← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 231 OF 242

Sashe 231

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TO! Ina mai farincikin sanar da ku cewa book ɗina mai suna MACE MAI DARAJACE, zai saukan maku da zafizafinsa very soon, wannan book ɗin na yisa ne kawai dan matan aure da kuma waɗan da suke gab da yin aure, ko zawarawa wanda ba aure zasu yi ba ban yarda su karanta mun littafi ba, ba novel bane, littafi ne da dan ma'aurata na yi shi, na jima ina tsara shi ina kuma tattara dik wasu muhimman abubuwa a cikinsa, book ne da ya haɗa komai da komai na rayuwar aure da sauransu, kada wata budurwa ta buɗe mun book tam!!! 2k yake, akwai sirrika kala daban daban a cikinsa, akwai kayan gyare gyaren abubuwa daban daban, kai baki ba zai iya faɗar abin dake cikin book ɗin nan ba, in kina buƙata kai tsaye ki mun magana, amma ba yanzu zan sake shi ba, saura kaɗan, idan na tashi sakansa zan sanar da ku!!. Amma dik mai so tin yanzu ta mun magana in san da ita, an zuba abubuwa a ciki, akwai salo kala kala sai wanda ya karanta zai gane, bana san buɗe me a ciki saboda kada na baku satar amsa, amma fa akwai abubuwa a ciki ba karya!!. IN SHA ALLAH RAYUWARKI ZATA CANZA KAMAR HAKA IDAN KIKA SAMU DAMAR MALLAKAR WANNAN LITTAFI KUMA KIKA YI AMFANI DA ABIN DAKE A CIKI!.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥=========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

60

Auta da guyson kuwa a tare suka yi lunch ɗinsu, Auta taki ci da farko, sai da guyson ya yi ta lallaɓata sannan ne ta ci.

Shi kuwa Ramish yana yin parking motarsa a parking lot na h-c É—insu kan kace me wasu jiga jigan jami'ai sun kewaye motar, sosai Leesharh ta tsorata daga ciki, dan a tinaninta tin da taki tayasa aiki shi ne ya kawota su lallasata irin na wancan karan!. Zuba mashi idanu ta yi tana kallan yadda ya É—aure fuska tamau tamkar hadari, abin sai ya yi mugun bata tsoro.

Buɗe mashi door ɗin aka yi, ba tare da ya sake kallan in da take ba ya fito waje abinsa. Shiru ta yi a ranta tana tinanin ya zata yi? Sai gani ta yi an buɗe mata door na side ɗinta, kallon jami'in da ya buɗe mata ɗin ta yi, wani shirgegen balarabe ne mai tsawo da cikar halitta. Fitowa ta yi jiki ba kwari, tinanin irin azaban da jami'an nan suka bata a farkon karonta da su ne kawai ya faɗo mata a rai, tin da ta zo duniya bata taɓa shan azaba irin wanda suka gana mata ba, a lokacin har ji ta yi da sun bata wata dama kaɗan tsab zata kashe kanta ta huta!.

Ta yi nisa a cikin tinaninta sai ji ta yi anja hannunta, almost 3 times yanayi mata magana bata ji shi ba, shi ne yasa ya kama hannunta kawai. Zaro idanu ta yi tana kallonsa tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, da ta san nan zai zo ba zata rakosa ba. Binsa kawai take yi tana karanta lailahaillah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, gabaɗaya jikinta kerma yake yi. Ya lura da ta tsorata sosai, hakan yasa ya yi ƙasa da murya sosai wajen cewa. "Aesh babu abin da za su yi maki fa, a yanzu wannan zuwan na daban ne, ba irin wanda kika yi a baya bane!".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa mashi da to, manya-manyan jami'ai guda shidda ne suke take masu baya har izuwa cikin office É—insa. Already mai zane yana zaune yana jiransu. Saman wani lallausan seat ya ce mata ta zauna. Ba musu ta zauna tana kallon office É—in, É—auko mashi wata chair dake kusa da table É—insa yasa aka yi aka kawo mashi kusa da ita, zama ya yi suna fuskantar juna, sannan ne ya ce. "Ki faÉ—a mashi fuskokin waÉ—an da kika sani daga cikinsu, dan gabaÉ—aya waÉ—an da kika ambata na bincikasu a gidan Abbie babu su".

In baku manta ba dattijuwa tasa sun ɓoye shaidar da za'a iya kamasu da shi, so ya bincika bai iya kamasu ba, dan haka dole su kasance suna da zanensu. Ganaɗaya jami'ansa tsayuwa suka yi a bayansa suka binta da kallo suna jiran ta fara zayyano bayanai. Lokaci guda ya ji hakan ya kona mashi rai, a ɗan dakile ya ce da jami'an dik su fice mashi daga office, dan bai ga amfanin su tsaya suna kalle mashi ita ba, shi kaɗai zai ganta kuma ya ga zanen da za'a zana.

Abin har murmushi yaso ya sakata, sai ta danne tare da cewa. "Yah Ramish ina tsoro sosai". ......... Hannunsa ya miƙa ya riƙo nata, cikin natsuwa ya ce. "Babu abin da zai faru kin ji? Please ki daure". Jinjina mashi kai ta yi tare da juyo da kallonta a kan mai zanen, cikin natsuwa ta fara bashi bayanan yadda suke a zahirance. Zanasu ya fara yi har da face mask na fuskokinsu, tana cigaba da yi mashi bayani yadda yakamata har suka kammala, bata yi kuskure ba sam sam, zanen ya fita sosai.

