Sashe 196
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"No Yah Ramish, na tabbata baka sona, nafa san halin larabawa, tin ina karama na tashi a cikinku, nasan dik wani hali naku, kuna da kishin zubewar mutumcinku, bare ma kai da ka fito daga cikin babban family masu karfin faÉ—a aji a kasar, dole ka yi komai dan mutumcin gidanku". Ta kai karshen maganar tana tari mara sauti sosai. "Aesh yanzu baki yarda da maganata ba kenan?". Shiru bata iya amsa mashi ba. Kara matsawa jikinta sosai ya yi, cikin sigar rarrashi ya fara yi mata dabara dan ta yarda. Ko da sunan wasa ba ya san abin da ya aikata ta fita, ko dan kakansu King Badeen, and ace É—a ga King Zuhair yana da É—an shege? Kai ai abin babba ne.
Uhm aka ce maka namiji a fagen kalaman yaudara to fa an rufe kofa, dan kuwa Ramish sai da yasa ta yarda da cewa da gaske yake sonta, amma taki yarda ta amsa zata auresa, sai ta ce ta yarda da yana sonta, amma dan Allah ya kyaleta haka nan, idan ma saboda ciki ne ya mayar da ita Nigeria in da babu wanda ya sansa bare har mutumcinsa ya zube, zata reni cikinta a can ta haifesa ta kuma rike kayanta, ba zata taɓa kama sunansa a bakinta ba.
Kai kawai ya girgiza, lallai yau ya yarda Leesharh yarinya ce sosai mai ƙaramin tinani, wai ba zata taɓa ambatar sunansa ba, tab bata san me haihuwar bane, ai wlh time da yaron zai titsiyeta a kan ina ubanta san da zata ji takura ta faɗa mashi ma babu wanda ya sani, kuma dik bama wannan ba, a Nigeria tasan ƴan uwanta ne? Sannan shi dik bama wannan ba, yana bala'in san yara, bare kuma ace jininsa, a gaskiya yana son kayansa, dole idan akwai cikin nan ta haifa mashi kayansa ta bashi ko me zai faru sai dai ya faru, babu wani Nigeria da zai maida ta da ɗansa!!. Babbar magana, ya kuke ganin wanna cakwakiya zata kaya?. Bala'in can, ya mama uwar jiji da kai zata ji a lokacin da Ramish zai kawo mata bastard matsayin jika? Tab ya King zai yi?.
Shiru ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi a hankali hankali. Tamkar a mafarki suka ga wutar gidan ta ɗauke gabaɗaya, a ɗan razane ta yunkura zata bar jikinsa, ta ɗago kai tana kallan saman ɗakin. Tin da ya ga hakan yasan akwai matsala, dan wuta bata taɓa ɗaukewa haka nan. Tana ƙoƙarin barin jikinsa ya yi saurin rikota, kamar mai raɗa ya ce mata. "Yi shiru kada ki motsa". Muryarta a dashe ta ce. "Yah Ramish meyasa wutar ta ɗauke? Ni dai nasan tsawon shekaru ba'a ɗauke wuta a kasar nan! Ko dai kai ka kashe ne?............"
Yatsa ya É—aura mata a saman lips É—inta. "Kada ki sake yin magana, yi shiru, and ki zauna a nan ina zuwa, kome zai faru kada ki motsa daga nan". Ya kai karshen maganar tare da saketa. Tana san tambayarsa ina zai je, tana tsoron ya ce ta yi shiru kada ta yi magana, wayarsa na aljihinsa, amma bai kunna ligh É—inta ba, cikin sanÉ—a ya nufi waje. Yana fitowa ya ji takun tafiyar kartin mutane suna haurowa saman stair case É—in, shiru ya É—an yi yana mamakin yadda suke da karfin hali da dabarar iya kashe wutar gidan dan kada camera ta É—aukesu, dama shi yasan zasu biyosu, saboda dama bai yarda mota É—aya ce ta bi bayan Leesharh ba, dole sun saka masu ido, sai dai bai sa a ransa zasu yi saurin biyosu ba, ya yi zatan zasu É—an kwana biyu su yi shiri, fatansa a nan yanzu shi ne Allah ya bashi sa'ar kama ko mutum É—aya ne da ransa, dan samu amsoshin wasu tambayoyi nasa.
Yana tsaye yana tinani sai ji ya yi an bangajesa za'a wuce, har sun iso in da yake ba tare da ya farga ba. Wanda ya bangajesa ɗin ya yi gaggawar fitar da light mai bala'in haske ya dalle mashi fuska da shi, hakan yasa ya kashe mashi kwayar idanunsa baya iya ganin su waye ne. Ya yi ƙoƙarin kwace hasken, amma ina ba zai yiwu ba, dan baya iya ganinsu ma bare har yasan waye ya rike hasken ya kwace.
Tamkar saukar aradu haka ya ji saukar wani irin karfe a kansa, sun kashe mashi ido da haske baya ganinsu sun dakesa da wani katan karfe a kai, take wani irin jiri mai karfin gaske ta ɗebesa, dik hasken dake haska shi duhu yake gani a wannan lokaci, kan ka ce me ya zube ƙasa baya numfashi. Kawar da light ɗin daga kansa suka yi zuwa kan wasu dake bayan mai rike da light ɗin, wasu irin shirga shirgan mutane ne masu sanye da bakaken kaya haɗi da manya manyan boots a kafafunsu, ga hands gloves, mask, baka iya ganin komai a jikinsu sai jajayen idanun da suka yi ja saboda kayan maye!!.
