← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 242

Sashe 103

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Sannan kada ki ji tsoron kwanciya a jikinsa idan har ya hau gadan, dik zafin kansa da kike ganin nan bai kai mahaifinsa a lokacin da yake matashi ba, so ni na faɗa maki dik zafin nan nasa ba zai iya taɓuƙa maki komai dangane da faɗa ko kyara ba a lokacin da zaki zo garesa, in dai kin bi dik tsarin da na tsara maki, lastly dik abin da zaki yi ki sanya nitsuwa a ciki, dik da naga kina da nitsuwa, amma ki kara, dan dik wani namiji yana san mace mai nitsuwa, nitsuwar tana jan hankalinsu sosai".

Tsabar daɗin kalaman momma har ji ta yi tamkar ta jawo dare ya yi, a yanzu dai gani take yi tamkar zata iya aikata dik abin da momma ta ce, sai ta ji ta matsu lokacin ya yi, har ga Allah tana kewarsa, kuma ya saba mata da hot kiss kafin su yi barci a Jimeta, to yanzu babu, da kyar take iya yin barci, ga ɗamin jikinsa dik bata samu, kuma tana buƙata, sai ta ji tana buƙatar dare ya yi da wuri yau ta kwana a saman kirjinsa....... Wayyo my belly, Mahnoor is to much, love ya rufewa yarinyar nan idanu fa, Jaish ɗan duniya ne wlh, ya koyawa yarinya abu dan iskanci yanzu kuma ya ce bai san wannan ba, zaka yi bayani ne bari Queen Zarina ta aure samartakanka nan ne zaka gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah Sallallahu........😅🥱

Momma ta karanceta tsab, dan akwaita da iya harbo jirgi mutun da wuri, tuni ta gano Mahnoor fa ita ma a hannu take tana san kasancewa da mijinta, ta ji daɗin hakan, ba ƙaramar dama hakan ya bata wajen kara karfafawa Mahnoor ɗin gwiwa ba.

Sun jima a wajen suna hira har 1:30 na rana, sannan momma ta buƙaci da ta tashi suje lokacin sallah ya yi. Miƙewa ta yi ta fita ta nufi part ɗin mama Haulat.

Momma na ƙoƙarin miƙewa ta shiga toilet sai ga mama Haulat ta shigo baki a ɗauke da sallama. Dakatawa momma ta yi haɗe da amsa mata sallamar. Zuba mata idanu ta yi tana jiran ta ji dame ta zo. Cikin girmamawa mama Haulat ta sanar da ita Jaish fa yaki cin abincin da aka kai mashi, da mama Haulat ɗin ta je ta sake kiransa a kan ya zo ya ci sai cewa ya yi ba zai ci ba, kada mama Haulat ta sake dawo mashi cikin ɗaki a kan wannan abincin.

Jinjina kai momma ta yi tare da yi mata almar ta je kawai babu damuwa. Juyawa ta yi ta fice tana jinjina zuciya irin na yaran King.

Toilet momma ta shige ta É—auro alwala ta fito. Sai da ta yi sallah ta yi addo'inta sannan ta tashi ya nufi dry kitchen nasu, a nan ta sake shirya mashi simple things da zasu É—an rike mashi ciki, ta É—auka izuwa part É—insa.

Tana shiga yana dawowa daga musque sanye da arab jallabiya milk color. Yana ganinta ya ɗan turɓune fuska tare da zama a saman sofa. Kasa saman sinfiɗar gashin jimmina dake parlourn ta ɗaura tray ɗin abincin, sannan ta koma saman sofa ta zauna suna fuskantar juna.
Sai kallanta yake yi yana jiran ya ji me zata ce mashi. Sallamar Jawad ya katse maganar da take san yi mashi, so sai ta fasa faɗin abin da zata faɗa ta miƙe ta nufi waje tana faɗin su ci abinci to.

Allah sarki Jawad ya kasa zama a office É—insa ne jin cewa Jaish bashi da lafiya, dik ya rasa sukuninsa har sai da ya dawo ya gansa.

Kallon time a wayarsa Jaish ya yi 2:00 dai'dai yanzu, dawo da kallansa a kan Jawad ya yi. "Bro me ya dawo da kai by this time around?".

Zama ya yi kusa da shi tare da kai hannu ya taɓa forehead na Jaish ɗin yana faɗin. "How's your body?".............. "Feeling better Alhdulillah" jinjina kai Jawad ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "Ka tayar mun da hankali, all my tougth ciwon ya fi haka". Yana magana ya shafa goshin Jaish.

"No ba wani ciwo bane bafa, is just only headache, and momma ta ce rashin cin abinci ya kawo shi". ............ Allah mai iko, gasu dai kamar twins, amma shi Jawad a kan lokaci yake cin abinci, shi kuma Jaish sam bai damu da ci ba, wani lokaci sai yunwa ta yi mashi over ya ji zai iya faÉ—uwa sai ku gansa ya É—an É—auko maltina ko wani drinks É—in ya sha, dik gudun cin abincin ne fa.