Ana kammalawa kallo ɗaya Ramish ya yi wa zanen ya gano su wanenen daga cikin securitys ɗinsu, ya girgiza sosai da ganinsu, zubawa hoton zanen idanu ya yi yana kara tambayarta ta tabbata sune babu kuskure, kai ta gyaɗa mashi alamar ta tabbata. Nisawa ya yi kafin ya karɓi zanen, sannan ya cewa mai zanen ya haɗa kayansa ya je, already dama ya biyasa hakkinsa.

Mai zanen yana fita Leesharh ta matsa kusa da shi. "Yah Ramish akwai abin da nike san faÉ—a maka fa, ko in ce akwai abin da nike san baka, amma dan Allah idan na baka kada ka tambayeni daga ina na samu ka ji?". Dawo da kallonsa tsam a kanta ya yi. "In Sha ALLAH ba zan tambaya ba". Ya faÉ—a yana sake riko hannunta cikin nasa.

Wayarta ta fitar daga aljihun rigarta da ɗayar hannunta, kai tsaye ta shiga picks, hotunan da ta ɗauka a ɗazun bedroom na dattijuwa ta fitar, miƙa mashi wayar ta yi tana faɗin. "Dik waɗan nan suna da sa hannun a abubuwan da suke faru, and ka nemosu zaka samu dik abin da kake so daga bakunansu".

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a ransa ya furta alhamdulillah almost 3 times, kai amma ya ji matuƙar daɗi, koba komai yanzu ya sami wasu da face ɗinsu yake a buɗe, a gaskiya Leesharh ta taimaka mashi, ya kuma ji daɗi, dole su nemo waɗan nan fuskokin.

Cigaba ya yi da duba hotunan a tinaninsa zai ga wasu, sai kawai ya fara ganin hotunansa kala daban daban a cikin wayar, dik kuma bai sani ba ta yi ta ɗaukarsa, sun yi fitina hotunan ba kaɗan ba, saboda yadda ta ɗaukesu bai sani ba, kun san hoto idan baka sani ba aka ɗauketa wlh ya fi kyau, ba karamun daɗi ya ji ba, ɗago idanu ya yi ya kallenta, while ita ma shi take kallo. Suna haɗa ido ta yi gaggawar sunkuyar da kanta ƙasa. Matsar da kujerarsa dab da ita sosai ya yi tare da ɗaura hannunsa a saman shoulder ɗinta, ya kashe masu selfish mai bala'in kyau, murmushi ne ya subce mata tasa tafukan hannayenta ta rufe face ɗinta tana yin ƙasa da kai!.

"Waye ya ce a saci mun hotunana ba tare da izinina ba?!". Ya faɗa yana janyota jikinsa. "Kai Yah Ramish ni da hotunan yayana kuma ka ce meyasa na sata? Yayana ne fa!". Ta faɗa tana cigaba da rufe fuska. Haɓarta ya ɗago. "Ni ban yarda da wannan wayan ba, kawai a bani amsar me ake yi da hotona". Ya kai karshen maganar tare da matsar da bakinsa saitin kunnuwanta. "Ko dan kinga kyakkyawan guy yaron mamarsa shi ne kika kyatsa kika kware mun e ƴan'mata?".

ÆŠan turo baki ta yi. "Ni ba wani kyatsawar da na yi". "Da gaske?". Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e. "To me kike yi da hotunana? FaÉ—a mun in ji!". "Ni babu abin da nike yi da su". Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Masu sunanki suna mai daraja basa karya fa, faÉ—a mun gaskiyar me kike yi da su?!". Kara rufe face É—inta da kyau sosai ta yi kafin ta ce. "Zuwa dare zan faÉ—a maka, amma yanzu please ka barci". ÆŠan lumshe idanu ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Mu je gida ko mu je yawo?".

Shiru ta É—an yi, can sai ta ce. "Yah Ramish yaushe zaka kai ni gidan Abbie in ga Æ´ar uwata?". Take mood É—insa ta É—an canza, alamar bai ji daÉ—in maganar bama, amma sai ya ce. "Ba yanzu ba, sai mun kammala binciken da muke yi, zuwanki gidan a yanzu babban haÉ—ari ne sosai". Da zata ce ya kaita a yanzu, amma ganin ya nuna alamar rashin jin daÉ—i yasa ta hakura, sai ta ce su wuce gida kawai dan tana san kasancewa da guyson and Auta. Bai musa mata ba ya É—auketa suka wuce wajen cin abinci mai kyau da tsada game da tsaro, daga haka suka wuce gida ya mayar da ita ya sake dawowa h-c É—insu dan su cigaba da bincike a kan wannan zane da ta basu game da hotunan waÉ—an can fuskokin!.

🔥🔥🔥🔥JIMETA🔥🔥🔥🔥

Ai tijara Nenne ta tsayar masu a kan ko sama zata haÉ—e da kasa yau sai bappa ya fitar mata da Mahreen, idan kuma ba haka ba zai ga jajjagen bala'i, banza da ita ya yi tare da wucewa ya shiga cikin gida abinsa, ransa fes tin da Mahnoor dai ta koma ga mijinta, yanzu damuwarsa a nan shi ne kewarsu da ya addaba mashi.
Chapter 231 · 0% Book details