta kunci na har karshen rayuwarta ba, gara ya aureta ko ba komai dama shi ya buɗeta, tabbas ba zai yi mata gori a kan komai ba.
Kai ta fara girgiza mashi alamar bata yarda ba, tsananta kukan ta yi, har wani shessheƙa take yi, tamkar zata haɗiyi zuciya, cikin kuka mai tsuma zuciya ta ce. "Ba zan iya aurenka ba saboda ƴar uwata, Sharifat ta mun komai a rayuwata, dan haka ba zan taɓa bakanta mata ba, da ta shiga cikin ƙunci gara ni na tabbata a cikin bakinciki, a lokacin da na rasa gata, nike matsayin mara galihu, nike cikin tsakiyar rana a dokar sahara, a lokacin da duniya ta juya mun baya, farinciki ya kaurace daga rayuwata, na cire tsammanin yin farinciki har abada, a lokacin Sharifat ta tsaya tsayin daka wajen ganin sai da ta sakani dariya a rayuwata, ta sakani na ji cewa ni mutum ce, ta sakani na ji cewa ashe ina da sauran farinciki a rayuwarta, ta zame mun uwa, uba ƴar uwa, ɗan uwa, bata kyamaceni ba, ta jani a jiki tamkar ƴar uwarta na jini, ta kyautatawa rayuwata, dalilinta nasan kai'na har nasan darajar mutuncin da yau nike kuka a kansa dan ka keta mun shi, ba dan ita ba da ban san darajar mutuncin nawa ba, Sharifat ta wuci tinanin mai tinani a rai'na, dan Allah kada ka sake yin magana a kan aure tsakanina da kai, dan kai ne burin ƴar uwata!!". Tana kai karshen maganar ta kwace hannunta da sauri ta haye sama tana kara rushewa da kuma mai taɓa zuciya.