← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 242

Sashe 70

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi dai shiru bai ce mata ko uppan ba, dan har yanzu bai fahimci a kan me take yin magana ba, ya É—auka ya cuci zuciyarta ne da ya ce yana santa.

Tsabar farinciki ta rasa a ina zata sanya ranta ta ji sanyi, a cikin tsakiyar kirjinsa ta cusa kanta, dunkule hannunta ta yi tana dukan kirjinsa da ɗan karfi ta fara faɗin. "I really love you Hoorain, ban taɓa san wani abin kamar yadda na soka ba, please ka soni ko bai kai wanda nike yi maka ba".

Ina, ai ƙasa iya ɗaukar gangan jikinsa ƙafafunsa suka yi lokacin da ya ji kalmar i love you Hoorain daga bakinta, sai ya ji jikinsa ta yi mashi nauyi, hakan ya ja ya durkushe kasa a kan gwiwowinsa, kusan a tare suka durkushe kasar da ita. Kuka take yi sosai tana goggo kanta a cikin kirjinsa...........(DUKKA WANNAN DAƊI NE FA😅 GIMBIYA ZUNAIRA MANYA ƳAN LOVE, TA IYA BAWA FLOWER ƊINTA RUWA YADDA YAKAMATA🥱)

Jin abin yake yi tamkar mafarki ba gaske ba, soyayya wata aba ce mai matikar kwarjini haÉ—e da karfin gaske wanda a duniyar nan zata iya zama abu na farko mai tsananin karfin da babu biyunsa, komai sai da soyayya ake yi, son Allah da Manzonsa ya ja zamu iya bada rayukanmu a kansu, haka zalika san iyayenmu yasa muke binsu sau da kafa, muke kuma burin ganin farincikinsu ko da zamu rasa namu farincikin mu yi bakinci, su umarcemu ko da bamaso haka zamu aikata dan son da muke yi masu, soyayya ta fi karfin dik tinanin mai tinani.

Hannunsa ya kai da kyar ya iya riko nata hannayenta da take ta bubbuga kirjinsa ta rasa ina zata sanya ranta saboda daÉ—i. Yau ji yake yi kamar zai yi hawaye shi ma, idanunsa sun yi jajir kamar wuta.

"Ranki ya daÉ—e da gaske kina sona? Da gaske kike yi?". Da kyar ya iya faÉ—ar hakan.

Kai ta gyaÉ—a mashi cikin wani irin tsantsar farinciki, ta kasa yin magana. Sake hannayenta ya yi tare da tallabo kanta da take ta gogawa a jikinsa, ya É—agota suna fuskantar juna. Idanunta a rufe ruf sai hawaye dake ketowa kamar hanyar ruwa.

Hannayensa ya kai saman face É—inta. "Ranki ya daÉ—e ina neman alfarma a mun inzini in goge waÉ—an nan hawaye".

Idanu a rufe cikin kuka ta ce. "Ka barsu su zuba my hero, ka kyalesu kawa, na farinciki ne". "To ai ni ganinsu a face É—inki babban tashin hankali ne a gareni, ba zan iya jura ba".

Wani irin sanyi ta ji ya kara ratsa zuciyarta. Hannayenta ta É—aura a saman shoulders É—insa.
"Dik yadda kake so ka yi my hero, ni dai nasan hawayen ba zasu dai'na fita ba, dan yau zuciyata ta karɓi sakon farincikin da bata taɓa karɓar irinsa ba, saƙon da ta jima tana jira, har mafarkinsa nike yi".

Goge mata hawayen ya fara yi cike da tausayi da soyayya. Ina ai kin dakatawa suke yi kamar yadda ta faÉ—a, yana gogewa wasu suna zubowa, ya rasa ya zai yi, ji yake yi kamar an mallaka mashi ita.

Zame hannunsa daga kumatun nata ya yi, da kyar ya miƙe tsaye, cak ya ɗauketa suka nufi wajen koramar nan, dan yaga da gaske hawayenta ba zasu dai'na zuba ba. A saman dutsen kusa da ruwan ya zaunar da ita, a kusa da ita ya zauna tare da sanya kyawawan fararen hannunsa ya taro ruwan dake zuba.

