← Book details Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 202 OF 242

Sashe 202

Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rahilarh ki matsa mun daga gabana, dik abin da ya faru ba ke kika ja mun ba? Dik cikin ƴaƴana akwai wanda ya isa ina faɗa yana faɗa ne? Dik suna da tarbiya kuma suna respecting ɗina, kin cutar da ni Rahilarh, kin zalunci zuciyata, kinsa yau ɗan cikina, ɗan da na fi kauna sama da kai'na ne ya tsaya a gabana ina faɗa yana faɗa har yake ce mun zan yi danasani a rayuwata saboda rashin tarbiya!"....... Nisawa Smart ya yi, ya ji King yana ƙoƙarin zagan mashi daddynsa na France, wato shi ne bai bashi tarbiya ba, maganar ta kora ransa sosai, cike da takaici ya ce. "Suma ƴaƴan dake da tarbiyar nan gaba kaɗan zasu dai'na yi maka biyayya idan har zaka cigaba da tauye masu hakkokinsu kana zaluntarsu dan wani san zuciya taka, suma zasu dai'na bin umarninka a lokacin da zasu fahimci suna da ƴancin kansu". Cikin kunar rai ya kai karshen maganar.
Ran King idan ya kai miliyan to fa a wannan gaɓar ta ɓaci, zuciyarsa a tafashe ya kwace rikon da momma ta yi mashi, yana huci kamar wani zaki ya damki wuyar rigar Smart. Momma bata ɓata lokaci ba wajen sake shiga tsakaninsu, cike da tashin hankali ta fara faɗin King ya yi hakuri ya sake shi a bi komai a hankali, tasan koma me ya faru ita ce sila, kowa laifinta zai gani, kuma hakan take laifinta ne, ita ta kai Smart in da tarbiyarsu ya saɓa da na gidan sarauta, krista ce fa ta tarbiyartar da shi, kunga kuwa dik abin da suka gani sai dai su ja baki su yi shiru kawai.

"Momma ki kyalesa ya yi dik abin da yake ganin zai iya yi, amma dai Zunaira ba zata taɓa auren zaɓinsa ba!". Smart ya faɗa ko a jikinsa, dan shi zafin da King ya ɗauka ma ko ɗaya bata dame shi ba, saboda yasan ba komai bane idan aka danganta da zafinsa idan ya ɗauka. Rai a matuƙar ɓace Momma ta ce. "Omerish idan ka sake saka baki kan batun auren Zunaira ban yafe maka ba, haba mana, kasheni kake san yi ne? Meyasa baka tinanin kuncin da zaka sakani a ciki? Meyasa ka canza kake san ɓacin raina abin da a baya shi kafi tsana fiye da komai? Meyasa menayi maka da zafi haka?". Ranta ya kai kololuwar ɓaci ne, tana san sasanta abu shi kuma Smart yana neman kara lalata komai, shiyasa ta yi wannan furucin!.

Jin saukar kalamanta ya yi tamkar saukar aradu, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, a fusace ya sa hannu ɗaya ya ɓanɓare hannun King daga wuyarsa, cikin zafa ya juya ya bar ɗakin yana wani huci kamar mayinwacin zaki. Yana fita King ya dubi momma, a dakile ya ce. "Kin gani ba? Kinga irin abin da kika ja mun ba? To daga yau na haramtawa Omerish komawa kasar France, ya dawo kenan, ba zai sake komawa ba, dole ya zauna da mu a nan ya koyi tarbiya da girmamawa na gidan sarauta, ki kira iyayensa na can ki sanar masu na ɗauki ɗana kenan!!".

Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya koma cikin É—akin, ransa sai tafarfasa take yi. Shiru momma ta tsaya, ta rasa waye zata bi, ga Smart ya É—auki zafi ya fita, ga kuma King shi ma ya É—auki zafi, to waye zata bi dan ta rarrashesa kenan? Ta jefawa kanta tambayar, yau fa ake yinta.

A gefe guda kuwa. Auta ta tsala wankarta tsab, sai murna take yi zata ga jaruminta, dan kada a gano akwai wanda zata je gani yasa bata saka wani kayan azo a gani ba, sai ta sanya sleeping dress masu mutunci, riga mai dogon hannu da wando shi ma dogo. Ta sanya headband a kanta, ta É—auki wayarta ta nufo waje, wai dan ma idan ta haÉ—u da wasu kada su zargi wani wajen zata je. Har ta kai bakin kofa ta juyo ta ce. "Pretty ina zuwa, dik wanda ya zo nemana ki ce ina wajen Yah Omerish kin ji?". Pretty dake kwance saman gado bata amsa mata ba, yau miskilancin ta motsa kenan. Sanin cewa ta jita yasa Autar bata damu da sai ya amsata ba, ta yi gaggawar wucewa kawai ta fita. Jikinta sai tsuma take yi tana san kallan jaruminta.

