← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 242

Sashe 76

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana can tana duniyar tinani sai gani ta yi ya kawo mata abinci saitin ɗan bakinta. Kai ta girgiza mashi alamar bata so, ta kai hannu ta karɓi spoon ɗin tana sunkuyar da kai. Ta ƙasan ido take satar kallansa, Arabs jallabiya tana yi mashi mugun kyau.

A hankali ta fara cin abincin kamar tana tsoron taunawa kada hakwaranta su karye, shi kuma ya zuba mata idanu yana kallanta, ji yake yi tamkar ya santa.

My people's me kuke tinani a wannan al'amari, wacece mai kama da Zee da ya sani? Meyasa ya yi kama da babyn Khadija? Kada ku manta babyn Khadija korean ne, ko da yake fa idan akwai jini wlh ba ta yadda ba zaka ga mutum ba, fata na dai Allah ya tashi kafaɗun Akka, dan idan zarginmu ya tabbata babu wadda ta dace da yi mashi hukunci sai Akka. (Ni ina da tantanama, anya uncle Jahiz ko ya gane Khadija zai yarda ya nuna ya ganeta kuwa?🤔 Ya kuke tinanin wannan al'amari?)

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Luv Bird 🕊️🔥

Shi da ya sami abin da yake so, ai bai saki Chuchu ba sai da ita da kanta ta kwace bakinta, a lokacin kuma ta gama kai shi ƙololuwa, dik ya rasa nitsuwarsa, idanunsa a lumshe, jinsa a sama kawai yake yi, yana ƙoƙarin dakewa ya capki tula tulanta ta yi saurin kwatar bakinta ta yunkura zata bar jikinsa.

Cikin magaggin soyayya da sha'awarta ya riƙota, kamar wani ɗan shaye shaye da kyar ya furta. "My Jannawad ina zaki je?".

"Knocking na door fa na ji ana yi". Ta faɗa tana kallan zakarar wuyarsa, wato wannan kashi nasu na maza, kashin ta miƙe sosai tana ɗan harbawa.

Sai da ta yi magana kunnuwansa suka tsinkayo mashi knocking da ake yi. Sake ta ya yi ba dan ya so ba, da alama da mai buga wannan kofar ya ɗan kara masu ƴan mintuna da Jawad ya yi disvirjin ɗinta, saboda ya luluƙa duniyar chaskale dayawa.

Da kyar ya iya miƙewa. Ƙasan bed ɗin ya sauko, jikinsa dik wani iri. Door ya nufa yana ɗan layi. Ya ƙasa iya tambayar wanene saboda nauyi da tongue ɗinsa ya yi mashi.

Da kallo Jannawad ta bisa tana jin wani irin kaunarsa a ranta yana kara ratsata.

Yana zuwa ya buÉ—e kofar babu tambaya. Duka Jaish ya kai mashi a kirji daga buÉ—ewarsa. Har sai da ya yi layi kamar zai faÉ—i, da kyar ya kama kansa tare da waro idanunsa da kyau.

"Wani irin iskanci ne wannan? Na kai 5 mins tsaye ina dukan kofar nan, mema na rufe kofar..........?". Bai kai karshen faÉ—ar tasa ba idanunsa suka hango mashi cikin É—akin, Chuchu dake zaune a saman bed tana binsu da kallo.

Idan baku manta ba shi Jaish bai san Jawad ya yi aure ba, ya ɗebo zafin kansa kawai zai zo ya sauke a kansu, ransa ne a matuƙar ɓace saboda momma ta same shi da safen nan a kan batun Mahnoor matarsa ce, shi ne fa ransa yake ɓace, ya zo wajen Jawad dan su tattauna wannan bala'in in jisa, shiyasa ya rinƙa dukar kofar da karfi.

Cike da mamaki ya dawo da kallonsa a kan Jawad É—in, zaro idanu ya yi, shi da farko ma bai lura da yanayin da É—an uwan nasa yake a ciki ba, sai da yaga Chuchu zaune a tsakiyar bed ne ya fahimci Jawad fa a cikin mayen sha'awa yake.

