← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 242

Sashe 102

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cigaba da kara mata kwarin gwiwa mama Haulat ta yi har sai da ta ɗan saki jiki ta aminta zata je, sannan ne ta saketa tana binta da kallo. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi bedroom ɗin nasa. Hannunta har rawa yake yi tasa hannu ta tura kofar tana haɗawa da ɗan siririn sallama ƙasa ƙasa.

Tana sanya kafafunta a cikin É—akin ta waro idanu waje, ya subhanallah É—akin ya haÉ—u ne sosai, sai tashin kamshi yake yi. Baya cikin É—akin, yana balcony yana waya da Jawad, Jawad ya je office É—insa bai same shi bane yasa ya kira waya ya tambayi ina yake, shi ne ya ce mashi ya dawo gida baya jin daÉ—i.

Ji ta yi tamkar ta juya a guje ta bar ɗakin, sai dai kuma tana san sanya shi a idanunta, ta yi kewarsa sosai. A hankali ta fara ɗaga kafafunta ta ƙariso cikin ɗakin, a kusa da bed ɗinsa ta tsaya tana kallan yadda king bed ɗin nan ya haɗu. Kamar ance ta ɗan ɗago kai sai ta hangosa saman wasu ƙayatattun kujeru masu laushi da kyau dake wajen yana zaune yana waya.

Subhanallah tsare shi da idanu ta yi tana kallansa ta cikin glass ɗin, shi baya kallanta saboda na waje baya kallan na ciki, na ciki ne zai iya kallan na waje. Tamkar yasan akwai mai kallansa ya kara juyowa da kyau yana fuskantar bedroom ɗin nasa. Lips ɗinsa kawai ta tsare da kallo tana tina lokacin da yake bata hot kiss a kauye, yanzu taga lips ɗin nasa su kara tura ja sosai sun ƙara kyau, da yake ya saba mata a baya sai ta ji tana kwaɗayin yi mashi kiss ɗin a yanzu, amma babu dama.

Ta shagala da tinanin soyayyarsu a kauye bata ga miƙewarsa ya nufo dakin ba sai ji ta yi ance. "Lafiya? Wacece ke?". Ya yi maganar kuma kallansa a kan zanen flowers ɗin hannunta.

A ɗan razane ta kyabta idanunta sau biyu tare da yin ƙasa da kai, a ɗan tsorace cikin sanyin murya ta ce. "Dama abinci ne na kawo maka". Tana matana tana satar kallan kayan jikinsa, ya yi makurar kyau sosai. Pj ne a jikin nasa masu silky launin milk color, kyawawan fararen kafafunsa suna cikin bedroom slippers ash colar mai laushin gaske.

Kawar da kallansa a kan hannunta ya yi izuwa kan face ɗinta, dai'dai lokacin ta ɗago kai dan ta kalli meyasa ya yi shiru. Unexpext suka haɗa ido. Wani irin faɗuwar gaba ta ji ya dira mata, shi kuwa wani irin shock ya ji a jikinsa, lokaci guda ya ji tamkar ya san face ɗinta, ƙwaƙwalensa ce ta amsa mashi, kamar walkiya ya ji tamkar an ambaci hamma a cikin kwakwalwarsa, kamar yana san tina rayuwarsa a gidan bappa ɗin.

Dik kunyar da take ji ta kasa iya zare idanunta a cikin nasa, shi ma ya kasa kawar da kallonsa daga kanta, yana jin ƙwaƙwalwarsa tana juyawa dama ga shi kansa na ciwo, bugu da kari yana bala'in san kwalliya, haba ai sai abin ya haɗe mashi, domin kuwa kwalliyarta ta fito sosai ta yi wani irin kyau na ban mamaki, ko iya kwalliyar kawai ya isa ya sanya ya kasa zare kallansa a kanta tun da yana son kyalliyar bare kuma ya haɗe da kyanta ga gyara da ta sha, sannan ga shi kamar ya san face ɗin.

Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta sosai.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

No editing💔😥

Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta sosai.

Abin ku da sun taɓa kasancewa masoya masu san junansu sosai a baya, kun san wannan abin ba zai taɓa barin zuƙatansu cikin sauki haka ba, shi kansa Jaish ɗin dik da ya dawo dai'dai ai soyayya ba karya bace, dole idan ya ga face ɗinta ko bai tinata ba zai ji a jikinsa kamar ya santa.

Nisawa ya ɗan yi, sannan ya ƙara ɗaure fuska tamau kamar bai san me murmushi ba, a takaice ya nuna mata hanyar fita da hannunsa tare da furta out. Tabbas bata san ma'anar kalmar out ba, amma ta fahimci fita ya ce ta yi ta hanyar hannunsa da ya nuna kofa da shi. Tamkar zata sa kuka haka ta juya ta nufi hanyar fita.

Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana tinanin wacece ita da har momma zata sanya ta kawo mashi abinci? Idan baku manta ba dama shi bai kalli matar da momma ta sanar da shi mallakinsa bace, an dai ce mashi yana da mata, amma bai ga face É—inta ba, so yanzu bai san ita ce wannan Æ´ar kauyen ba, ya fi tinanin ma daga cikin Æ´aÆ´an Æ´an uwan momma wato su uncle Rahab daga can ne ta zo ziyara momma ta aikota kawo mashi abinci.

