← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 242

Sashe 138

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Innalillahi Queen Zarina ta tura a ɗauko mata shi dan samartakansa ga shi yau ya bawa Mahnoor samartakar tasa, innalilahi wa inna ilahir, shi mutum ne mai addini hakan yasa Queen Zarina bata iya ganin halin da yake a cikin ta madubin tsafinta, tab akwai cakwakiyoyi matuƙa.

Mama Haulat baiwar Allah, ita ta gasawa Mahnoor jiki da ruwa mai zafi da ta haÉ—a mata, sai dai kuma har ta yi mata dik abin da zata yi mata ta gama Mahnoor bata farfaÉ—o daga wannan doguwar suma da ta yi ba, kuma jinin yaki tsayawa dan ta samu rauni daga ta ciki, hankalin mama Haulat in ya kai dubu to ya tashi a wannan lokaci.

Jikinta na kerma ta tallabi Mahnoor zuwa cikin bedroom É—in, ta fahimci ciwo ta ji sosai daga ta ciki, dan haka sai ta cire bedsheet É—in da jinin ya lalata, ta kudundunesa, ta kwantar da Mahnoor a saman sofa ta É—auki bedsheet É—in ta nufi wajen momma da shi.

A lokacin momma ta dawo daga wajen King kenan, tana ƙoƙarin kwantawa mama Haulat ta shigo bakinta a ɗauke da sallama. Da kallon mamaki momma ta bita kafin ta amsa sallamar tare da kafeta da idanu alamar tana jiran jin abin da ya kawota.

A gaban momma ta zube gwiwowinta ƙasa, cikin girmamawa ta fara neman izinin magana. Kai momma ta ɗaga mata alamar ta yi magana tana jinta. A natse ta ce. "Ranki ya daɗe princess Mahnoor dai ta kawo budurcinta ga mijinta ga kuma shaida nan ina tafe da shi, sai dai an samu matsala sosai ta zubar jini da alamar ta samu rauni daga ta ciki". Ta kai karshen maganar tare da ware bedsheet ɗin ta nunawa momma shaidar da ta kawo na jinin Mahnoor dake jikin shi.

A lokacin da mama Haulat ta ce Mahnoor ta kaiwa Jaish budurcinta ba ƙaramin daɗi momma ta ji ba, a bayyane ta sauke ajiyar zuciya mai sanyin gaske, har ta ji dik wata damuwa tata ta gudu, amma a lokacin da ta ji zancen karshe na cewa Mahnoor ta samu rauni take farincikin nata ya tsaya cak, dama dai tasan Mahnoor zata sha wahala, dan dik ƴaƴanta babu rago, sai dai bata kawowa ranta wahalar har haka bane, hankalinta ya tashi sosai, da sauri ta fasa kwanciyar da take da niya.

Kasan gadan ta sauko, bata bi ya kan mama Haulat ba ta yi gaggawar nufar waje, kai tsaye ta nufi ɓangaren Jaish ɗin, hankalinta dik a tashe matiƙa. Da sauri mama Haulat ta miƙe ta rufa mata baya dan su je su san abin yi. Ko da momma taga Mahnoor ta tausaya mata matuƙa, dan ta ganta a wani irin yanayin da dik zuciya mai imani sai ta tausaya mata, sai dai kuma momma bata tambayi ina Jaish ba, dan ita kanta ta san ba zai tsaya ba, saboda shegen kunyar nan tasa ta rashin kunya in ji Jawad, so sai bata ma nemesa ba, da kanta kawai ta tsayawa Mahnoor ɗin ta yi mata komai ta hanyar kirar likitarta mace dan ya zo ta dubata.

Shi kuwa Jawad da yake iya suma Chuchu ta yi bata samu rauni ba, da kansa ya yi treating kayassa, sai dai fa akwai cakwakiya matuƙa, domin kuwa tun da ta farfaɗo banda kuka babu abin da take yi mashi, ya yi rarrashin duniya taki ta kula shi, ta dai ce wajen mummynta zata koma wlh ba zata zauna da shi ba tun da shi mugu ne. Dik abin da take faɗe he's not minding her word, hakuri kawai yake cigaba da bata yana rarrashinta dan yasan ya yi ɓarna.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥🔥

A ɓangaren Smart kuwa, Sarina tana ganin ya shiga dressing room ta lallaɓa ta miƙe da nufin ta gudu, kasa iya taka kafafunta ta yi, dan haka sai ta koma ta zube ƙasa, da ciki ciki ta fara ja wasu zafafan hawaye suna tsere a saman ƙuncinta, wani irin azaba ta ji lokacin da ta gwada mikewan nan, da kyar ta cigaba da jan cikin nata har ta fice daga ɗakin. Ganin komawa part ɗinsu ba zai yiwun mata ba saboda nisa ne yasa ta nufi part ɗin King dan a ganinta shi ne kawai zai iya cetanta daga hannun Smart. Amma kuma sai da ta ɗauko alkyabbarta ta sanya a jikinya kafin ta fice tana ja da ciki. Tasan in ta je wajen King da irin wannan shiga zata yabawa aya zaƙinta ne, sai ta mayar da alkyabbarta.

A lokacin da ya fito bai sameta a cikin room É—in ba, wani irin É—aure fuska ya kara yi, a ransa ya ce lallaima wannan yarinyar ta jawa kanta bala'in da babu wanda zai iya tare mata, har kamar shi ta isa ya sakata kneel down ta tashi ta gudu? Tab ta É—ebowa kanta wutar gasa kanta da kanta. Auta dai tana zaune a saman bed, ta dai'na kuka amma bata iya mayar da barcinta ba, ya kuma ganta, sai dai ya mayar da hankalinsa a kan kamo Sarina, ya ce sai ya dawo zai rarrashi Auta.

