← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 242

Sashe 79

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma sai kuma ya tina in har bai É—auki wannan call É—in ba to Ramish zai fita nemansa ne, saboda sun san dik abin da ya sha kansu basa wuce miss calls biyu ma junasu ba tare da sun yi picking ba, shirunsu basu yi picking ba hakan na nuna suna cikin matsala kenan, kunga dole ya fita nemansa.

Hakan yasa ya ɗauki call ɗin tare da kara wayar a kunnensa yana seseta nitsuwarsa. Daga ɗayar ɓangaren Ramish ya yi cikakken sallama. Amsawa ya yi idanunsa a kanta, ita ma shi take bi da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa.

"Ina kake Bilal?". Ramish ya jefa mashi tambaya.

Shiru ya É—an yi yana tinanin abin faÉ—e, basu saba yin karya ba, hakan ya ja ya rasa abin faÉ—e.
"Ina zuwa gida yanzu". Ya faÉ—a yana san katse kiran.

Katse shi Ramish ya yi da cewa. "Ka faÉ—a mun in da kake in zo in sameka yanzu". A hanzarce ya ce. "A'a ba sai ka zo ba, ina hanyar gida yanzu".

Shiru Ramish ya É—an yi, can kuma sai ya ce. "Ka dai san bana magana biyu ko?". Jinjina kai Bilal ya yi alamar e tamkar yana gabansa haÉ—e da cewa e haka ne.

"To ina kake zanzo yanzu".

Zaro idanu Bilal ya yi, sai ya ji kamar an kwaÉ—a mashi guduma a kansa, hankalinsa ne ya tashi, Ramish ya zo ya samesa a nan ai ya shiga uku, me zai ce mashi ya rabu da shi kenan?.

Zare wayar daga kunnensa ya yi, ba tare da ya sake yi wa Ramish magana ba ya yi saurin katse kiran, a hanzarce ya tashi motar.

"Yah Bilal lafiya?". Ta jefa mashi tambayar tana kallan wayar dake hannunsa.

"Sauke nikaf naki, sorry ba zamu iya tsayawa sayen ice cream ba, gida kai tsaye zamu wuce, gobe muna da taro, idan mun taso daga taron zan saya maki ice cream É—in in kawo maki". Ya kai karshen maganar tare da kunne mota.

Da gudun gaske ya figi motar tamkar zai tashi sama, har sai da ya bata tsoro.

A can gida kuwa. Ramish yana tsaye a parlournsu, daga shi sai sexy short, babu riga a jikinsa sai white singlet mai kyan gaske, yana tsaye a jikin windownsu dake fuskantar harabar gidan, hannunsa rike da cup and his phone.

Shi ma Ramish yana da zanen letter R a damtse hannunsa da ya zana kamar yadda Bilal ya yi zanen B a wuyarsa, yanayinsa ta nuna yana cikin damuwa sosai, saboda abubuwa sun sha kansa matuƙa, ga shi gobe zasu yi wannan taro da yake sa ran kafin taro ya kama masu nikaf kenan, sai dai har yanzu bai samu wata makama da zai iya kamasu da ita ba, babu ma wanu abin zargi da suka bar mashi, abin dai ya sha gaban tinani, dik yadda aka yi su ma shegu ne.

Ya yi shiru yana kallan harabar gidansu kamar mai tinanin wani abin, bawan Allah damuwa ta yi mashi yawa, bai san ya taron gobe zata kasance ba.

Ba tare da ya juyo ba, cikin nitsuwa ya ce. "Daga ina kake a cikin wannan dare bayan kasan halin da muke ciki?"............ Kamar wani aljani, ko yaushe ya ji yo takun sahun Bilal?.

Bilal da ya shigo yanzu ne ya É—an fara kame kame kamar wani maras gaskiya, dama kamar yasan zai sami Ramish a wajen yasa ya shiga parking space É—insu ta kofar baya ba tare da kowa ya gansa ba, dik dan gujewa Æ´an gidan kada su gansa.

"Meyasa kaki yarda in zo in sameka a in da kake? And meyasa ka katse kirana ba tare da mun gama magana ba?". Ramish ya sake jefa mashi tambaya a karo na biyu ba tare da ya jira ya amsa ta farko ba.

Shiru ya kasa amsawa, dan bai san me zai ce mashi ba, ga shi dik in da suke zuwa dama a tare suke tafiya bare ya yi mashi wani karya.

A hankali Ramish ya juyo garesa, wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce.
"Me kake ɓoye mun my love". Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallan tuhuma, dan yanzu zuciyarsa ta rigata da kai point ɗin da ba zai iya ɓoye zargin da ya jima yake yi ba, ya daɗe sosai zuciyarsa tana ɗarsa mashi zargi a kan Bilal na ɓoye mashi wani abin, amma a koda yaushe ƙoƙarin kawar da wannan zargi yake yi domin yaga ya kori shaiɗan dake san rabashi da ɗan uwansa ya haɗasu faɗa.

"What do you think that I'm hiding for you?". A ɗan razane ya yi maganar, alamar kamar dai da gaske akwai wata a ƙasa.
"Ka fini sani Bilal, ka fini sanin abin da kake ɓoyewa". "Wai Yah Ramish lafiyarka yau kuwa? Shin na taɓa ɓoye maka wani abin ne? Tin tasowata har zuwa yau ba a tare muke yin komai ba?..........."