Face É—inta ya fara wanke mata yana cigaba da rarrashinta. Da kyar ya samu ta yi shiru, kasa cikin ruwan dake gangara izuwa wajen da yake taruwa ya tsaya, a gabanta yana kallan face É—inta, har lokacin idanunta a rufe, da alama akwai É—an kunyarsa a tattare da ita.

"Ranki ya daÉ—e zaki iya buÉ—e idanu yanzu na gama wanke maki face É—inki". A sanyayye sosai ya yi maganar.

A cikin ranta ta furta sai kace an ce mashi saboda ya wanke mun face yasa na rufe idanu. Shiru a fili ta yi bata amsa shi ba, kuma bata yi kamar zata buÉ—e idanun nata ba.

Yana tsaye yana kallanta unexpext wani tsuntsu mai bala'in kyau launin blue da ratsin yellow a wuyarsa ya sauƙa mashi a saman shoulder ɗinsa, hannu ya kai cikin dabara ya capko ɗan tsuntsun mai shegen kyau.

Zuba mashi idanu ya yi yana kallonsa. Ya ɗan shagala da kallan tsuntsun ya tsinkayo voice ɗinta a ɗan sarkafe ta ce. "Ruwa nike san sha my hero". Ta yi maganar tare da waro idanunta wajen.... Ni kam na ce ai dole ki nemi ruwa gimbiya ƴar daddynta......🥱

Tana buÉ—e idanu ta yi arba ta kyakkyawar tsuntsuwar dake hannunsa, kara É—an zaro idanunta waje ta yi, cike da yarinta ta saki murmushi ga hawaye basu gama bushewa ba.
A hanzarce ta kai hannu zata taɓa tsuntsuwar. Ɗan ja baya kaɗan da ita ya yi alamar baya san ta taɓa kenan, cike da mamaki ta ɗago da kallanta a kansa.

Tin bata nemi jin ba'asin hanata taɓawa da ya yi ba ya yi saurin cewa. "Amin afuwa, ina tsoron ya cizan mun kene yasa na ja baya".

Sosai ta yi daÉ—i ya ratsa zuciyarta, irin wannan kulawa haka, ai sai yasa mutum ya mance a duniya yake, ya mance kowa da komai.
"My Hero shi fa tsuntsu baya cizo, ya mun kyau ne sosai fa shiyasa zan taɓa". A ɗan shagwaɓe ta yi maganar, ga murya a ɗan dashe.

Kai ya É—an girgiza mata. "Ni dai gaskiya a'a, banyarda ba, kada in saki jiki baya ciwo ya zo kuma ya cijeki".

"Shikenan to, dik yadda kace hakan za'ayi, amma na so riƙesa a kusa da ni in gani, dan yana da kyau". ....... Takowa step biyu ya yi ya kariso dab da ita, a hankali ya ɗan rage tsawonsa, sannan ya matsar mata da ɗan tsuntsun kusa da ita.

"Ki gansa a kusa da ke, amma a hannuna".

Iyayi ne fa kawai irin nata, dan kuwa tana tsoron tsuntsun, da ya matsar mata da shi kusa da ita sai ga shi tsoronta ya bayyana, wai da ita zata nuna ita jinin bamodare ne, wato jinin King, shi ne har da wani nuna bata tsoro a farko.

Yanzu kuma sai ga shi ta koma har da ɗan ja baya, abin dariya ma shi ne ta ɗan kai yartsarta manuniya tana san taɓa jikin gashin tsuntsun, kun san yadda mutun yake dankwalar abu mai zafi ko? To haka take sanya yarsarta a miliyan tana ɗan taɓa gashin ta sake janyewa da gudu.

Shi dai Hoorain hakan ba ƙaramin birgesa ya yi ba, a duniya dik abin da ta yi birgesa take yi, sai ma idan ta haɗa da murmushi, ya ilahi ya lilliahi, sai ya ji tamkar ta yi ta cigaba har abada su kasance a haka. SOYAYYA MUGUN WASA.