Cikin takun jarumta ya bi bayanta, sai dai bai san ko'ina a cikin fam part É—in ba, dan haka da ya fito sai da ya É—an tsaya a bakin kofa yana tinanin ina yakamata ya bi.

Ƙasa ya yi da kansa domin yin tinani sai yaga jininta a kasa saman tiles, da ta ja jikinta a ƙasa jininta ya ɓata ko'ina, bin jinin da kallo ya yi ya ga hanyar da ta bi, ransa a ɗan ɓace ya bi wajen, ta ja ya kuduri niyar yi mata abin da bai shirya ba.

Dik abin da yake faruwa Mammie ɗinta tana ganinsu ta madubin tsafinta, ta so ɗaure hannun Smart a lokacin da yake dukan Sarina ta kafar mashi da hannun, sai dai ta kasa sage mashi koda jijiya guda ɗaya, saboda ni da ku dai dikka mun san yadda yake da riƙo da addini, ko jijiya guda ɗaya ta kasa sagar mashi, infact ko kusa da shi abubuwan tsafin nata sun ƙasa zuwa, wannan dalilin yasa ta baro part ɗinsu ta zo domin ta kwaci yarta.

A main parlour na part É—in King Smart ya isko Sarina, tana jin motsi ta juya, tana ganin shi ne ta daddage ta kurma ihu mai amsakuwar da sai da ya daki kunnuwan dik wanda bai yi barci ba a cikin part É—in except Jawad and Jaish da suke duniyar sama jannati.

Cikin zafa King ya fito daga bedroom É—insa sanye da arabs jallabiya saboda wannan ihun, ita ma Mammie da sauri ta karisowa wajen, da yake uncle Jahiz ma bedroom É—insa yana cikin part na King sai ya fito da gudu, dama Dr Raj yana kan hanyarsa na zuwa wajen King, so jin ihun yasa ya yi saurin karisowa. In short cikin short time gabaÉ—aya family suka haÉ—u a cikin parlon, kowa sai tambayar kansa yake yi me yake faruwa?.

Mammienta na ganin haka ta yi wa uncle Abbas sms a kan ya zo main parlour babu lafiya. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai ga shi ya zo, gabaɗaya kowa ya tsaya cirko cirko kaman masu shirin kaurewa da yaki, an rasa mai bakin iya tambayar Smart me yake faruwa?.

Da yake momma ce ta yi karshen zuwa wajen sai yazama sun É—auki almost 5 mins babu wanda ya iya kallan Smart ya tambayesa dalili, sai King ne ma ya yi kokarin buÉ—an baki zai tambayesa sai ga momma ta kariso wajen da sauri tana faÉ—in meyake faruwa ne?.

King É—in ma bai fasa tambayar da ya yi niyya ba, dan haka tana rufe baki ya ce. "Omerish meya haÉ—aka da kanwar taka kuma?". Shi King dama mamakin shigar jikin Sarina yasa ya É—an yi shiru ma, dan ba kaya bane na hankali da musulunci, kaya ne na Allah wadarai, so abin ya bashi mamaki ganin irin wannan shiga a jikin Æ´aÆ´ansu. Ja da take yi da ciki yasa alkyabbar da ta sanya ya yi sama kayan suka bayyana.

A wannan karan har da su Zee and su Pretty, Auta dik sai da suka haÉ—u a parlourn, su Jaish da matansu ne kawai basa nan.

Mu koma baya kaɗan kafin mu ɗaura daga labarinmu, a lokacin da Zee ta baro garden ta baro Dr Raj kenan, tana kan hanyarta na nufar bedroom ɗin momma suka ci karo da mama da ta fito daga part na Akka. To kun dai san yadda halin mama yake da kyara haɗe da tsangwama, ga shegen walaƙanta mutane da ƙasƙanci. Hakan yasa tana ganin Zee ta bita da kallan walaƙanci kafin ta yi mata zagi ta uwa ta uba wanda ko kare ba zai ci ba dik da bata san wacece ita ba, daga karshe ma ta kirata da bola kazama, a tinanin mama ƴar aiki ce Zee momma ta kawo, dan haka sai ta rufe zancenta da cewa. "Kada ki kuskura na ganki ta arear side ɗina da sunan kin zo mun aiki, dan bana da buƙatar irinku a masu yi mun aiki".

Wato idan jininka bai haɗu da mutum ba fa bai haɗu bane kawai, ga shi dai babu gaira babu dalili mama ta tsani Zee, har ta yi mata wannan ƙasƙantaccen zagi mai muni haka. To ita ma dai Zee kun san ba shiru take yi ba, dan haka a karshe ta ce. "Ai ko zan yi wa kowa aiki a cikin gidan nan ke kam ba yi maki zan yi ba, banza ma irinki shashasha mara mutumci".

Amma da Hausa Zee ta yi maganar, hakan yasa mama bata fahimci abin da ta faɗa ba, ta daiga tana magana kawai. Hmmm Zee fa bata san mamar Dr bace wannan, haka kawai ta tsani mama ta kuma zageta fes har da ce mata shegiya mai idanun mujiya dik da Hausa, ta kara da cewa dik ranar da hannunki ya taɓa jikina zaki gane baki da wayo, dan sai na lillisaki wlh. Ta dai tsaya tana surutanta ita kuma mama ta kara gaba. Sai da ta gama babu mai bata amsa sannan tasa kai ta wuce part ɗin momma tana kunkuni ciki ciki.
Chapter 138 · 0% Book details