Siririn tsaki ya ja tare da hayewa bed ɗinsa ya kwanta, a ransa ya zayyana ba zai ci wannan abincin ba tin da momma ta aiko mashi wata. Hmmmm dama Jaish ai da wuyar sha'ani yake, kowa kuma yasan da haka, sai ka yi kamar zaka fahimci in da ya dosa sai ya sake watsawa mutum ƙasa a ido, ji abin da ya aikata yanzu fa, harda wani ba zai ci abincin ba.

Da sauri Mahnoor ta isa ga mama Haulat, wani irin kuka ne ta ji ya kubce mata, dan yadda taga ya ɗaure fuskar nan dik da bata jin turanci sai taga kamar zaginta ya yi, abin ya ƙona mata rai.

Tararta mama Haulat ta yi, sam bata yi mamakin ganinta ta fito cikin ɓacin rai har da guzurin kuka ba, dan ita tasan halin Jaish fiye da tinanin mai tinani, tasan dama ya yarda da Mahnoor cikin ƙankanin lokaci haka abu ne mai wuya gaskiya.

So bata tambayi Mahnoor É—in menene ya faru ba, kawai ta riko hannunta suka koma wajen momma. A saman bed suka isko momma ta kwanta tana tinanin duniya, Mahreen ta tafi tare da Chuchu da suka dawo daga school ba jimawa, momma ta ce ta bi Chuchu ta kara koya mata abubuwa.

Momma na ganinsu ta miƙe zaune tana kallan Mahnoor dake sharar kwallah, dama tasan za'ayi hakan, kawai shahada ta yi ta gwada dama, to ba'ayi nasara ba.

Mahnoor na ƙoƙarin durkusawa ƙasa momma ta yi saurin ce mata ta hauro saman bed. Ba musu ta zauna bakin bed tana cigaba da sharar kwallah. Rungumota momma ta yi tare da bin mama Haulat da kallo alamar tana jiran karin bayani. Girgiza kai mama Haulat ta yi alamar bata da masaniya a kan komai.

Da hannu momma ta yi mata alama da ta tafi kawai. Cike da girmamawa ta amsa da to, sannan ta juya da sauri ta fita. Dawo da hankalinta kacokam a kan Mahnoor momma ta yi, cike da kauna haÉ—e da sigar rartashi ta fara tambayarta me ya faru?.

Kamar ba zata faÉ—a ba, sai kuma ta daure ta ce ya koreta daga É—akinsa. Ajiyar zuciya momma ta sauke, dama ta yi expecting hakan, so sai ta rarrashi Mahnoor har ta yi shiru, sannan ta ce.

"Amma ba nace maki in dai ba a cikin ɓacin rai yake ba ko ya hantareki kada ki matsa kada ki damu ba?". Momma ta jefa mata tambayar.

Cikin kuka ta ce. "Momma tsoronsa nike ji"........... Tabbas ta fahimci tsoronsa sosai take ji, dan haka sai ta shiga bata wasu dabaru ta yadda zata bi har Allah ya bata ikon shawo kansa. Ƙasa kunne ta yi tana saurara sosai saboda kaunar da take yi wa mijin nata, dik wasu shawarin momma ta naɗesu a cikin kwakwalwarta, momma bata jin kunyar nuna mata hanyar da ake bi dan maganin mazan gidan King ba, kun san ita ai ta kware, wannan hanya da take bi dan yin maganin King har ya amsa abin da bai niyya ba, shi ta zauna ta warwarewa Mahnoor komai tsab, daga karshe ta rufe mata da cewa in dai har tana san shi da gaske to ta jure ta bi dik shawarin da ta bata.

In ta dage ta yi komai cikin nitsuwa tabbas yau Jaish ba zai zulle mata ba, dan rauninsu kenan.
Kunya tamkar Mahnoor zata shige cikin ƙasa, ta yi ƙasa da kai kamar ba zata sake ɗagowa ba, sai dai da yake tana san Jaish, zuciyarta ruwan madarar albarka take kwaranyawa momma da ta jajirce a kansu.

Momma kuwa, da bata ji kunyar komai ba har da cewa. "Zan yi magana da shi, kuma a daren yau, zan kira shi in sanar mashi da matsayinki a wajensa da kai'na, zan tayaki da yi mashi nasiha, daga karshe zan ce ya kama hannunki ku tafi part ɗinsa, ba zai yi mun musu ba, dan bai taɓa yi ba, tabbas zai karɓe ki idan na buƙaci hakan, amma ni da ke mun san ba dan ransa ya so zai yi hakan ba, dan haka ya rage naki sauran aiki, in kina san ransa ya so kuna shiga part ɗinku ki yi wanka a toilet ɗinsa, kada ki matsa ko nan da can, ki sanya ɗaya daga cikin kayan da zansa mama Haulat ta baki anjuma, ki shirya ki haye bed ɗinsa ki kwanta,kada ki damu da sai ya kulaki ya yi maki magana a daren, kada fa ki rusa mana shiri, kuma kada ki damu da dik abin da zai ce maki dan kin kwanta a bed ɗinsa, in kin kwanta ki yi gaggauwar rufe idanu dan ma ya zaci barci kike yi, tabbas ina da yakinin zai dawo gareki".
Chapter 102 · 0% Book details