← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 221 OF 242

Sashe 221

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba karya ta yi fitina sosai cikin white abayan, ta yi rolling veil a kanta, ta É—auki karamar fashion bag and flat shoe dik white color kalar rigar, sai tashin kamshi take zubawa ta nufi bedroom É—insa. Bakinta a É—auke da sallama ta shigo cikin room É—in. Yana zaune a in da ta barsa hannunsa rike da cup of cappuccino, yanzu tsohuwar ta kawo mashi cappuccinon da kayan abincin ta fita, har ta sake shirya masu wani kenan, yanzu ya É—auki cappuccinon bai kai ga sha ba!!.

Ai tana gani bata san lokacin da ta ƙariso cikin room ɗin da sauri ba, shi kuwa yana ɗaura idanunsa a kanta ya kafeta da kallo, ta yi fitina sosai, yanzu a ƴan kwanan nan wani irin sihirtatcen kyau take karawa na musamman. "Yah Ramish cappuccino zaka sha?". Ta jefa mashi tambayar a ya yin da ta iso wajensa. Kai ya jinjina mata haɗe da cewa. "Aesh you're so pretty, zo ki sha cappuccino sai mu tafi ko? Lokaci na kurewa". Ya kai karshen maganar tare da kai cup ɗin bakinsa da nufin ya kurɓa.

Ai bata san lokacin da ta tafi kamar zata faɗi cikin dabara ta buge cup ɗin ya faɗi ƙasa ba, cup ɗin ya fashe cappuccino ya zube a ƙasa. A hanzarce ya ɗago kai yana ƙoƙarin yin magana sai faɗowa ta yi jikinsa mai gabaɗaya tare da fara salatin karya a zuwan zamewa ta yi ta faɗo jikinsa ba da gangan ba.

"Aesh lafiya kuwa?". Ya faɗa yana kallon face ɗinta, ta datse idanu wai irin ya zaci da gaske ne ma. Yunƙurawa ta yi zata bar jikinsa saboda shegen iya basaja. Rikota ya yi yana kallan face ɗinta. "Aesh yakamata in kai ki hospital a dubaki, naga kamar jiri yana damunki".

Ya bata satar amsa, sai kuwa ta ce. "Nima abin yana bani mamaki, kawai ina tsaye na ji jiri ya ɗebeni". Sorry ya ce mata tare da kai hannunsa ɗaya saman goshinta ya taɓa. "Ga shi jikinki babu zafi, amma dik da haka bari mu dawo zan ɗauki mataki". Langwaɓewa ta yi a jikinsa wai irin ta kara nuna bata da lafiyar nan.
"Aesh ko dai mu wuce hospital ɗin nan ne?". A ɗan rikice ya yi maganar. "A'a mu je airport ɗin dai mu dawo". Ta faɗa tana sake yunkurwa zata bar jikin nasa. Sake riƙota ya yi, take suka zubawa juna idanu a kurkusa, wani irin kallo mai cike da sirrika suke aikawa junansu.

"Idan kika tashi jiri ba zai sake ɗibarki ba? Ko in kaiki mota da kai'na?". Ya faɗa idanunsa sosai a cikin nata. Ƙasa iya basa amsa ta ta yi, abin da yake cikin zuciyarta yana neman fin karfinta.
"Aesh" ya faɗa yana mai da kallansa kan soft lips ɗinta da suke ɗan kerma kamar mai jin sanyi. Bata iya amsawa ba. Zai sake yin magana wayarsa ta fara ringing. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Let's go, kinga kin sa har jirginsu ya sauka ban isa airport ba, dan ma babu nisa nan da 5 mins zamu isa". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa da ita a jikinsa. A haka suka nufi waje. Ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta ya kwnata, burinta na ɓata mashi lokaci ta hana shi shan wani cappuccino ko cin wani abin ya cika.

Sai dai daga shi har ita basu lura da cappuccinon da ya zube a kasa ba, ya canza kala daga brown zuwa dark green sosai, kamar ba cappuccino ba, suna fita wannan tsohuwa ta yi gaggawar zuwa domin tattare komai, a gaggauce ta goge cappuccinon da ya zube, tasan basu sha komai ba, dan dik abin da suke faɗa kada ku manta tana jinsu, ranta bai so hakan ba sam, ranta ya sosu, haka ta kwashe kayan abincin ta fita da shi tana tinanin irin hukuncin da zata yi wa Leesharh, ba zata kyaleta ba sai ta hukuntata! Dan tana ganin kamar ita take sanya Ramish yana tsallake tarkonsu, kuma hakan ce, sau da dama Leesharh tana shiga tsakaninsu ba tare da ta san ta shiga ba, kamar dai yadda ta ɓarar da abincin ɗazun da suka yi karo, kun ga bata san akwai wani abin a cikin abincin ba ta ɓarar, to haka dayawan lokuta sai sun yi shiri a kansa sai ta shiga tsakani ta watsa komai.

Daren jiya Ramish zai fita ta hana shi ta hanyar ce mashi tana tsoro kuma ita ba zata iya fita waje a daren nan ba bare ta bisa, haka ya fasa fita, kuma sun shirya mashi mugun abu a fitar da zai yi, kunga Leesharh ba tare da saninta ba a nan ma ta shiga tsakaninsa da su!!.

---------------------------------------🔥🔥

Bai direta a ko'ina ba sai a cikin mota, da gudun gaske ya shiga ya figi motar suka bar gidan. Saboda gudun da yake yi yasa suka yi saurin isa airport, a dai'dai lokacin su Smart suka fito daga cikin jirgin yana rungume da gawar Auta. Ai Ramish yana ganinsu haka bai san lokacin da ya ɓalle kofar motar ya fito waje ba, take ya ji zuciyarsa ta amsa, hankali nan da nan ya tashi, a ruɗe ya ce. "Yah Omerish meyake faruwa? Meyasameta?".