Tana fita dai'dai lokacin kuma Abdussalam ya shigo part na family daga ɓangaren uncle Abbas, ya zo ganinta ne, dama ya yi kewarta sosai, so ya samu labarin ta dawo shi ne da marmarinsa ya zo ganinta. Ita kuwa a lokacin ta fita ta kofar baya, sai nemanta guyson ma yake yi, Chuchu and Aneesa dik suna ta nemanta, cikin sanɗa da dabara ta nufi ɓangaren mayaƙa, tana tafiya tana ɓuya. Har ta isa ɓangaren warriors ɗin. Kai tsaye ta nufi bedroom ɗinsa, sai murna take yi, a lokacin yana kwance saman bed ɗinsa, ya idar da sallar isha'i ba jimawa, ya yi wanka yana sanye da white arabs jallabiya mai shegen kyau, ya ɗauko wayarsa da nufin zai kirata kenan ya ji knocking, a tinaninsa Abbonsa ne ko su Ansar, sai bai yi magana ba ya ajiye wayar tare da saukowa kasan bed ɗin ya nufi door.

Ba tare da tambayar wanene bane yasa hannu ya ɓalle key na door ɗin ya ja ya buɗe. Ai bai san lokacin da ya zaro ido tare da blinking sau biyu a lokacin guda ba ganinta da ya yi. Cikin gaggawa ta raɓa gefensa ta shige cikin bedroom ɗin tana dariya, ƙasa juyawa ya yi ya koma, sai yake ganin abin kamar a mafarki, ko kaɗan bai yi zato ba, kuma ko kusa bai ji labarin ba, shi dai ya ga baki suna ta zuwa, idan baku manta ba Abbonsa ya ɓoye mashi lamarin, so bai da labari. Saman drawer dake kusa da bed ta zauna tare da ware tafukan hannunta ta rufe face ɗinta tana sakin cool smile. Ya jima tsaye a wajen yana al'ajabi kafin ya juyo ya dawo ciki, rufe kofar da key ya yi, gabaɗaya sai ya ji ya ƙasa iya ɗaga idanu ya kalleta, wani irin zazzafar sonta ne yake kara fisgarsa. Da kyar ya karisa in da take, a bakin bed ya zauna suna fuskantar juna, sai ya yi ƙasa da kai ya kasa magana ita ma ta rufe fuska tana murmushi ta ƙasa magana.

Abin like wow gwanin birgewa, yadda suka zauna abin ya ƙayatar, kamar wasu mata da miji da suka mallaki juna!. Almost five minutes suna a haka kafin ya ɗan nisa, kansa a ƙasa yaki ɗagowa ya ce. "What a wonderful surprised! Gaskiya ba zan taɓa manta wannan rana ba my Hoonaira". Taki cire tafukanta daga face ɗinta ta ce. "My Hero ka ƙara kyau sosai, ka ɗan yi kiba abinka"........ "Na sha drips ba adadi ai dole na yi kiba, kema ai kin kara kyau sosai, kinsa na ji tamkar yau na fara ganinki". Cike da mamaki ta ce. "Dama ka ganni ne?". Ta yi maganar ne saboda taga ko sau ɗaya bai ɗago ido ya ganta ba, kansa a ƙasa, kuma ya ce ta kara kyau, ko a ina ya ganta?..... Bata san ɗan ikka ne yana satar kallanta ba, mai kunya irin na Jaish😅

Kai ya jinjina mata alamar ya ganta mana. "My Hero kai ne fa kullum kake damuna a kan yaushe zan dawo, na dawo cike da muradin zuwa in ganka, na zo kuma ka yi ƙasa da kai, kaki ɗagowa mu kalli juna, to me yasa?". Cikin shagwaɓa sosai ta kai karshen maganar. Ɗan ɗago idanunsa ya yi ya saukesu a kan kyawawan kafafunta dake cikin wasu kyawawan flip flops masu laushin takawa. "Ni ai na ganki". Ya faɗa idanunsa na ɗan rawa, kamar yana tsoron ɗagowa ya kalli kayan jikinta ne!..... "No my hero, ni gaskiya ban yarda da irin wannan kallon ba, ni fa yanzu nasan gaskiyar abin da yake cikin zuciyarka kamar yadda kasan nawa, meyasa zaka cigaba da azabtar mun da kanka wajen hana idanunka kallan abin da kasan zai zama mallakinka koma in ce ni taka ce?". Kamar zata saka mashi kuka ta yi maganar.

Nisawa ya ɗan kara yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗimi, lallai ba shakka yau ta yi mashi abin da tasa saura kaɗan farinciki ya kashesa, dan a lokacin da ya buɗe kofar nan ya sauke kallansa a kanta saura kaɗan numfashinsa ta dakata da breathing!. Slowly ya ɗago da kallonsa izuwa saman face ɗinta, cikin natsuwa ya ce. "Ba wai ina hana kaina kallanki bane, bana san kallan ya wuce na Musulunci ne, nasan in dai na ɗaga idanu direct na kalli face naki to fa zan zarce kallan musulunci, dan ba zan iya hakurin zare kallona daga kanki ba". Ya kai karshen maganar yana tsayar da idanunsa a cikin nata, kallansa take yi kawai tamkar ta mayar da shi cikin kirjinta haka take ji. Take idanunsu ya sarkafe cikin na juna, suka mace da zubawa juna kallon kauna, wani irin salon kallo da suke aikawa junansu mai cike da saƙonni da suke nuna tsantsar kewa da kauna juna tin da nike a wajensu kawai na taɓa kallan irin wanna salon kallon. Ko waye ya koya mashi? Gara ita Auta mun san daga ina ta koyo, shi fa? Mu dai mun san banda yaki babu abin da ya iya!.
Chapter 202 · 0% Book details