← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 242

Sashe 125

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadijah and Zee ne zaune a saman sofa a part É—in mama bedroom na Aneesa. Su biyu ne kawai a cikin É—akin, sai hira suke yi Zee tana jin daÉ—i Khadijah ta samu lafiya.

Khadijah dai ciwo bai rage mata komai ba, sai kiba ma da ta kara, kumatunta ɓulɓul gwanin sha'awa, momma ta ce ta fara bawa babynta nono tin da ta samu lafiya, dan nonon uwa ba ƙaramin abu bane, idan yaro ya rasa shi ma sai kuga ya girma ga shi ga shi nan ne kawai.

So tana rike da babyn a hannunta, dikkansu kayan Aneesa suka sanya, sun yi kyau matiƙa, sai dai dik in ka kalli face ɗin Khadija zaka kalli tana cikin bakinciki, dan damuwa na cunkushe a ranta, wai a hakan ma dan likitoci sun ce ta cire damuwar dake ranta in ba haka ba zata iya kamuwa da ciwon zuciya, shi ne fa ta ɗan rage.

••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Aunty Khadijah tin da kin samu lafiya yakamata mu koma Nigeria ko?". Cewar Zee. Yadda ta yi maganar tasa Khadijah ta zargi wani abin. Cike da mamaki Khadijah ta ce. "Kina da matsala da nan É—in ne?".

Kai ta jinjina da sauri tana amsawa da e tana da matsala. Nisawa Khadijah ta É—an yi kafin ta amsa da.
"Meyasa Zee dik in da muka je sai kin yi wa wajen mummunar zato ne? A nan É—in ma nasan cewa zaki yi kina zargin wani abin ko?".

Kai Zee ta gyaɗa. "To Aunty Khadijah ki faɗa mun wani waje ne da na yi wa mummunar zato bai zama sharri a garemu ba? Kina dai gani mai napep da ya ɗaukemu daga kawo Kaduna da nace ban yarda da shi ba, kin dai ga sace mu ya yi izuwa Abuja, Allah ya kuɓutar damu, muka sake faɗawa gidan matar can, ita ma na ce maki ban yarda da ita ba, haka kika matsa mu zauna da yanzu babu junior ta sacesa, nan ma Allah ya karemu da kariyarsa, muka tsallaka rijiya da baya, kinga kuwa ai ba kya tuhumeni a kan dan nace nan ma ban yarda da su ba, basu kwanta mun a rai ba".

Tun da ta fara magana Khadijah take binta da kallo tana sauraronta har ta kai aya, sannan ta ce mata. "To ke yanzu meyasa kike zargin wannan gida?".

Ajiyar zuciya Zee ta sauke, juya harshe ta yi izuwa turanci, sannan ta ce. "Saboda wannan É—an kwallon, ina zargin yana shigo mana É—aki da daddare, sannan kuma yana yawan sakawa dik wani motsina idanu..........."

A hanzarce Khadijah ta katseta da cewa. "Wani É—an kwallon kenan?". "Jahiz mana". Ta bata amsa tana kara É—aure fuska.

Zaro idanu sosai Khadijah ta yi zata yi magana daga bakin kofa suka jiyo muryar Aneesa cikin harshen turanci ita ma tana faÉ—in.
"My second dad ba yadda kika ɗaukesa yake ba, ke ba abin alfahari bane ma a wajenki ki ce kin taɓa ganin shi a zahiri? Na tabbata dik wanda zaki ce wa kin taɓa ganin uncle na a zahiri ma ba yarda zai yi ba, domin baki yi kalar wadda ta taƙa matsayin da zata samu damar ganinsa a zahiri ba".

ÆŠan siririn tsaki Zee ta ja, a kule ta ce. "Then so what? Kuma da kike wannan magana ce maki aka yi wata tsiya ce shi? Ko an faÉ—a maki Nigeria irin nan ne da zamu yi alfahari da ganinsa?".
Zee ta samu Khadijah ta samu lafiya yanzu kuma su Aneesa sai sun sarara mata, dama saboda lafiyar Khadijah ta koma baya ta yi zaune, yanzu kuwa kowa zai sha mamakinta, ba É—aga kafa.

Wani irin matsiyacin kallo Aneesa ta wurga mata kafin ta ce. "Ni ba mate naki bane okey? Ki rike words É—inki da kyau kada ki bari su kubce maki a kai'na, dan zaki yi danasani, rubbish useless people kawai". Ta yi maganar tana dalla masu harara.

Da sauri Zee ta buɗe baki zata mayar mata da martani, a hanzarce Khadijah ta tareta da faɗin ta rufe bakinta a wajen. Ranta ne ya ɓaci sosai, ba zata iya yi wa Khadijah musu ba, dan haka sai ta miƙe da sauri ta nufi waje, Khadijah na kiranta amma bata tsaya ba, ta ce ita ta bar wannan ɗaki ma ba zata sake dawowa ba, gara ta kwana a waje da ta sake kwana a ɗakin, kun san mutuniyar da shegen zuciya.

Tana fitowa ta nufi elvator, ƙasa mai gabaɗaya ta yi domin ta fita waje. Ita da bata san ko'ina ba amma saboda zuciya sai gata a tsakar kingdom ɗin, ta ko'ina warriors ne suke shawagi dan tabbatar da tsaro. Shiru ta ɗan tsaya tana kallan yadda hasken bulb suka haska harabar kingdom ɗin tamkar rana, ko allura ka jefar zaka iya tsinta.