Sai kallan face ɗinta yake yi, tana murmushi da guntun hawaye. Cigaba da wasa da tsuntsun ta yi tana taɓa shi kaɗan kaɗan. Zuciyarta ce ya raya mata yana kallan face ɗinta, dan haka sai ta ɗago kai da sauri.

Aikuwa karaf suka haɗa idanu da shi, da sauri ya yi yunƙurin kawar da kallonsa. Yatsunta ta fyasta mashi a saitin face ɗinsa, hakan yasa bai kawar da kallonsa ba, ya cigaba da kallonta ko da akwai wani sakon da zata faɗa mashi.

"Meyasa baka san haÉ—a idanu da ni my Hero?"........... Sake tsuntsuwar dake hannunsa ya yi ta tashi sama, sannan ya ce. "Zo mu je in baki ruwan da kika ce zaki sha".

Make mashi kafaÉ—a ta yi. "Ni dai a'a, sai ka faÉ—a mun abin da yasa baka san mu haÉ—a ido".
Ajiyar zuciya ya sauke, Auta ita ma ashe ta iya rigima da yake ganinta kamar ba haka ba, ashe dai ta iya ita ma.
"A da ne bana san mu haɗa ido saboda ban san ya zaki fassara kallona a gareki ba, kuma ke ma kin san dokace da take a kanmu na haramta mana ɗaura kallonmu a kanku, kin san ba wani mayakin da ya isa yake da ƴancin ya kalleku, kin san hukuncin da yake kansa idan ya yi hakan, ni kuma bana iya ƙasa kallanki a dik time da muka haɗu, shiyasa idan kika ɗago kika kalleni nike kauchar da kallona". Ya kai karshen maganar yana mayar da kallonsa kasa kan kafafunsa dake cikin ruwan gudun.

"To ai a da kace, yanzu kuma meyasa kake kin yarda mu haɗa ido?". A ƙagare da san jin amsa ta jefa mashi tambayar.

"Babu wani dalili yanzu kam, na dai saba kaucewa a da ne yasa har yanzu ma nike yin hakan".

Murmushi ta ɗan sakar mashi kafin ta riko hannunsa da ya harɗe a saman kirjinsa, a hankali ta sauko da ƴan kafafunta cikin ruwan da nufin ta miƙe tsaye.

Warware hannunsa ya yi da sauri ya riko nata, a hankali ya taimaka mata ta sauƙo kasa. Unexpect ta sauke ƴan kafafunta a saman nasa dake cikin ruwan. Sosai ya ji wani irin har cikin ransa, ita kuwa sai ta yi baya kamar zata faɗi. A hanzarce ya sanya hannunsa ɗaya ta baya ya riko waist ɗinta.

A wani irin slow ya dawo da kallansa saman face ɗinta, sai yaga ashe shi take kallo, yanayin yadda suka tsaya abin ya ƙayatar matuƙa, dama ga yanayin wajen fili ne na masoya, abin ba'a magana.

Hannunta ɗaya da ya saki ya riko waist ɗinta da nasa ta kai saman shoulder ɗinsa, da yake ya ɗan rage sawonsa hakan yasa ta iya dafa shoulder ɗin nasa. A kusa da kusa suka kalli zuna, wani azababben kaunar juna ne ya kara ratsa zuƙatansu, sanyi mai ni'ima ya ratsa fatar jikinsu, dikkansu basu ki su dawwama a haka ba.

"Hoorain". Ta ambaci sunansa a kurkusa kurkusa ba tare da ta zare kallanta daga kansa ba. Ya ƙasa iya amsa mata, saboda yadda ta yi magana a kusa tasa ya rasa control ɗinsa. He's in out of his control yanzu.

"Idan nace zan faÉ—i kyanka tabbas sai dai na rageta, dan baki ba zai iya zayyana shi ba, meyasa ka É—auki tsawon lokaci kana mun rowar ganinka?". Ta jefa mashi tambayar tana É—aga mashi gera guda.
Chapter 70 · 0% Book details