← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 242

Sashe 111

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayansa ta bi da sauri dan ta ga wanenen? Tana da karfin hali ita ma, a ranta take rayawa lallai lokacin barinsu gidan nan ya yi tun da dai maza ne suke shigo masu É—aki da daddare.

Da sauri ta fito daga bedroom É—in nasu ta nufi bin bayansa. Sai dai ko da ta fito bata gansa ba, babu shi babu alamarsa, É—an waige waige ta tsaya yi a wajen, kamar dai a mafarki ta hango inuwar mutum ta wajen wannan kofa da Guyson ya bi ranar ya je wajen dinner Jawad, kun tuna ranar da ya haÉ—u da aljanar nan? Kun san ai dama ta part É—in mama ne kofar yake ko idan baku manta ba? To ita kuma Zee kunga a part É—in take tare da Aneesa, so tana fitowa sai taga inuwar mutum kamar dai yadda aka yi wa guyson.

Ɗan tsorata ta yi, sai kuma ta tina abin da mamarsu take yawan faɗa masu a kan kada su ji tsoron kowa face Allah da ya haliccesu. Tuna hakan yasa ta ce bari ta je ta leƙa kila inuwar wanda ya shigo masu ɗaki ne, yau so take taga wanenen?. Ba tare da tina abin da zata iya gani ba ta nufi kofar, tana taɓa kofar kuma sai ta jita a buɗe.

Wai nace ba, meyasa wannan kofar a dik lokacin da wannan inuwa ta gifta kofar yake buÉ—e kansa da kansa ne? Kun san fa ba'a buÉ—e wannan kofa kwata kwata, ko da rana a rufe yake, so meyasa in dai inuwa ta gifta kofar zai buÉ—e? Muje dai zuwa.

Jan kofar a hankali Zee ta yi da nufin ta fita waje, daga bayanta ta ji muryarsa ya ce. "Ina zaki je a daren nan, sannan kofar nan ai ba'a buÉ—eta". A hanzarce ta juyo da kallonta a kansa, uncle Jahiz É—in ne dai, yana tsaye yana kallanta.

Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin juyo da jikinta a garesa dan ta bashi amsa ta wuce ciki, unexpext idanunta suka kallo mata fuskar mace mai kama da aljana ga wasu kahohhuna dogaye a hancinta har zuwa bakinta, jini na bin jikin kahon, sannan idanunta manya manyan jajir kamar wuta, gwanin ban tsoro.

Ai Zee bata san time É—in da ta zunduma wani irin ihu mai doÉ—e kunne ba, kwata kwata bama ta san ya akayi ba sai ganin kanta ta yi a kirjin uncle Jahiz, shi kuma fa babu abin da ya gani, ita kaÉ—ai aka tsorata, kada ku manta uncle Jahiz fa na Aliyah ce, Aliyah kanwar Mammie shugaban mashirikai ita mammie ta ce zata auresa in baku manta ba, to ni dai ina ga kila saboda uncle Jahiz ya nuna ra'ayinsa a kan Zee yasa Mammie ta fara É—aukar mataki, amma ku ya kuke gani?.

Kankame shi ta yi tana ihu. Gudun kada ta tashi family yasa uncle Jahiz ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa yana kai kallansa a wajen da ta baro take ihun. Shi dai bai ga komai ba face kofa kawai, to meyasakata ihu har haka? Ya jefawa kansa tambaya.

Motsi ya ji a bayansu ta wajen part ɗin momma, hakan yasa ya yi saurin janta baya dan ma kada wani ya gansu, ganin kamar razana sosai ta yi yasa ya fara tofa mata addu'oi har lokacin bai zame hannunsa daga bakinta ba. Ita kuma tana ƙanƙame da shi.

Addu'oin da yake tofa mata ne yasa ta fara samun nitsuwa hankalinta yana dawowa jikinta, tsoratar da ta yi yasa har ta fita a hayyacinta.

Ganin ta É—an fara nitsuwa yasa ya jata suka karisa shiga bedroom É—in Aneesa, a saman sofa ya zaunar da ita tare da zame hannunsa daga bakinta, ya kurawa face É—inta idanu yana kallanta. Ta É—an É—auki lokaci a haka kafin ta iya dawowa dai'dai, hankali a tashe take kallansa, sai kuma ta kasa yin magana.

Cikin nitsuwa ya tambayeta dalilin ihun da ta yi, ta kasa bashi amsa, tamkar an ɗaure mata tongue ɗinta, ganin hakan yasa ya ce ta je ta kwanta da safe zasu yi magana kuma kada ta sake fitowa. Ba musu ta miƙe ta isa bakin bed ɗinsu, hayewa ta yi ta kwanta har wa lokacin tongue ɗinta a ɗaure ta kasa iya yin magana.

Miƙewa ya yi ya koma kusa da ita, addu'oi sosai ya tofa mata, tin tana satar kallan face ɗinsa har ta lumshe idanu tana sauke ajiyar zuciya alamar hankalinta ya kwanta. Jin saukar ajiyar zuciyarta yasa ya fahimci ta samu natsuwa, bargo ya ja ya lulluɓeta tare da karisawa gaban switch ya kashe masu wutar, sannan ya fita ya janyo kofar ya rufe masu.

