Sashe 188
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuwa binta da kallon tuhuma ya yi, yadda ya ga idanun nan nata bai yarda da ita ba, dole akwai abin da take shiryawa wanda bai sani ba, dan haka sai ya gyara tsayuwarsa a jikin door ɗin, ya harɗe hannunsa a saman kirjinsa da kyau ya cigaba da binta da kallon dan gane ina ta dosa. Gabaɗaya sai ta tsargu, ita kaɗai sai ta rinƙa sauke ajiyar zuciya tana ɗan dafe kirjinta, sai kuma ta rinƙa satar kallonsa ta kasan ido wanda dik yana kallonta, alamar rashin gaskiya dai ya tabbata kamar yadda yake zargi.
"Aesh". Ya faÉ—a ba tare da ya kawar da kallonsa daga kanta ba. Kin amsawa ta yi, dan tana ganin ko magana ta yi zai gane bata da gaskiya. Nisawa ya É—an yi kafin ya juya, kamar bai gane komai ba ya ce. "Tin da ba zaki yi mun magana ba to na tafi, zan fita nan da 30 mins, zan dawo da wuri, pray for me". Ya kai karshen maganar tare da barin wajen ba tare da ya sake É—aure idanunsa a kanta ba.
Wani irin daɗi ta ji da ya tafi, da gudu ta diro kasan bed ɗin tana sauke ajiyar zuciya, bukatarta kenan. Kai tsaye kofar ɗakin ta nufo domin ta leƙa shi, ya yi matuƙar kyau cikin wanna dressing ɗin, dama daurewa kawai ta yi ta ki kallansa, tin da ya tafi shi ne bari ta leƙa ta kallesa.
Sai dai kash, tana leƙowa suka yi four eyes, dan kuwa ba tafiya ya yi ba, ya ɗan yi baya ne ya tsaya a wajen tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana bin kofar ɗakin nata da kallo, kamar yasan zata zo leƙa shi. Ai suna haɗa ido bata san time da ta kurma ihu ba, saboda ya mugun bata tsoro, bata yi zaton zata gansa a haka ba, ga shi ya ɗan saki manyan idanun nan nasa sai ya yi kama da ya zarosu, hakan ya kara razanata. Abin gwanin birgewa gwanin ban dariya.
Da gudu ta juya ta koma cikin ɗakin tana cigaba da kurma ihu. Har da turo kofa zata murza key kamar wata mai aljanu. Hannu ɗaya yasa ya tare kofar ya hanata rufewa. Ai a miliyan ta saki kofar ta koma ciki, ta ji haushin da ya kamata zata leƙa shi, sam bata so haka ba.... Oh su Leesharh ana so ana kai wa kasuwa, wai ita mai amana, ta zage ba zata ci amanar Sharifat ba, to da alama soyayyar Ramish ne zai kasheta........ Suna yi ina shan maltina and exotic mai sanyi......🥱
Turo kofar ya yi ya dawo ciki. Tana tsaye a tsakiyar ɗakin ta yi ƙasa da kai tana kuka. Ko me na kukan kuma?. Oho mata dai. Tsayuwa ya ɗan yi na sakanni a bakin door ɗin, sannan ya taka izuwa ciki, mamakin kukan nata yake yi, amma kuma ya ji daɗi yadda ya gane cewa tana san kallon shi, in bata san shi ba zata rinƙa leƙosa tana san kallonsa idan yana waje ba. A gabanta ya tsaya kafin ya kai hannu ya riƙo hannayenta cikin nasa. Wani irin shock da ta ji ne yasa ta yi saurin ɗago kanta, while kukan nata ma ta ji ya tsaya cak.
Ƙasa sosai ya yi da murya kamar mai raɗa, cike da class haɗe da sigar rarrashi ya ce. "Aesh menene abin kuka kuma? Na yi maki wani laifi ne yanzu kuma?". Ya subhanallah, ai yadda ya yi magana yasa bata san lokacin da ta ji gabaɗaya ya kwance mata notikan ƙwaƙwalwa ba, ta ji tamkar ba'a duniya take ba.
Rasa abin faɗe yasa ta ce. "Ba kai ne kake ta kallona ba". Ita kanta tasan bata da dalilin yin kukan nata. "Da wani idanu kika kalleni har kika san ina kallanki?". Ya faɗa kamar mai raɗa. Irin wannan kallon nata mai kama da harara mai matukar tafiya da imanin nasa ta bishi da shi kafin ta yi ƙoƙarin kwace hannunta daga nasa tana faɗin. "Ni ban kalleka ba, kuma ka dai'na kallona". Ta kai karshen maganar tare da kwace hannunta da nufin ta bar wajen, tana ɗaure fuska, kamar wata maras gaskiya ta yi saurin kai hannu saman face ɗinta tana goge hawayenta, saboda tsabar karya na zuciyarta har da raya mata nadamar zub da hawaye a gabansa da ta yi, a gaggauce ta nufi toilet dan ma kada su sake haɗa ido.
Sarai yana lura da dik wani motsinta, ya tabbata yau bata da gaskiya, akwai abin da ta ɓoye mashi, amma koma menene zai gano ne, binta da kallo ya yi yana mamakin yadda idan tana tafiya surar jikinta yake motsawa cikin natsuwa da ɗaukar hankali. Sai da ta kurewa ganinsa sannan ya juya ya fita zuciyarsa na saƙa mashi abubuwa daban daban a kanta.
