← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 237 OF 242

Sashe 237

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune Auta take a saman bed É—inta ta yi shiru tana tinanin rayuwa, wasa wasa yau ta shafi almost 3 month ba tare da Hoorain ko jin sautin muryarsa ba, abin har ya fara zame mata jiki, yanzu ta fara yarda da Hoorain baya duniya, Leesharh tana bedroom É—inta tana wanka, guyson ya koma kingdom of power saboda an buÉ—e school, dole ya koma.

Ramish baya nan ya fita, a yanzu ya yi nasarar capke mutane kaso 60 cikin ɗari na masu nikaf, sai dai dik wanda ya kama sun ki faɗa mashi wanenen mai turosu, ya azabtar da su har ya gaji, amma sun ki faɗa, sun ce su haya killers ne, idan sun karɓi contract ko kashesu za'ayi alkawari suke ɗauka basa taɓa tona asirin wanda ya sanyasu aiki, sannan su idan suka karɓi aiki fa ko mutum me zai yi sai sun kashe shi, ko duniya dikka zai basu idan sun karɓi aiki a kansa sai sun ƙaddamar.

Ba karamun ɓacin rai Ramish ya ji ba, ya sanar da Smart ga abin da yake faru, Smart ya ce mashi kada ya damu ya kashesu gabaɗaya a rage mugun iri a cikin al'umma, kuma idan ya kashesu kada ya sake saka hannunsa a neman wanda ya sakasu, ya bar mashi aikin dan matsalar daga cikin gida ta samo asali, wanda ya sakasu yana cikin kingdom of power, su kansu basu san ainahin wanda ya sakasu ba, dan haka ya bar binciken shi zai kama koma wanenen a nan, saura kaɗan ya tattara dik wasu hojjijinsa ya tinkaresu gadan gadan! Wannan ne ma dalilin zamansa a kingdom of power bai koma Paris ba, shi ne kuka ga ya yi shiru kamar babu abin da yake yi, uhm babban ɓarna yake yi masu ta karkashin kasa ba tare da sun sani ba,. BALA'IN CAN, WANDA YA SANYASU KUMA YANA KINGDOM OF POWER?! HOW TO?! KUMA WHO?. UHM AKWAI ABUBUWA FA!!.

Ba kara mun shocked Ramish ya ji ba a lokacin da ya ji abin da yayan nasa ya ce, ya so ya faɗa mashi wani abin da zai kwantar mashi da hankali yasa ya ji sanyi a ransa, amma ina sai ma kara mashi zafin da ya yi ta hanyar cewa kada ya kuskura ya sake zuwa gidan King Badeen, dan baya son kowa ya zargi wani abin, sannan shi Smart ɗin a zuwansa wancan karon da ya kawo Auta basu yi rabuwar daɗi da kakan nasa ba, ya yi masu tas bai ragawa kowa ba, ya kuma ce masu in dai kannensa basu auri waɗan da suke so ba to su ce shi ba jinin King Zuhair bane!!! Har da ce masu ya yi ya yi masu alkawarin Zunaira zata rayu ne kawai da abin sonta, ba zata zauna da Abdussalam ba! Sannan kuma Ramish ma yana da wacce yake so, kuma bare ce, yaga wanda zai hanasu zama ma'aurata tun da su babu abin da suka iya sai son kai, to shi kuma zai gwada masu a cikin Rahilarh ya haifu, ba su yi rabuwar daɗi ba dai, dan King Badeen ya nuna kafewarsa a kan babu auren bare a cikin zuri'arsa, dik gida zasu dawo su yi aure, har da cewa shi ma Smart ɗin ya dawo gida ya zaɓi mata! Shi kuwa ya ce zai gwada masu shi ɗan yau ne. DA ALAMA SHIYASA YA AURI PRETTY DAN YA GWADA MASU SHI MA YA AURI BARE, KAI SMART ƊAN DUNIYA NE WLH!!

Wannan dalilin yasa ya ce wa Ramish ɗin kada ya kuskura ya je gidan King Badeen, dan yana zuwa zasu kama shi su yi mashi auren gida ne tin da Smart ya ce yana da bare wacce yake so, sannan yasa Ramish ɗin ya cire sim ɗinsa ya ajiye a ƙasa, yanzu yakin ya koma na cikin gida, bari a saita na cikin gida tukun nan, dama kun san idan kana son yin gyara to ka faro daga cikin gida, a nan ne zaka iya cin nasara, amma idan ka faro daga waje, kana gyara a cikin gida ana warware maka komai!.

To kun ji abin da ya faru a zuwan Smart gidan kakan nasu, a lokacin Momma tana gidan uncle Rahab abin ya faru, da ta dawo baban nata bai sanar da ita ga abin da yake faruwa ba, sai ya kira King Zuhair ya sanar mashi, nan King Zuhair yake sanar da shi cewa shi ma Smart bai barsa ba, ya fi karfinsa, abin da yagadama kawai yaron nan yake yi, nan fa ran King Badeen ya kara ɓaci ya kira uncle Muhammad wato daddyn Smart na Paris, dan shi kaɗai kawai a duniya Smart yake jin maganarsa bayan Momma.

Sosai King Badeen ya yi wa uncle Muhammad faÉ—a a kan irin tarbiyar da ya bawa Smart, yaro kwata kwata baya ganin girman manya, sannan baya da tsoro, dik wata barazana a banza!. Hakuri uncle Muhammad ya shiga bashi kafin ya ce bari ya kira Smart É—in. Da ya kirasa sai dai a maimakon ya yi mashi faÉ—a sai ya ce. "Son me kaje kake yi wa tsoffin nan ka tunzurasu har haka ne? Daddynka ya kirani last week, yau kuma kakanku ya kirani, ka je kana goda masu iko ko? Kasan fa su sarauta ne, babu mai nuna iko a gabansu".