Wani ɓangare na zuciyarta ne ya zugata wajen ce mata ta ɗan yawata cikin kingdom ɗin mana ko zata huce kafin ta koma ciki ta je su kwana a tare da Pretty, dan ba zata sake komawa part ɗin mama ba, kun san zuciya da sake sake, sai ya rinƙa saƙa mata tabbas Aneesa ta ci mutumcinta.

A hankali ta fara taka kafarta tana tunane tunane ta fara kewaye cikin harabar family part. Wasu warriors guda biyu ne suka nufota cikin takun jarumta. Ta É—an ji tsoro da ta gansu, amma haka ta daure ta cigaba da tafiya suna tinkarar juna.

A gabanta suka tsaya, cikin girmamawa suka ce ko tana buƙatar wani abin ne ta fito? Kai ta girgiza masu kafin ta amsa masu da bata buƙatar komai, shan iska kawai ta fito yi. Ɗaya daga cikin warriors ɗin ne ya nuna mata hanyar babban garden na family part, sannan ya ce mata ga wajen shan iska a can ai idan tana da buƙata.

Ta ji daɗi sosai, sannan ta nufi wajen tana yi masu godiya. Juyawa warriors ɗin suka yi suka koma bakin aikinsu........ Sosai Zee ta baza idanu tana kallan ƙawatuwar garden ɗin nan, ga wasu irin flowers masu kamshin daɗi, a hankali iska ke kaɗawa yana ratsa jiki, sai ta ji wlh zata iya kwana a nan wajen, haɗuwar wajen ya tafi da imaninta.

A hankali ta nufi karisawa wajen da luntsuma luntsuman sofas dake wajen wani ƙayataccen rumfa dan ta zauna a can, tana tafiya tana waige waige dan ta kurewa ko'ina kallo a cikin garden ɗin. Unexpect suka ci karo da mutum, a razane ta juyo da kallanta a kansa domin ta ga wanenen?.

Tana juyowa dai'dai lokacin ya ɗaga hannu zai dallah mata mari sakamakon cappuccino dake hannunsa ta buge mashi ya zube a white sleeping dress dake jikinsa,.hakan ya kona mashi rai sosai, ga wayarsa da ta buge ya faɗi ƙasa, ya ji zafin hakan natuƙa.

A fusace ya cire hannu zai dallah mata mari, da sauri tasa hannunta dikka biyu a face É—inta domin ta kare lafiyar fatarta daga marinsa. Ta datse idanunta gam tana jiran ta ji saukar mari sai kuma ta ji shiru bai mareta ba. A hankali ta É—an waro idanunta domin taga meya hana shi sauke mata wannan mari.

Tsaye yake ya mace da kallan face ɗinta, dalilin da ya dakatar da hannunsa ga isa fatar kumatunta kenan, da alama a kallan farko ya fola, idanunsa a kan dogon wuyarta mai kyau da ƙawa. Ganin ta waro kallanta a kansa ya sa ya dawo da kallonsa a saman face ɗinta.

Kara waro idanunsa waje ya yi yana kallan haɗuwarta, lokaci guda ya wani ja numfashi tare da mai da kallansa a saman kirjinta. Ita kuwa ganin face ɗinsa ba ƙaramin girgizata ya yi ba, ta ga kyau na jinin Akka tamu ta amana, sai taga kamar ya fi kowa kyau a gidan. Yo dama yana kanin Ramish ba dole ya yi kyau ba.
Slowly ta kai kallanta kasa saman kyawawan fararen kafafunsa dake cikin wasu kyawawan takalma na yawo a tsakar gida, a hankali ta fara binsa da kallo har izuwa sama dai'dai wuyarsa, sai ta ji nauyin karisa kai kallanta saman face É—insa dan kada su haÉ—a idanu.

Kasa Dr Raj ya yi da hannunsa ya fasa marin nata, sannan ya ɗan kawar da kallonsa a kanta yana maidawa kan wayarsa dake ƙasa, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi. Ganin yana kallan ƙasa yasa ta kai kallanta wajen ita ma. Wayarsa yake kallah, ɗan satar kallansa ta ɗan yi kafin ta duka zata ɗauka mashi wayar.

Dai'dai lokacin shi ma ya duƙa zai ɗauki kayansa ya wuce, ba tare da sun ankaraba suka kai hannunsu kan wayar a tare, ta rigasa ɗauka, amma da hannunsu ya goge juna wani shock da ta ji ne yasa ta saki wayar, shi ma sai ya ja hannunsa baya kaɗan. A hankali ya ɗago da kallansa a kan face ɗinta, while ita ma dai'dai lokacin ta ɗago da nata kallan a kan face ɗinsa, wato wannan fa shi ake cewa soyayya a kallan farko, the most luckys persons.

So idan ta tashi shiga mutum fa wlh bata excuse, wani lokaci ma zaka haÉ—u da yarinya da rana, sai da daddare idan ka koma ka kwanta santa ya shigeka im ka tinata, so, so, so, a karshe dai ao ita ce silar kowa a duniyar nan, bari dai mu cigaba.

Sarkafe juna da kallo suka yi, Dr Raj ya ga jinin Nigerians ya rasa natsuwa da control of his heart. Ita ma Zee taga ɗan balarabe jinin modarawa jinin Akka tamu ta amana ta rasa natsa natsuwar. Sun ɗauki a kallah 2 mins a haka suka kallan juna ido cikin ido kafin ta yi ta mazan zare idanunta daga kansa, sannan ta miƙa hannu ta ɗauka mashi wayarsa.

Wai ni kam ba Zee bace ta ce babu ita babu maza? Har da wani cewa ta tsani maza! Ko dai ba ita bace nikam?! Kaina ya ɗaure, ina ƴan special grp kuzo ku warware mun kullin dake kai'na,...........🥱
Chapter 125 · 0% Book details