Shirinsa ya yi tsab cikin tsadaddun kayansa, sannan ya É—auki car key da wayarsa ya fice daga gidan, tana tsaye a jikin window tana kallansa har ya fita, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, lokaci guda ta saki cool murmushi dan ta kalli yadda ya buÉ—e gate É—in, kenan ta samu abin da take so. A gaggauce ta saki curtain na window ta dawo cikin bedroom É—in, echolac É—inta ta janyo daga cikin dressing room, jikinta na kerma saboda sauri, please call me hijab É—inta dake saman bed ta É—auka, a gaggauce ta nufo stair case, ko tura kofar bedroom É—in ta rufe bata yi ba, kirjinta sai bugawa yake yi, fargaba kamar zai kasheta, har ta fara haÉ—a gumi.
Cikin sauri ta yi ƙasa, bibbiyu take tsallake stair case ɗin. Tana fitowa harabar gidan har da haɗawa da gudunta wajen isa wajen gate, kamar yadda ta ga ya yi haka ita ma ta yi wajen buɗewa, ta kuwa yi dai'dai, kaifin ƙwaƙwalwarta dai yana taimaka mata wani sa'in. Ta sha madarar mamakin ganin yanayin arear a zahiri, tsayawa ta ɗan yi wajen yin ƴan waige waige tana kallan hamshaƙan gidajen dake wajen, gaskiya sun haɗu iya haɗuwa. Ganin zata iya shekara a wajen ba tare da ta gaji da kallan ƙawatuwar arear da gidajen dake wajen bane yasa ta yi gaggawar jan echolac ɗinta ta kara gaba. Tana tafiya tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Ganin yadda take yi ne ma yasa Officers dake tsaron main gate suka tareta haɗe da tambayarta wacece ita kuma ina zata je?.
Bata ɓoye masu wacece ita ba, har da yi masu kwatancen Ramish, ta ce masu ita ce suka fita da shi rannan, Officers ɗin sun ganeta sosai, sai suka saussauta muryoyinsu a kanta wajen tambayarta ina zata je da ta fito yanzu? Kuma meyasa take tafiya take waige waige haɗi da sauri haka kamar zata faɗi? Lastly ina Ramish da ta fito ita kaɗai?......... Yau Ramish ta north gate ya fita, bai biyo ta main ba, shiyasa basu ga fitarsa ba. Murya na rawa ta hau basu excuse ɗin cewa Ramish yana gida ita kuma zata je gidan Abu Abdussalam ne duba ƴar uwarta Sharifat, ta yi maganar cike da fargabar kada ace sun ga fitarsa su gano karya ta yi masu su mayar da ita gida ko su kirasa a waya, jin cewa sun tambayi ina yake neman yasa ta yi zatan kila basu ga fitarsa ba, tin da tasan gate uku ne arear take da shi.
Da farko sun so su É—an yi kokwanto a kan fitarta, amma da suka tina wanenen Ramish sai suka ji ba zasu iya ja da ita ba, kada yazamana shi ya ce ta tafi su kuma su kutsa cikin lamarinsa su ja wa kansu, dan haka sai suka bata hanya cikin mutumci har ma da É—aga hannu su sara mata, ta ci albarkacin Ramish.
A hanzarce ta wuce, bata sake waigosu ba har ta yi nisa, dan tana tsoron waigowa su sake jefanta da wani tuhuma. Tafiya take yi ba tare da ta san ina ta nufa ba, har da saurinta gudun kada ruwan sama ya jiƙata, ta ga garin nata kara narkewa da hadari.
Tsawon good two hours tana tafiya, idan ta gaji sai ta zauna ta huta, ta yi tafiya mai nisan da har ta dai'na jiyo ƙamshin arear tasu. Daga karshe da wahala ta yi wahala kafafunta dik sun yi mata tsami sai ta nemi waje saman wani kujera da ake shiryawa a bakin hanya dan jiran ƙananan jiragen ƙasa masu kama da bus ɗin nan, a nan ta zauna tana mayar da numfashi, ga wani irin kishirwa da take ji, saboda tafiyar da ta yi.
Tinawa ta yi a ranta yau saura sati a fara azumi, lokaci guda ta ji zuciyarta ta buƙaci da sanin ina zata samu mafaka? Afkawa ta yi duniyar tinani dan nemanwa kanta mafita, bata yi aune ba sai ji ta yi ruwan sama mai karfin gaske ya kece kamar da bakin kwarya, juyawa ta yi gabas da yamma, kudu da arewa babu mafaka a wajen, sai dogayen bishiyoyi dake can nesa da ita, wani irin tsoro ne ya dira a ranta lokaci guda, sai ta ji tamkar ta koma, sai dai kuma ita kanta bata san ta wani hanya ta bi ta zo nan ba, tafiya kawai ta yi ta yi.
Wasa wasa ruwa na kara yawaita while gari na kara tsananta duhu, bata da mafitar da ya wuce ta zauna a wajen, dan babu mafaka a kusa. Tana ji tana gani train na farko ya zo ya tsaya a gabanta har tsawon mintuna biyu, a zaton drivern shiga zata yi, suna cika mintuna biyu kamar yadda yake a dokansu drive ya tasheta ya kara gaba. Kazalika train na biyu ma ya zo ya tsaya, nan ma bata iya miƙewa ta je ta shiga ba, dan bata da wajen zuwa. A haka tana zaune a wajen har train huɗu suka wuce, ruwan sama ya yi mata dukan gaske, ga shi ko kaɗan ruwan yaki tsagaitawa, bata san lokaci ba, dan babu abin duba time a hannunta.