Kai tsaye ya amsa da. "Daddy tsoffin ne basa a kan hanyar da ta dace shiyasa nike mayar da su kan hanya, kasan ba zan yi abu mara kyau ba ai ko my lovely dad?". Kamar mai shagwaɓa haka ya yi maganar, ALLAH ya gani yana kaunar daddynsa over.

Murmushi daddyn nasa ya yi. "That's my son, nasan gyara kake yi shiyasa ma da daddynka ya kirani ban kiraka ba, dik yadda aka yi nasan basu aikata dai'dai, cigaba da dawo da su kan hanya my son, zan yi alfahari da kai, amma ka yi sauri ka dawo ka ji? Ina kewarka over"...... Da okey kawai ya amsa tare da cewa i love you dad, love you too shi ma ya ce, daga haka suka yi sallama. NA CE YANZU KUN GANE MAI KARA SANGARTAR DA SMART KO? KUN JI UNCLE MUHAMMAD WAI YA CIGABA DA DAWO DA SU HANYA, KAI WATO ALLAH KA BARMU DA IYAYENMU!!.

---------------------------------------🔥🔥🔥

Baki a ɗauke da sallama dattijuwar nan ta shigo room na Auta, irin dogayen rigunar shan iskan nan ne a jikin Auta ɗin, rigar tana da ɗan siririn hannu, while a dai'dai gwiwarta ta tsaya mata, tana gajin dattijuwar ta yi gaggawar saukowa ƙasa daga saman bed ɗinta ta nufeta da sauri, kwandon mai shake da kayan fruits dake hannunta Autar ta karɓa tana faɗin. "Mama ai da baki wahalar da kanki ba, sai in zo in ɗauka da kai'na". Ta yi maganar tana kallon kayan fruits ɗin kafin ta ɗago da kallanta a kan tsohuwar, yau shi ne kallonta na farko da fuskar dattijuwar.

Wani irin faÉ—uwar gaba ta ji dan taga wannan kamar ba tsohuwar gaske bace, kada ku manta yaran Momma they're gifted!. Amma sai ta kawar da tinanin nata tare da juyawa ta koma wajen bed É—inta, a saman bedside drawer ta É—aura kwandon tana cigaba da kallon dattijuwa ta kasan ido, juyawa ta yi tana tafiya har da É—an É—ingisawa irin na tsoffi............... Yanzu Fisabilillah my people's ku faÉ—a mun mutum mai irin zuciyar Auta meyasa zaka so kasheta? Yarinyar da babu ruwanta, bata da girman kai, ga girmama manya, bata duba da talaucinsu ko aiki a karkashinsu da suke yi, da zarar mutum ya girmeta zata bashi girma koma wanene!.

Komawa saman bed É—inta ta yi ta zauna tare da É—auko wayarta tana duba sakon mutuminta, dan koba komai a yanzu kalamansa suka sanyata farinciki, tana samun annashuwa. ..............Wai ina mijinta Abdussalam ne? Allah sarki ya dawo Dubai, dan a tinaninsa ta mutu, har ya cire rai da ita, sai dai kuma har yau har gobe sonta yana a cikin zuciyarsa, kullum sai ya yi mata addu'ar samun rahama, ita kuwa tana nan ta mance da wani Abdussalam, dan Smart ya ce mata kada ta damu Abdussalam ya saketa, yanzu ita ba matar kowa bace, so dan haka ta mance da wani Abdussalam ta fara sabuwar rayuwa!. Amma fa dan ta yi farinciki Smart ya faÉ—a mata haka, ba wai dan Abdussalam É—in ya saketa ba!!!.

Ɗan siririn murmushin da tsawon watanni bai samu gurbi a face ɗinta bane ya bayyana a fuskarta a lokacin da take karanta saƙon guy ɗin can, hannu ta miƙa ta ɗauki apple a cikin kwadon fruits da dattijuwa ta kawo mata, wato tana shan fruits tana karanta saƙonsa abin zai fi sugar. Bakinta kai tsaye ta kai apple ɗin zata gatsa kenan unexpected taga harbi da kifiya an harbi apple ɗin hannun nata ya faɗi ƙasa tare da kifiyar. Zabura ta yi ta miƙe tsaye tare da gefar da wayar hannunta dan ta tsorata sosai.

Cikin natsuwa ya tako izuwa cikin ɗakin, sanye yake da security uniform, wlh kayan sun yi bala'in yi mashi kyau matuƙa, tamkar dam shi aka yi, uniform ɗin su Smart ne, ƙasa ya yi da kansa cikin girmamawa ya ce. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe, ban yarda da inganci apple ɗin bane shiyasa na dakatar dake daga sha, sannan a doka sai na bincike abinci kafin ki ci, ban bincike bane shiyasa na hanaki ci!". Da kyar ya iya kai karshen maganar saboda yadda words ɗinsa suke sarkewa, da alama hakan yana da nasaba da yanayin shigarta, ɗaya ne daga cikin jami'an dake kula da lafiyarta, mai kawo masu abinci ne!. Ya kai karshen maganar tare da mayar da kwari da bakarsa ya maƙala a bayansa kamar wani warriors!.

A wani irin slow ta ɗago idanunta ta sauke a kansu. Murya tamkar a mafarki ta ce. "Ina ainahin mai kawo mana abinci?". Nisawa ya yi, har yanzu kaifin ƙwaƙwalwarta yana nan bai ragu ba, dik da ciwon da ta sha, tsawon wata uku tana jinya, amma babu abin da ya sauya!.
Chapter 237 · 0% Book details