"Ku shiga ku É—auko mun ita, shi wanna angama da shi!". Wanda ya rike light. Wucewa karti uku suka yi izuwa cikin É—akin, saura suka tsaya a tare da ogan nasu mai rike da light É—in.
My people's me kuke tinanin zai faru ne? Ni kaina page ɗin yau sai dai in kora Maltina and exotic kawai in yi shiru, mu leƙa Paris mu dawo!!.
🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥
Smart ya ɗauki a kallah 10 mins suna tattaunawa da King, da alamar rashin jituwa kuma a maganganun nasu, dan yadda Smart yake maganar zaka fahimci dikkansu ransu a ɓace yake. Daga karshe cikin fushi ya katse kiran, sannan ya yi off na wayar gabaɗaya tare da miƙewa ya nufi cikin ɗakin, haka ya rinƙa rarrashin Auta har tsawon kwanaki.
Yau takama weekend, Saturday, Smart yana tare da su a gida, bai je ko'ina ba, a ƴan kwanakin nan ya yi matuƙar sabo da su Pretty, tin tana bakanta mashi rai har ta dawo tana burgesa a dik abin da take yi, ba abin da ya fi ɗaukar hankalinsa a tattare da ita sai olive eyes ɗinta da kuma shegen shariyarta na jinin sarauta, tana bala'in burgesa yadda bata daga idanu ta kalli mutum, sannan tana matuƙar burgesa yadda take da tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take mashi tana tafiya da imaninsa ba, wani lokaci da gangan yake tafiya waje filin dolphins na Auta ya barsu a ciki, idan ta farga da baya kusa da su ta tsorata ta fara kuka kyau matuƙa take yi mashi.
Sanye yake da pj a jikinsa, suna sama gabaÉ—ayansu, Auta tana gyarawa Pretty gashin kanta suna ta hira, shi kuma ya tasa laptop a gabansa yana ta aiki dangane da bincikensa. Auta da Pretty suna sanye da hoodies na mata a jikunansu, Auta ta sanya hular kayan a kanta, ita kuwa Pretty daman kun san ba sanya É—ankwaki take ba koda ba gyaran gashi ake yi mata ba!.
"Yah Omerish me kake yi ne haka? Naga kamar zanen kunnan mutum da ido?". Cewar Auta, ta yi maganar idanunta a kan laptop dake gabansa, da yake suna kusa da shi sosai, a saman duguwar sofa set guda suke.
Hankalinsa a kan aikinsa ya amsa mata da. "Ina san kirkirar karfin ji ne fiye da komai, abin da zai iya dauko sauti tin daga nisan kilomita 10 a tafiya da ƙafa". Cike da mamaki ta sake cewa. "Yah Omerish to naga hoton kunne, me kake yi da shi?"........ "Kwaikwayon halittar Allah zan yi! Kamar yadda muka kwaikwayi halittar idanun mutum muka fidda camera haka nike san kwaikwayar halittar kunne dan in samu majiya mai karfi".
Ai Auta bata san time ɗin da ta saki Pretty ta miƙe ta dawo kusa da shi sosai ba, cike da mamaki ta ce. "Yah Omerish dama Camera idanun mutum aka kwaikwaya ne?".... Kai ya jinjina mata kafin ya amsa da. "Komai da kimiya take kirkira ai kwaikwayo muke daga halittar Allah, babu wanda ya isa ya kirkiro wani sabon abu a duniya, sai dai ya kwaikwayi wanda Allah ya yi, Ubangiji ya rigada ya halicci komai, kawai dai mu muna zamanantar da shi ne"..... Kara shiga mamaki sosai Auta ta yi, ita kuwa Pretty bama su isheta kallo ba, mashirmaciya, kwanciya ta yi tana kallan sama kamar wata dake da motsi a kai, babu ruwanta da tattaunawarsu.
"Yah Omerish to tayaya kuka kwaikwayi ido? Tayaya Camera yake kama da shi?". Cike da zaƙuwa da san jin amsa ta tambayesa. Dakatawa da aikin da yake yi ya yi, sannan ya juyo da kallonsa game da hankalinsa a kanta, cikin sanyin murya ya fara bata ilimi kamar haka!.
"Abubuwa da dama muka kwaikwaya daga idon mutum muka kirkiro Camera, cikin abubuwan da muka kwaikwaya sun haÉ—a da. Lens da Focusing wato mayar da hankali. Kamar yadda ruwan ido wato lens yake daidaita haske domin samar da kallo mai kyau, ya iya fahimtar menene a gabansa, haka ma camera ke amfani da lens dan mayar da hankali wato focus ga abubuwan da take É—auka, kin ga a nan mun kwaikwayi ido".
"Abu na gaba shi ne. Aperture wato kofar shigar hasken shiga. Ido yana da wani ɓangare da ake kira da pupil, wanda ke buɗewa ko rufewa don daidaita adadin hasken da ke shiga. To haka camera ma, tana amfani da aperture wanda ke sarrafa yawan hasken da ke shiga camerar, nan ma kinga idanu muka kwaikwaya".
"Na uku shi ne. Retina da image sensor, wato fuskar karɓar hoto. A cikin idon mutum, retina ce ke ɗaukar hoton da haske ya samar, sai ta aika wa kwakwalwa ta hanyar jijiyoyin gani, ƙwaƙwalwa itake tantance menene a wajen ba ido ba!. To haka a camera ma, akwai image sensor, wato kamar CMOS ko CCD wanda ke ɗaukar hoton da haske ya samar sannan ya juya shi zuwa hoto har ma a iya adanawa kamar yadda ƙwaƙwalwa take adana hoton da ido ya gani, in kaga abu ai ka rigada ka gani ne, ya zauna a kwakwalenka".