Sashe 129
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bari in kara maku wani haske kaÉ—an kafin mu wuce gaba. Tabbas Smart É—an King ne, kuma shi ne babban yayansu, ya fi su Ramish dikka.
Ya aka yi ya fi su Ramish?. Mu je dai zuwa, kada ku manta ita ma mummyn Chuchu tana da babban yaro da ya fi Ramish amma ya rasu, kada ku manta na faÉ—a maku hakan a baya.
Akwai wani abin da ya taɓa faruwa a kingdom ɗin a lokacin da momma ta haifesa bai wuci kwana uku a duniya ba, so a lokacin momma ta gudu Dubai ba tare da sahalewar King ba, saboda ta ce zata tafi ya hanata, ita kuma tana ganin ɗanta zai mutu ne idan tana Kingdom of power, shi ne ta gudu bai sani na.
Time da ta koma Dubai, ta yi ta yi ta zauna iyayenta suka ki yarda saboda King ya ce bai aminta ba, ya ce ta dawo, ta yi ƙoƙarin yi masu bayani a kan in ta koma tabbas ɗanta zai mutu, amma suka ki fahimtarta, hakan yasa ta yanke shawarar shirya masu cewa Smart ya rasu. Ta kuma yi nasarar yin hakan tare da taimakon yayanta wato daddyn Smart na Faransa kenan, sai da kowa ya aminta da Smart ya mutu, sannan daddynsa ya tafi da shi France.
Momma bata taɓa yin kwana biyu bata yi video call da yayan nata ta ga ɗanta ba, hakan yasa Smart ya tashi da sanin ita ce mahaifiyarsa, yana yawan tambayarta ina daddynsa, kullun sai ta ce mashi sai ta zo ɗaukarsa zata zo tare da daddynsa. Time da ya kai 20 years sai ya matsa mata a kan lallai yana san ganin daddynsa, a lokacin ne ta kira shi video call ta juya camera ta shiga ɗakin King, so a lokacin ya fara sanin daddynsa shi kuma King bai lura da video call take yi ba, so bai ga ɗan nasa ba, da yake yayan momma ɗin yana yi mashi komai yasa bai damu da yazo ga iyayensa ba, dan suma sun ɗaukesa kamar ɗa dama Allah bai taɓa basu haihuwa ba.
Kun ji a in da Smart ya samo kamanninsa da daddynsa na France ko? Daddyn nasa yayan momma ne uwarsu É—aya ubansu É—aya wato King Badeen kenan, kunga dole a samu kamanni ai.
Shi kuwa daddyn nasa tun yana yaro ya tafi kasar France, a can ya yi karatu ya kammala, har ya samu aiki sannan suka fara soyayya da mom ɗin Smart ɗin, suka yi aure, a dalilin haka ya samu takardar ƙasa ya zama ɗan ƙasa har ya iya shiga siyasarsu.
Momma kuwa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen nunawa Smart ƴan uwansa gabaɗaya, dan bata san kan ƴaƴanta su tashi a wargaje, tana san su tashi kansu a haɗe, su kaunaci juna, ta kuma yin nasarar samun hakan, tabbas sun tashi cike da kaunar juna dikkansu, sun san juna.
Sai dai shi kuma Smart ba iya kannensa kawai ya sani ba, a lokacin da ya girma ya gama karantu sai ya fara bincike a kan Æ´an uwansa, a nan ne ya san su Ramish dikka, dik kuma yana kau taimakawa su Ramish a bakin aikinsu sosai, domin dayawan lokuta da taimakonsa Ramish yake samun karin girma har ya zo matsayin da yake, amma su basu san shi ba, kuma basu san yana taimaka masu ba.
In short shi ne ma ya binciko in da Jaish yake time da ya ɓata, sannan ya turawa Ramish address ɗin, so dik abin da suke yi yana gani kuma yana sane da su, momma take hana shi zuwa ga kingdom of power, ta ce ba yanzu ba sai ya kara girma, dan tsaro.
Harta gidan Smart dake France in da yake yawan zama in ya bar gidan daddynsa, wannan gida da sunan Zunaira ya ginata, gidanta ne da ya mallaka mata, yana da nasa na daban, ya zaɓi ya rinƙa zama a nata ne kawai, yanzu haka yana nan yana kan bincike a kan masu nikaf dan ya taimakawa Ramish ba tare da sanin kowa ba, shi ɗin garkuwan gabaɗaya familyn marigayi King Abdul Malik ne, dan yasan kowa su ne basu san shi ba, kuma yana taimaka masu ta hanyoyi daban daban wanda mutum ba zai taɓa zata ba idan dai ba faɗa mashi aka yi ba.
Jama'a nace ku zo mu haÉ—u mu tsinewa tsafi, tsafi karyar banza ne da na wofi, idan ba karya ba ne meyasa dik tsafin Mammie bai iya gane mata Smart ba? Meyasa ta kasa iya gane cewa yana raye har ma ya girma? Kullum sai dai ta kare a hasashe shegiya, karyar banza da wofi, wlh idan mutum zai koma ga Allah ma da ya fi mashi, tsafi dik surkullen banza ne shegu.
Wannan dalilin yasa kuka ga Smart and his dad musulmai ne, saboda dad É—insa yayan momma ne, balarabe ne, mom ce baturiya kuma krista, kuma tana da kyan hali, dan ita ta makale lallai tana san daddy.
To in short dai kun ji yadda labarin Smart ya kasance ko? Nasan a iya wannan bayanin kun fahimci in da na dosa, ba zan tsaya dogon bayani sosai ba, dan akwai labari a gaba sosai, gaba zaku ji karin bayani dai. Mu cigaba da labarinmu.