Wani irin bugawa ya ji kirjinsa ta yi, da karfi ya bugi kirjin Jawad har sai da Jawad ya ji ya wastsake, cikin zafa ya danko wuyar rigarsa haÉ—e da daka mashi tsawa.

"Me Jannat take yi a cikin ɗakinka har saman bed ɗinka da sanyin safiyar nan? And wani irin shiga ce a jikinku?". Cikin lokaci ƙanƙani Jaish ya rikiɗe tamkar ba shi ba, har wani huci yake yi, a tinaninsa sheke aya Jawad yake yi da kanwarsa, ga shi ya gansu a wani irin yanayi.

Gyaran murya da uncle Abbas ya yi ta bayansu ne yasa suka yi saurin kai kallansu a wajen. Da sauri Jaish ya ɗauke kansa daga kan kallan uncle ɗin nasa, domin kuwa in dai abin da yake zargi Jawad yake aikatawa babu abin da zai ana shi yi mashi hukunci mai tsanani yau, dama su a dokarsu dik wanda ya yi zina dandaƙa ake yi mashi.

Chuchu da dama bala'in tsoron Jaish take yi tuni ya sha jinin jikinta, ta takure waje guda jiki na kerma.

"My son sake shi, ba abin da kake zargi bane, Jannat matarsa ce, kai ne baka sani ba". Cewar uncle Abbas da ya ji komai da Jaish ya faÉ—a, dan tun time da Jawad ya buÉ—e kofar ya shigo cikin parlourn shi ma.

A miliyan Jaish ya juyo da kallansa a kan uncle Abbas. Jinjina kai uncle Abbas ya yi alamar tabbatar da abin da ya faÉ—a. Kara zaro idanu Jaish ya yi. Da sauri ya juyo ga Jawad.

Shi ma kai ya jinjina mashi alamar e haka. A wani irin slow Jaish ya zame hannunsa daga wuyar rigar Jawad, like wow he was so surprised.

Uncle Abbas ne ya ce. "Jawad P.a É—inka ne ya kirani wai yana ta kiranka baka picking time na tashin jirginku ya kusa".

Da sauri Jawad ya juyar da kallansa izuwa cikin É—akin, kan wayarsa ya sauke kallansa, lallai kuwa soyayya ta yi daÉ—i, har ma anyi sallar asuba shi yana nan ya afka wata duniyar.

ÆŠan dafe kansa ya yi, babu ko kunyan daddyn nasa ya ce. "Sorry daddy, Jannat tasa ban ji kiran ba, amma yanzu zamu shirya mu fito".

Jaish dai kamar ruwa ya cinyesa a wajen, faÉ—i yake yi a cikin ransa shikenan Jawad ya gama yi mashi fata fata da mutumci a idanun kannensu, Jawad ya gama da shi ya ja mashi kima a kan titi, yanzu shikenan Jannat tasan komai, gaskiya idan ya kyale Jawad bai yi mashi hukunci ba ya cuce shi dayawa.

Uncle Abbas kuwa cewa ya yi. "Ina zaku je ne dama?".

Ɗan sunkuyar da kai na munafinci Jawad ya yi, sannan ya ce. "Daddy wai dama Jannat ce ta ƙasa samun nitsuwa a nan, sai kuka take yi mun ta ƙasa barci, shi ne fa dama zan ɗauketa mu je honeymoon a Dubai".

Da yake uncle Abbas ma É—an zamani ne sai ya ce. "Yanzu kai Jawad ba zaka iya kwantar mata da hankali a nan ba sai kun je Dubai?".

Shiru ya É—an yi yana Æ´an kame kame.

"Anya kai namiji ne kuwa?". Uncle Abbas ya sake jefa mashi tambaya. Nan ma dai shiru ya yi.
"To ni ban yarda ku je ko'ina ba, ku na nan, idan baka iya kwantar mata da hankali a nan na ga É—an uwanka ya koya maka". Yana kai karshen maganar ya juya ya fice abinsa.