Dai'dai lokacin Bilal ya yi parking motarsa shi ma ya fito. Smart bai yi magana ba ya buÉ—e gidan baya na motar Ramish ya kwantar da Auta a ciki, sannan ya yi juyo ga su Jaish. "Ku bi Bilal izuwa gidan uncle, bari in je ni da Zunaira, ka kula da Omar". Fitowa ita ma Leesharh ta yi daga cikin motar tana kallan Smart, sai da gabanta ya faÉ—i yadda ta ga face É—insa.

"Aesh shiga gidan baya ku zauna da Zunaira". Cewar Ramish kenan. Da sauri ta shiga tana kallan Smart, ta É—aga kan Auta ta É—aura a saman cinyarta, sai a lokacin ta lura da guyson, Allah sarki ta jima rabonta da shi, tin da ya koma kingdom of power bai sake zuwa Dubai ba, ta yi kawarsa sosai mutumin kirki. Gidan gaba na motar Ramish Smart ya shiga ba tare da ya yi masu magana ba, yau first time na haÉ—uwar Smart and Ramish face to face kenan, Ramish ya ci burin ya haÉ—u da yayan nasa mai tayasa aiki mai taimaka mashi, sai dai sun haÉ—u a wani irin yanayin da word can't explain how they're feeling, sai ma lokacin da su Ramish zasu fahimci Zunaira bata raye, uhm!!.

Bilal na kallon Ramish har cikin ido, ba dan Smart dake wajen ba da babu abin da zai hana bai ci kwalar rigar Ramish ya faÉ—a mashi dalilinsa na gudunsa ba, ya kirasa a waya baya É—auka, ya nemesa kamar hauka bai gansa ba, wlh har kuka sai da ya yi da hawayensa, ashe dama Ramish yana cikin Dubai, to me ya yi mashi da zafi har haka da zai yi mashi irin wannan hukunci? Tare suka taso, tare suke komai, rana tsaka Ramish ya gujesa dole abin ya gigita shi, har rama sosai ya yi wlh, albarkacin Smart yasa bai yi magana ba, yasan koma menene yanzu tin da yayan nasu yana nan zai warware masu komai, zai aje ye su ya ji menene ya haÉ—asu faÉ—a.

Shi ma Ramish kallon Bilal É—in ya yi ido cikin ido, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta damu, wlh yana bala'in son É—an uwan nasa fiye da kansa, dik sai ya ji bai kyauta ba, ko da Bilal yana da sa hannu a cutar da shi bai kamata ya juya mashi baya ta irin wannan sigar ba, kuma yasan Bilal É—in ba zai iya jurewa ba, amma haka ya sharesa, gaskiya bai kyauta ba, take ransa ta É—acaca, haka ya shiga mota ya tayar suka bar airport É—in zuciyarsa cike da tinani kala kala. Bilal ma zuciyarsa tana zogi ya tada motar suka wuce gidan Abbie.

Suna fitowa airport Ramish ya ce. "Yah Omerish ina zamu je?". Kai tsaye Smart ya ce. "Gidanka, and kada ka bari kowa ya san muna nan, kada momma ta sani shiyasa ban wuce family house ba".

Shin kun san dalilin zuwan Smart Dubai kuwa? Zai fara ne daga kan King Badeen kakansu kenan, wato Akka bata isheshi gani ba, bari ya fara da mai bawa Akkan da kanta umarni kafin ya koma kansu, yanzu zuwan na King Badeen ne, sai sun faɗa mashi a wace aya ce Allah ya banbanta mutane, ya ce kuma a yi banbaci kamar yadda suke yi, tun daga nasi har bakara sai sun nuna mashi a in da ya ce mai arziki mai daraja ne mara arziki kuma mara daraja ne, uhm abin babba ne. My people's ni fa bana san kanku ya ɗauki zafi sosai shiyasa nike sake maku cakwakiyar nan a hankali hankali, kun gane ai?. Ina tausaya maku ne.......🥱

"In Sha Allah babu wanda zai san kuna nan, amma Yah Omerish please tell me meya samu Zunaira". Cikin raunin murya ya yi maganar. "Mutuwa ta yi". Smart ya faɗa can ƙasa ƙasa. Ai wani irin mahaukacin birki da Ramish ya taka sai da Smart ya buga kansa da jikin glass na door, tashin hankali, ita kanta Leesharh bata san time da ta zabura ba!!.

Ƙasa iya yin magana Ramish ya yi, tamkar wanda aka datsewa baki, da bai taka burki bama ai da mutuwa zasu yi, dan babu abin da zai hana bai saki kan motar nan ba, irin wannan tashin hankali. A miliyan ya juyo da kallansa a kan Smart da yake kallon hanya, da hannu ya yi mashi alamar da ya kunna motar su je. Kasa yin magana Ramish ya yi, sai yake jin kamar kunnuwarsa basu ji mashi abin da yayan nasa ya faɗa daidai ba, yana san sake tambayarsa tongue ɗinsa ta yi mashi wani irin balai'n nauyi. Sake nuna mashi hanya Smart ya yi a kan su tafi, dan dole ya tashi motar yana ta faman sauke ajiyar zuciya yana addu'ar Allah yasa ba dai'dai kunnuwarsa suka ji mashi ba.
Chapter 221 · 0% Book details