••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥
Tsaye momma ta isko King a tsakar ɗakinsa, sai huci yake yi, ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, zuciyarsa sai tafasa take yi, momma bata kyauta mashi ba, tasa Smart ya taso baya ganin girmansa, bai ma san shi ba, wannan ai zalinci ne.
Da alama King ya samu É—an da zai iya sanya shi ya gane yadda zafin kaunar É—a yake da yasa commander Zafar ya hukunta É—ansa É—aya tilo a duniya, dan ga dikkan alamu King yana tsananin kaunar Smart over, dan shi ne first born É—insa, har ciwo ya kwanta lokacin mutuwar Smart na karya da momma ta shirya. Wato fa idan Allah ya tashi kama mutum wlh baka isa ka iya canka ta wace hanya zai kamaka ba, ga shi dai cikin ruwan sanyi ya kama King bama aje da nisa ba, zakuwa muga yadda wannan cakwakiya zata kaya.
A gabansa momma ta zube gwiwowinta a ƙasa, cikin sigar ban hakuri ta ce. "Dan Allah ka yi hakuri Yah Zuhair, wlh ban yi abin da na yi dan na cutar da kai ko wani abin makamancin hakan ba, na yi ne kawai saboda san da nike yi wa Omerish, ba zan iya jurar rashinsa ba, kuma kai da kanka ka shaida da tabbas zai iya mutuwa a wannan lokaci, ba kai da kanka daga baya ka ce in dai'na haihuwa a nan in rinƙa komawa Dubai in haihu a can ba? Kaga da ban yi mashi hakan ba da mutuwa zai yi, kana ganin yadda Jaish ya tsira da kyar fa, kasan komai, dan Allah ka mun afuwa ka ji?".
"Kin cutar dani Rahilarh, cuta mafi munin da ba zan taɓa mantawa da shi ba!! Ki duba yadda ɗana ya taso, ya taso cikin kafurai, bai san darajar manya ba, ki kalli yadda yake magana da ni tamkar ɗansa ne ni, gaskiya kin cuceni". Cikin zafi ya yi maganar, bai taɓa shiga ɓacin rai irin na wannan rana ba, abin da ciwo matuƙa wlh, dan ma tana matsayin ƴar kawunsa ne, kuma Akka na bala'in kaunarta, da wlh sai ya hukunta hukunci mai zafin gaske.
Aunty MieMie da take binsu da kallo ne ta samu waje saman sofa ta zauna, bata taɓa kallan daddynsu a cikin irin wannan yanayi ba, gaskiya ko mafarki ta yi akwai ranar da zata zo King da momma su samu gagarumin matsala irin wannan idan ta tashi daga wannan mafarki sai ta yi sadaka kuma ba zata taɓa yarda da hakan ba, sai ga shi a zahiri ya faru, ita dai tasan sosai King yake bala'in san momma.
Mummyn Chuchu da ta shigo tun ɗazun ne ta matso tare da rike Momma dake durkushen tana ƙoƙarin faɗuwa, ƙoƙari buɗe baki ta yi dan ta taushi King.
Cikin zafa ya ɗaga mata hannu alamar baya da buƙatar jin komai daga garesu, infact su fita mashi a ɗaki baya san ganinsu. Ganin ya ɗauki zafi sosai hakan yasa mummy ta miƙar da momma tare da ce mata. "Rahilarh ki yi hakuri mu je, zuwa da safe idan ya huce sai muyi magana ko?".
Hawaye sosai momma take yi, dan ita kanta tasan bata kyautawa King ba, haba wani irin zalinci ne wannan? A lokacin da ya samu labarin rasuwar Smart yana zaune a saman kujerar mulkinsa sai da ya miƙe tsaye, bai san lokacin da ya cire crown ɗinsa daga kansa ba, ya jijjiga sosai, kwana uku bai fita fada ba yana jinyar zuciyarsa, da taimakon Allah da addu'ar iyaye da abokan arziki ya samu zuciyarsa ta iya ɗaukar wannan kaddarar, shi ma ya kusa mutuwa, ashe dik shirin momma ne, gaskiya abin akwai ciwo, babban abin da ya fi kona ran King ma shi ne yadda Smart bai ɗaukesa da daraja ba, yanayin tarbiyarsa kaf ta sha banban da tarbiyar jikokin Akka, dik ya damesu a komai ya shanye, King ya yi takaicin hakan matuƙa.
Waje gabaÉ—ayansu suka fita, suka kyale King shi kaÉ—ai a cikin É—akin yana ta huci. A bakin kofa mummyn Chuchu ta tsaya ita da Aunty MieMie suka hau sharewa momma hawaye suna tausanta har sai da ta yi shiru, sannan suka rakata É—akinta.
A parlour kuwa kowa ya yi mutuwar zaune da jin abin da momma ta faɗa, su uncle Abbas an rasa abin faɗe, Akka kuwa ta kara ɗaukar zafi, abin ya bakanta mata rai, momma ta yi masu ba dai'dai ba, a fusace ta miƙe ta nufi part ɗinta domin ta je ta kira Husaininta wato King Badeen ta sanar da shi abin da ƴaƴansa Momma da baban yayanta wato daddyn Smart suka aikata.
Da sauri Dr Raj ya miƙe ya bi bayan Akka, a cewarsa kada ciwon zuciyarta ya tashi ta sume, bari ya yi saurin bin bayanta......................... Sarina kuwa, dik abin da ake faɗa baya shiga kunnuwanta, hankalinta na'a kan Smart, sai kallansa take yi kamar zata cinyesa da ido, taga kyau iya kyau, tini ta yi rantsu da Allah ga mijinta nan ya bayyana.