Jaish ya gama zuwa har wuya, ɓacin rai kan ɓacin rai, sarai Jawad ya lura da shi, shiyasa ya yi readyn guduwa, dan yasa saboda uncle Abbas yana wajen ne yasa Jaish ɗin ya daure bai aiwatar da abin da ya yi niyya ba.

Tsabar tsakiyanci irin na Jawad, uncle Abbas na tafi ya dawo da kallansa a kan Jaish, cike da neman tsokana ya ce. "Babban abokin ango kuma yaya babba zo mu je ka gaisa da amarya, dama tana kewarka ai.........." Bai kai karshen maganar ba ya yanka a miliyan ya fito waje saboda wani irin capka da Jaish ya kai masa a wuya, Allah ya taimakesa ya zulle ya yo waje.

Da gudun gaske Jaish ya biyo bayansa, dan yau wlh ba zai kyalesa ba, ya zubar mashi da mutunci, wannan ai iskanci ne, dama ga zafin ɓacin ran anki ƴar kauye Mahnoor matsayin matarsa, sai ya haɗa dikka zai sauke a kan Jawad.................

Wayyo abubuwa sun haɗewa Jaish fa😅

Bari mu leƙa wani part mu dawo.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥 DUBAI🔥🔥🔥🔥

AFTER SOME WEEKS.

Zaune Sharifat take a saman bed, Leesharh na tsaye a wajen dressing mirror tana ɗan gyara face ɗinta, har ta mayar da jikinta ta yi ɓulɓul abinta saboda kulawa na musamman da ta samu daga Abbie, Yah Bilal, and Sharifat, sai ta yi saurin recovery.

Sanye take da riga da wando Pakistan mai bala'in kyau launin purple color. Ta gyara gashin kanta, sai dai hannunta har yanzu bai gama warkewa sosai ba, sun koma kamar yadda suke a da ita da Sharifat, suna kula da juna haÉ—e da nunawa juna soyayya.

Irin kayan jikin Leesharh shi ne a jikin Sharifat, sai dai ita nata maroon color ne. Hira da guyson Sharifat take yi a Whatsapp a in da take faÉ—a mashi Obaid and Omaid sun samu hutun karshen shekara suna gidan King Badeen, sun ki zuwa gidansu sun ce Tunisia kawai zasu wuce.

Shi ma guyson kwance yake a saman bed É—in momma daga shi sai Short, ya rungumo pillow a kirjinsa yana aikin wannan sakalancin nasa da ya saba, shi kaÉ—ai sai turo baki yake yi.

Sun nitsa cikin hiran da suke yi wayar Leesharh dake kusa da Sharifat ya hau ƙara.

A razane Leesharh ta É—ago da kallanta a kan Sharifat ta cikin mirror, ita ma Sharifat kai kallanta a kan wayar ta yi.

Private number ne yake kira, hakan yasa Sharifat ta dawo da kallanta a kan Leesharh, cikin sauri kamar maras gaskiya ta kawar da kallanta tana É—an kame kame.

"Leesharh wayarki na kara kuma private number ne". Cewar Sharifat.

Wani irin dum dum Leesharh ta ji kirjinta ya buga, domin kuwa ko bata ɗaga ba tasan masu nikaf ne. Jiki ba kwari ta juyo ga Sharifat. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufo Sharifat. Wayar Sharifat ta ɗauko ta miƙa mata.

Tana karɓa wayar ya katse. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da Sharifat ta ɗan yi mamaki. Kunna data Leesharh ta yi haɗe da shiga cikin Whatsapp ɗinta.

Sakon Yah Bilal kawai ta gani a ciki har wajen massages guda biyar. Sake satar kallan Sharifat ta yi, sai taga baiwar Allah ta mayar da hankalinta a kan hiran da suke yi da guyson.

BuÉ—e sakon ta yi cikin sauri kamar wadda take kan gangara.
Chapter 76 · 0% Book details