← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 242

Sashe 49

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har kamar zai fita waje da ya fito daga wanka, sai kuma ga kalli sabbin Queen cover shoes masu bala'in kyau a kofar ɗakinsa, hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, shi ne ya ce bari ya shiga ya ga wacece a ciki.

Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Arɗo ne ya amsa mashi sallamar tasa. Yana ɗaura idanunsa a kan momma ya gane cewa mahaifiyar Jaish ce, wani irin farinciki ne ta lulluɓesa, Allah sarki har kasa haƙura ya yi sai da ya tambayi ina Jaish, ko zama bai yi ba.

Sai dai da fulatanci ya tambaya, ya manta da basa jin fillanci, sai da ya ji momma bata amsa shi bane yasa ya juya harshe izuwa larabci.

Mahreen tana ganinsa ta yi sauri ta zo ta rungumesa tare da saka mashi kuka tana faÉ—a mashi hamma bai dawo ba sai dai wani mai kama da shi ne ya zo. Guyson kenan.

Nan take bappa ya ji jikinsa ta yi sanyi, gabansa har sai da ta faÉ—i, dik tinaninsa Jaish ya dawo garesu ne. ArÉ—o ne ya ce mashi ya nemi waje ya zauna momma wajensa ta zo.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya samu waje ya zauna yana tinanin Jaish. Cikin mutunci da girmamawa ya É—agawa momma gaisuwa da larabci.

A É—an dake ta amsa mashi kafin ta É—an yi shiru na Æ´an mintuna. Sannan ta gabatar mashi da wacece ita da kuma abin da ya kawota.

Sosai bappa ya sake jin zuciyarsa ya karaya, wato godiya suka zo yi mashi ma ba wai sun kawo Jaish bane, sam abin bai yi mashi daÉ—i ba, ba haka ya so ba, shi bai yi dan ayi mashi godiya ba, saboda Allah da kuma kaunar da yake yi wa Jaish ya yi.

Ganin ya yi shiru kaman ya shiga damuwa ne yasa Momma ta buƙaci da ya bata tarihin a ina ya ga Jaish da har ya rikesa na tsawon watanni haka?.

Jiki ba kwari ya zayyana mata komai daga farko har karshe, bai ɓoye mata komai ba har da gudun Jaish da ƴan kauyen suka rinƙa yi suna ce mashi aljani, dik ya zayyane mata.

A gabaɗaya maganganunsa da ya faɗa abu ɗaya ne ya yi mata daɗi shi ne Jaish ya yi aure, wannan magana ta yi mata daɗi sosai, har sai da ta ɗan murmusa, cike da farinciki a ranta ta buƙaci da a nuna mata matan ɗanta.

Bappa ya yi mamakin ganin bayyanar farinciki a tattare da ita daga jin Jaish yana da mata, ya yi zaton zata ki batun auren, ashe ba haka bane baiwar Allah. Tabbas momma har cikin ranta ta ji daɗi, saboda ko ba komai ta kara samun ɗiya mace, sannan kuma zata rama masu alkhairi da suka yi mata, sun cancanci hakan, sun cancanci a rike masu ƴa da amana, dik ɗan halak ba zai manta halacci ba, dan haka tana maraba da Mahnoor from the button of her heart. Kuma ni da ku mun san bappa ya yi matuƙar ƙoƙari a kan Jaish, kada ku manta fa farko ko irin abincinsu Jaish baya iya ci, amma haka bappa ya rinƙa yanka mashi nama yana ci, dik kaunar ƴan kauye da dabobinsu haka bappa ya sadaukar da nasa dabbobin wa Jaish, ai ya yi namijin kokari.

Allah sarki ni Princess Teema na ji matuƙar tausayin Fanan, tana murna Jaish ɗinta ya dawo sai aure, ashe mata garesa, heart breaked!!.

"Mahreen jeki ki kira Mahnoor a É—akinta". Cewar Bappa.

Cikin kunci, tana guntun kuka ga hawaye a saman face ɗinta ta miƙe ta fita, sai gunjin kuka take yi. Godiya momma ta yi wa bappa sosai tare da nuna mashi jin daɗinta a kan wannan aure, ta kara mashi wani godiya na daban a kan bawa ɗanta mata da ya yi, daga karshe ta rufe mashi da zata tafi da Mahnoor.

Tashin hankali, nan fa matsalar take, dan kuwa bappa bai shirya rabuwa da Mahnoor ba, a tinaninsa wai sai dai Jaish ya zo su yi zaman aure da ita a cikin kauyen, shi bai yarda a ɗauketa ba, ita kuwa Momma ta ce mashi ina hakan ba zai yiwu ba, Mahnoor matar Prince ce fa ba wai matan mutum gama gari ba, ai kuskure ne ma su bari wani yaga face ɗinta, nan fa momma ta shiga zayyana mashi dokikin gidan sarauta da tsarukanta da yadda matansu suke kasancewa cikin tsaro da lulluɓe kai, daga karshe ta ce tafiya da Mahnoor dole ne!!! Idan suna da ra'ayi su tashi mutanen da zasu bisu su ga in da suke, amma tafiya kam babu fashi............ Babbar magana.

Bappa ya yi shiru cikin ransa yana tunanin yadda zai fara rabuwa da yarsa. Dik tattaunawar da suke yi Ibrahim kawunta yana jinsu, dan yana zaune a tsakar gida, ba ƙaramin daɗi ya ji ba na jin matsayin da Mahnoor ta samu, abin da basu taɓa tsammani ba, ya ji daɗi da suka ce zasu tafi da ita, kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha.