Dik wannan bidiri da ake yi Aneesa tana can duniyar mafarkin ita da Yah Rizwan, bata farka ba, amma abin mamaki kuma zata iya wayan gari ta bada labarin abin da ya faru daren jiya É—in, anya Aneesa mutum ce kuwa? Ta fara bani tsoro sosai gaskiya, amma mu je zuwa, ita ma labari zai biyo ta kanta ne, lokacin na nan tafe.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A tare Jawad and Jaish suka jera har izuwa takiyar main parlour, a nan ne suka rungumi juna tare da yi wa juna good night, a daidai lokacin Chuchu da Mahnoor suka iso wajen.

Wucewa gaba Jaish ya yi ya nufi part É—insa ba tare da ya kalli in da Mahnoor take ba, shi kuma Jawad ya rike hannun Chuchu yana janyota jikinsa suka wuce nasu part É—in suna yi wa Mahnoor good night.

Shiru ta É—an tsaya a wajen tana tinanin yadda zata kwana da shi É—aki É—aya yau. Ganin tsayuwa ba zai haifar mata da mafita bane yasa a nitse ta taka ta bi bayansa.

Tana sako kafafunta a cikin parlonsa ta ji kamshi na daban ba kamar wanda ta ji da rana ba, kenan ancanza mashi perfume, shakar kamshin ta yi ta lumshe idanunta, cikin natsuwa ta ƙarisa shiga cikin parlourn.

Mama Haulat ta isko zaune saman sofa tana dudduba wasu sexy sleeping dress dake cikin kwalayensu. Cikin girmamawa ta ce. "Barka da dare mama Haulat".

Fuska É—auke da fara'a mama Haulat ta amsa da. "Yauwa barka dai amarya kuma sarauniyarmu, zo nan ki É—auki kayanki ki wuce É—akin mijinki". ÆŠan siririn murmushi ta saki kafin ta karisa kusa da mama Haulat, sannan ta ce. "Mama kaya kuma?".

Jinjina kai ta yi tare da amsa mata. "E kaya, momma ce ta ce abaki wannan kayan su zaki saka, kuma ta ce karfe tara kije ki ɗaukawa mijin naki cappuccino". Kasa da kai Mahnoor ta yi alamar ta ji kunya ance mijinta. Miƙo mata kayan mama Haulat ta yi ta karɓa tana wani sunkuyar da kanta ƙasa.

"Kada ki nuna jin kunya a wannan ɓangaren, domin kunya bata da wani amfani, ki tsaya tsayin daka ki faranta ran mijinki shi ne dai'dai, ki sani yanzu kin shiga layin da Mala'iku zasu yi rubutu a kanki a kan aure, so yana da kyau ki kula sosai, ki sanya shi farinciki domin ki samu rahamar Allah, na ɗaukeki ne tamkar yata, dan haka a matsayina na uwa shawarata a gareki shi ne ki ajiye wannan kunya a gefe"

Ƙasa ta yi da kanta wajen amsa cewa ta gode sosai kuma In Sha Allah zata yi amfani da shawarinsu ita da momma, fatan alkhairi da fatan nasara mama Haulat ta yi mata sannan ta ɗaura da cewa sai da safe.

Bedroom É—in ta nufa cikin natsuwa. Baki É—auke da sallama ta shiga ciki, babu kowa a É—akin sai tashin daddaÉ—ar kamshi da yake. Shiru ta tsaya tana bin ko'ina da kallo, tinani ta shiga yi a kan ina yake ne? Ko dai bai shigo É—akin ba ne?. Ta kai almost 5 mins a É—aya a wajen kafin ta iya fahimtar yana toilet yana wanka ne.

A hankali ta taka ta ƙarisa cikin ɗakin, zata zauna a ƙasa sai ta tuna kaman momma da mama Haulat, momma ta ce ta mayar da gadansa wajen zamanta kamar yadda zata mayar da jikinsa gadanta. Tina hakan yasa ta ƙarisa bakin bed ɗin nasa a hankali ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.

Shiru ta yi tana bin ɗakin da kallo tana ɗan shafa kwalin kayan dake ƙasar hannunta, bata ga lokacin da ya fito daga wanka ya shiga dressing room ba, amma shi ya ganta a cikin dakin, sai ya kawar da kansa kamar bai ganta ba.

After some minutes ya fito sanye da kayan barcisa masu kyau da tsada, kao tsaye bed É—insa ya nufo, sai da ya matso kusa da ita ne ta iya gane ya fito, a cikin hanzarce ta É—ago da kallanta a kansa. Unexpectly suka yio four eyes, domin kuwa shi ma ita yake kallah yana jin kamar ya je ya É—auki lallen hannunta hoto.

Kwayar idanunsa ne suka rikitar da ita, a ruɗe ta miƙe daga saman bed ɗin, tsabar ta tsorata har ta ce mashi ina kwana ba tare da ta sam t faɗa ba. Kawar da kallansa daga kanta ya yi ya haye saman bed ɗinsa ba tare da ya amsa mata ba. Lokacin guda ta ji jikinta ya mutu na banza da ita da ya yi, sai ya tsaya kamar wata doluwa.

GabaÉ—aya ta ji ta karaya da wannan al'amari, sai dai lokaci guda zancen momma ya dawo ranta a in da take ce mata kada ta karaya, ta jajirce kome zai yi mata, tina hanan yasa ta ji kwarin gwiwa ya dawo mata, a hankali ta fara takawa ta nufi toilet É—insa dan ta yi wanka.
Chapter 111 · 0% Book details