Jin haka yasa Jawad ya sauko ƙasa wajen da momma ta ajiye abincin. Buɗewa ya yi ya fara zubawa ɗan uwan nasa abin da ya dace da shi yana faɗin. "Since nike faɗa maka cewa sometimes yunwa zai janyo maka wani big problem ɗin, amma baka yarda, anyway come down and eat yanzu kam".

Jaish bai yi wani gardama ba ya sauko kasan suka fara ci a tare cikin plate É—aya, suna ci suna hira sama sama.

3:00 dai'dai har lokacin suna tare momma ta kira Jawad a waya a kan ya zo. Tashi ya yi cikin sauri ya nufi bedroom É—inta yana sanar da Jaish ya kwanta ya huta even for one hour bari ya zo. Jinjina mashi kai kawai Jaish ya yi ba tare da ya yi magana ba, hayewa bed É—insa ya yi ya kwanta da nufin ya yi barci ko da na 30 mins.

Sai dai kuma yana kwanciya tinane tinane suka cika mashi barin har da tinanin yarinyar da ta kawo mashi abinci a yanzu, haka kawai ya tsinci kansa da tinanin face É—inta yadda ta tsare shi da idanu tamkar ta san shi, da tinanin yadda ta sha kwalliya har lallen hannunta yake fisgarsa gareta.

Siririn tsaki ya ja tare da ƙoƙarin kawar da banzan tinanin a cewarsa, sai dai kuma tinanin taki tafiya, saboda idan baku manta ba dama ya ce kamar da akwai wani gurbi da yake ji a cikin zuciyarsa ya rasata, to zuciya kuma yau taga burbin da ta rasa ba dole ta takura mashi ba, ai ya yi ya yi ya dai'na tinanin yarinyar nan sai ya ƙasa.

Daga karshe wayarsa ya ɗauko tare da miƙewa zaune a zuwan ya fasa yin barcin tin da wani banzan tinani ya sako shi a gaba. Balcony ya koma ya zauna ya shiga latsa wayar tasa bayan ya kunna data.

Sai dai fa ko da ya koma balcony ɗin tinaninta yaki sakesa, dik abin da yake yi face ɗinta ƙwaƙwalwarsa take kwaso mashi, abin har ya fara ɓata mashi rai.

A ɓangaren momma kuwa, magana ta sirri suka yi da Jawad har karfe 4 daidai ta cika, sannan suka rufe maganar tasu kowanne ya miƙe dan ya yi sallah, momma na miƙewa ta ce mashi kada ya manta ya turo mata Jannat ɗin fa.

Da okey ya amsa mata tare da fita ya nufi wajen Jaish dan su tafi masallaci a tare.

After some hours. Bayan sun yi sallar mangariba da isha'i. Momma da Chuchu ne zaune a saman bed É—in Momma suna jiran mama Haulat ta kawo masu Mahnoor, sai hira suke yi irin ta uwa da Æ´a cike da so da kauna.

Sallamar mama Haulat ta dakatar da su a in da suka mayar da kallansu a kanta, tana rike da hannun Mahnoor dake sanye da kyakkyawan abaya mai shegen tsada launin army green.
ÆŠan zaro idanu Chuchu ta yi tana kallan Mahnoor, da yake shekarunsu kusan É—aya sai girmansu ma yazamana É—aya.

Ƙasa shanye mamakinta Chuchu ta yi har sai da ta ce. "Momma wacece wannan?"....

Da hannu momma ta nunawa Mahnoor gefenta da ta zauna, sannan ta buƙaci da mama Haulat ta basu waje kuma nan da 30 mins ta kawo mata alkyabbar Mahnoor zata kaita wajen King. Cikin girmamawa mama Haulat ta amsa sannan tasa kai ta fita.

HaÉ—e Mahnoor da Chuchu momma ta yi a in da ta yi masu nasiha mai ratsa jiki da kyau, sannan ta tambayesu da ya ake yin wankan haila da na janaba?. Ita Mahnoor ta karanta wannan, amma kunya ya hanata faÉ—a, ita kuma Chuchu iliminta bai kai nan ba, so bata karanta ba, dikkansu biyu babu wadda ta fara period a cikinsu, shiyasa ma Chuchu bata nemi yadda ake yi ba.

Ganin sun yi mata shiru ne yasa ta fahimci basu sani ba ne, dan haka sai ta É—an yi gyaran murya kaÉ—an kafin ta fara magana kamar haka.
"Wannan tambayace da yakamata ace kowacce mace tasan amsarsa, nasan yanzu mata dayawa basu san yadda ake yi ba, amma bari in yi maku bayani dan dayawan mata su karu".

Shiru dai suka yi babu wadda ta yi magana, Mahnoor dai ta lura su fa ƴan gidan nan basa jin kunya kwata kwata, mijinta Jaish da guyson ne kawai masu kunya, su biyun nan ne masu kunya a ganinta.............. Lallai Mahnoor baki da kunya in ji ni princess Teema, wai har da uwar mijin nata ma bata da kunya kenan? Amma kuma fa gaskiya ta faɗa, ko shi Jaish daga ina ya samo nasa kunyar? Dan dai momma kam bata da shi, kada ku ce na ce na ce ɗin...........🥱
Chapter 103 · 0% Book details