A tare Mahreen da Mahnoor suka shigo cikin ɗakin, Allah sarki ashe da ta koma cikin ɗakinta kuka ta je ta rinƙa yi, idanunta har suka kumbura. Suna shigowa bappa ya ce da momma ga matar Jaish ɗin, ya kuma cewa Mahnoor wannan mahaifiyar mijinta ne ta je ta gaisheta.

Matsawa ta yi kusa da momma, kanta a kasa ta tsugunna zata gaisheta. Jawota momma ta yi ta runguma tana tsananin farinciki, dan kuwa tamkar an shiga ranta anyi bincike kafin a bashi wannan mata, tabbas irin matar da take mashi fata take kuma yi mashi addu'ar samu kenan, kyakkyawa san kowa kin wanda ya rasa, abin ya yi mugun yi mata daÉ—i, dik wani bakincinkinta sai ta ji ya kau, tamkar zata mayar da Mahnoor cikin cikinta saboda so da kuma murna.

Shi dai bappa dik wannan bashi bane damuwarsa ba, ya za'ayi momma ta ce, zasu tafi da Mahnoor? Gaskiya ba dan su gidan sarauta ba a ja in ja da su ba wlh da shi dai ba zai yarda ba, amma ba yadda ya iya.

Dai'dai lokacin Jaish ya kira Momma ta Whatsapp, voice call kuma ya kirata, dan ya gwada number kai tsaye taki shiga.

Ganin shi ne yasa ta yi saurin É—auka, cikin nitsuwa suka gaisa ya tambayeta ya hanya?. Murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha ta ce mashi ai gata a cikin gidansu tare ma da matarsa.

Ya ɗauka wasa take yi sai ya ce. "Momma kada ki ɓata lokaci please, ku dawo da wuri dan har na damu na fara kewarki".

Ita kuwa sai ta ce mashi ga matarsa nan su gaisa.

A É—an dakile ya ce. "Mata kuma?!".

Jinjina mashi kai ta yi haÉ—e da tabbatar mashi, bada ban ita ta ce matarsa ba da ya ja tsaki kuma ya kashe wayarsa, amma ita ce ya zai yi? Sai ya ce.......... "Please momma kada ki fara wannan zancen auren naki, ni kada ki ce ma zaki ga Æ´ar mutane ki saka mata ran aurena, bani da lokaci a yanzu, please kada ki mun irin abin da kika yi wa uncle Abbas, zan tabbata cikin kunci". Yana maganar fuska a É—aure tamau kamar hadari, alamar bada wasa yake yi ba!!.

Kunsan momma ita ta haɗa auren uncle Abbas da maman su Yah Jawad, kawai daga ziyara ta haɗa wannan aure, to shi Jaish a tunaninsa irin taga mace kyakkyawa ne ta ce zata zaɓa mashi, kwata kwata bai taɓa kawowa ransa matar ta gaske ce kuma mallakinsa ce ba.

Momma da ta rasa me zata ce mashi saboda bata san tsayawa yi mashi dogon bayani ta waya, sai ta ce mashi zasu yi waya anjuma, yanzu bari ta samu ta bar wannan kauyen su kamo hanyar kasarsu shi zai fi.

Da okey ya amsa mata, har zai katse kiran kuma sai ya sake ce mata dan girman Allah shi kada ta jajuɓo mashi bala'i yana zaune lafiyarsa. Bata amsa mashi ba ta katse kiran, dan bata san biye mashi yanzu.

Bappa dik da bai san da waye take waya ba sai ya ji yana san yin magana da na cikin wayar, dan zuciyarsa na faÉ—a mashi da Jaish take waya.

In short haka momma ta gama dik abin da zata yi, ta kawo makudan kuɗin da suka canza nasu izuwa na Nigeria, miliyoyi ta bawa bappa, suka kara yi masu godiya sosai, sannan ta ce yakamata su tafi da wani ya bisu ya ga ƙasarsu.

A nan ne ArÉ—o ya ce su tafi da kawu Ibrahim. Bappa ma ya aminta da hakan. Sai kuma me?.

Momma tana rike da hannun Mahnoor taki saketa, sai da suka je zasu shiga motocinsu Mahreen ta ce wlh basu isa ba, bata ga uban da zai rabata da Æ´ar uwarta ba. Ita ma Mahnoor É—in kuka ta saka masu, ta ce wlh ba zata iya rabuwa da Mahreen ba, infact sai cewa ma ta yi da a rabata da Mahreen gara ta hakura da Jaish É—in har abada.

Ganin haka yasa momma ta ce zata tafi da su dikkansu biyu kuma ta yi alkawarin zata rikesu amana, dan ba zata iya barin Mahnoor ba, ai ita taga wa É—anta matar da babu rabuwa.

Nan fa bappa kuma ya ce gaskiya bai aminta a tafi da Mahreen ba, to shi wa za'a bar mashi?. Sai da Arɗo yasa baki ya roƙesa a kan ya dubi girman Allah kada ya raba ƴan uwan nan guda biyu, tare suka taso, tare suke komai, suna bala'in kaunar junansu, idan ya rabasu wlh zai cutar da su ne, ya yi hakuri ya kyalesu su tafi ɗin kawai.

Kun san abin isn't easy wlh, rabuwa da yara biyu lokaci guda, yaran ma su kaÉ—ai ka mallaka, a rabaka da su kai akwai wuyar iya É—auka fa. Da kyar da suÉ—in goshi bappa ya aminta da su tafi a tare. Kawu Ibrahim ya yi masu rakiya suka tafi.
Chapter 49 · 0% Book details