Cikin zafa da kunan rai ya ce. "Banda wannan lokacin Bilal, tin da muka taso tare muke yin komai amma banda yanzu!". Yadda ya yi maganar da alama ransa ya fara ɓaci, zuciyarsa ta fara raunata sosai, dan da alamar zarginsa tana san tabbata, idan kuma abin da yake zargi ta tabbata da gaske, magana ta domin Allah zai iya rasa ransa, saboda kowa yasan bayan iyayensa babu wanda yake kauna biyun Bilal, yana sansa kamar ransa, dole zuciya ta buga idan kuwa haka ne.

"Yah Ramish why are you talking like that? Talking out of control, and you're shouting like mad............".

Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata cak sakamakon wani irin tsawa da Ramish ya daka mashi a kan ya yi mashi shiru.

Taku biyu ya yi ya matsa gabansa, dama tin da ya fara bincike a kan masu nikaf Bilal ya zare hannunsa yaki taimaka masa, tare suke yin komai, amma a wannan karon Bilal yaki tayasa, hakan yasa zarginsa a kansa ya karu, sannan ga fita da Bilal ɗin yake yi shi kaɗai a yanzu, idan baku manta ba a ranar da Ummie ta je ɗakin Ramish nace maku Bilal baya nan, ya fita ko?. To kun ga kuma a tare suke fita, yanzu Bilal baya taɓa fita tare da Ramish, sai dai ya fita shi kaɗai, ga yawon dare da yake yi wanda a baya sam baya yi, baya zaman gida ko wajen aiki sosai yanzu, hakan ya kara ɗarsa zarginsa a zuciyar Ramish, sannan sai ya rinƙa kawowa Ramish wasu silly silly abubuwa da basu da amfani ya haɗa shi da aiki yasa Ramish baya aiki bincikensa yadda ya dace, hakan yasa ya ja lokacin bai iya gano gaskiya a kan abin da yake bincika ba, ga shi gobe taron da zasu yi ne. A takaice abubuwa dayawa ya ja Ramish ya fara zargin Bilal tun watannin huɗu da suka wuce.

Da karfi Ramish ya damki wuyar rigar Bilal, idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir, da alama yana out of control ɗin da gaske, jikinsa har wani kerma ta soma yi, yana gudun tsono abin da zai iya zame mashi narazana ga rayuwarsa, sannan kuma yana san tono gaskiya ko dan ya san ina ya dosa da suwaye yake tare.

"Ka faɗa mun me kake ɓoye mun". Cikin zafa Ramish ya yi tambayar haɗe da ɗan ɗaga murya.

Pretending................. Ƙoƙarin nuna gaskiyarsa Bilal ya yi, yana san nuna shi ba mai laifi bane kuma babu abin da yake ɓoyewa, hakan yasa ya dunkule hannunsa da karfi ya kaiwa Ramish duka a kirji. Cikin ɗaga murya ya ce.
"Wani irin abu ne wannan? Meyasa na zama abin zargi a gareka? Meyasa zaka ce ina ɓoye maka wani abin? Mekake nufi da kalamanka a kai'na? Ko kana tinanin ni zan iya cutar da kai ne?".

(My people's yanzu na ce waye ya kawo maganar cutarwa a nan? Babu rami meya kawo maganar rami? Shin Ramish ya ce Bilal zai cutar da shi ne da Bilal ya kawo batun cutarwa? Ku tayani yin alkalanci a nan wajen.)

Da gudu Dr Raj and Yah Rizwan suka fito daga nasu bedroom É—insu jin muryar Bilal cikin faÉ—a yana magana. Innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne abin da suka furta a tare.

Zame hannunsa Ramish ya yi daga wuyar rigar Bilal, da hannu É—aya yasa ya daki kirjin Bilal da karfi har sai da Bilal ya yi baya baya ya bugu da jikin bango. Duuuuuuuuuummmmmmmmmm

"You are lying Bilal! There must be something you are hiding for us, and you have to tell us what you are hiding today!!". Cewar Ramish kenan.

Bilal domin ya kare kansa ya kuma tabbatar da gaskiyarsa sai ya yi ƙoƙarin kawo abin da zai kawar da batun ya faɗa masu me yake ɓoye masu, sai ya yi ƙoƙarin yin faɗa da Ramish ta yadda hakan zai ja wancan zancen ta kau.

Da karfi ya nufi Ramish da nufin zai rama dukan kirjinsa da ya yi. Dr Raj da Yah Rizwan ne suka shiga tsakaninsu da gudu, sanya karfi Bilal ya yi ya bangaje Dr Raj da karfi har sai da ya faÉ—i a saman sofa. Yah Rizwan kuma ya taresa yana mai daka mashi tsawa a kan ya nitsu su bar shir men nan.

Yah Ramish dai yana tsaye yana binsa da kallo, mamaki ne ma ya kama shi, wai yau shi da Bilal ne a irin wannan yanayi? Wannan wace iriyar musifa ce? Su da suke san junansu tamkar su yi wa juna numfashi! To wai me matsalar ne?.

Ya jefawa kansa tambaya, jikinsa dik a mace sosai, sam baya san dukan Bilal, dan wlh idan ransa ya ɓaci za'a iya kwasan Bilal ranga ranga, shiyasa yake ya ƙoƙarin koran shaiɗan kada ya kaisa ya barosu, dan har yanzu yaki yardanwa da zuciyarsa Bilal mai laifi ne. Allah sarki zuciya, kun san dama da wuya ya iya karɓar wannan kaddara idan har ba yaga da gaske ido da ido Bilal ya cutar da shi ba.
Chapter 79 · 0% Book details