Sashe 25
Rawanin Zalinci Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
So ya fi kayar da hankalinsa a kan ginin da kusan rabin aikin Robbot ne suke yinsa ba ƴan adam na, hakan yasa aikin yake kara sauri yake kuma tafiya yadda ya kamata, ga shi girman companyn gidan sama ne mai hawa goma, Robbot sun taka muhimmiyar rawa sosai wajen rage samu mace mace mutane a kan wanna gini, su suke hawa sama ƙololuwa su yi aiki, kunsan a gini irin haka laburas and engineers suna rasa rayukansu wajen faɗowa kasa daga sama idan aka samu akasi, so yanzu Robbot ke hawa sama wanda su idan ma suka faɗo sai dai su tashi su karkaɗe jiki su kara gaba abinsu, babu abin da zai same su!.
So yanzu an samu sauki sosai wannan fasaha ta Black Tiger wajen amfani da Robbot sosai a aikin da ƴan adam suke yi ya yi matuƙar birgewa, saboda ya taimakawa mutane matuƙa. Yanzu hankalinsa baya a kansu sosai.
Ko ban faɗa ba nasan kunsan dik faɗin birnin Black world babu wanda za'a samu ta iya doke Sweetie a kyau, dan faɗe ma ɓatawa ne, kun san in ta shiga fili dole mata su matsa mata, hakan ma yasa Floris ta kullah mata tuggun ta hanata shiga wajen, amma ina hakarta bai cinma ruwa ba.
Sweetie ta yi gasa kuma ta ci na É—aya, Angela ta zo na biyu, sai Floris ta uku, ba komai yasa Angel ta zo na biyu ba kuma face alhakin Sweetie ne ya kama Floris, ta mata mugunta reshe ya juye da mujiya, ita da take zuwa na É—aya kullum yau ta kare a na uku.
Idan ranta ya kai miliyan to ya ɓaci, zuciyarta ya sosu, tsabar kishi da kuka ta bar wajen taron, bata ma tsaya an shigar da mark na kowa a Idanta ba, ta wuce ciki da gudu.
Sai gobe da safe za'a bawa waÉ—an da suka ci gasar kyautarsu, hakan yasa Sweetie ta ce da Ronnie zata je ta yi barci dan zata tashi ta yi sallar dare.
Sam bai so hakan ba, ya so ta tsaya su yi casun rawar da zasu yi, ya so koya mata rawa, amma baya san shiga hakkinta, sai ya rakota har cikin room É—insa ya ce ta kwanta a nan shi zai je wajen rawar, in suka gama rawa kuma ba lallai ya dawo É—akin ba, kila a É—akin yayansa zai kwana.
Ko tsoro babu a tattare da ita ta amsa da to tare da wucewa ciki, yana tsaye har sai da ta canza kayan jikinta izuwa kayan barcin Floris da ya kawo mata, dressing room É—insa ta shiga ta canza kayan, sanna ta zo ta haye gado, da kansa ya rufeta da bargo kafin ya juya ya fita.
A tunaninsa Floris tana wajen gasa, dan bai ga fitarta daga wajen ba, hankalinsa na kan Sweetie, so bai san ta fice ba, hakan yasa ya koma can dan su yi rawa da ita.
Ita kuwa Sweetie Ronnie na tafiya ta miƙe zaune, dama ba wani barcin da take ji, so take ta dawo dan ta zo ta yi masu bincike a cikin gidan.
Kamar wata ɓarauniya haka ta saɗaɗa ta fito waje ta hanyar sanya password na kofar ta buɗe, ya gaya mata password ɗin yanzu.
Ko tsoro babu ga dare wajen karfe 12, ga kuma kanta ko É—ankwali babu, kuma tasan akwai ababen ban tsoro a gidan, amma ko É—ar bata ji ba ta nufi part É—in Black Tiger.
Kunsan komai ilimin mutum in dai yaro ne to sai yarintar nan ta nuna, a shirmen yarintarta wai tunani take yi Black Tiger ya yi barci, hakan yasa ta lallaɓa dan ta je ta yi mashi bincike a part ɗinsa, Ronnie ya gaya mata akwai kofar sirri na fita daga cikin Daular nan a saukake, amma kofar tana cikin part ɗin yayansa, shi kansa bai san takamaiman in da kofar take ba, amma zai bincika masu, to shi ne ita uwar ƴan rashin tsoro ta je dan ta fara bincikawa da kanta, bayan kuma Ronnie ya gaya mata ta yi taka tsantsan kada ta sake shiga gonar yayansa, in ba haka ba zata rasa ranta ne a banza, amma kunga yarinyar nan bata ɗauki zancensa a bakin komai ba, ta yi fatali da komai ta yi biris.
Babban parlournsa ta shiga, babu komai sai daddaÉ—ar kamshi dake tashi, ko'ina very very clean, kamar sabbin kaya aka zuba.
Wucewa ta yi ta nufi É—aya daga cikin bedroom dake cikin parlourn, ba ainahin bedroom É—insa ba.
Babu wani É—ar ta gwada sanya password irin na É—akin Ronnie, ga mamakinta sai gani ta yi kofar ya buÉ—e, wato ba ina ga daga kan Sweetie karfin hali ya kare yarinyar nan. Kila ma ba dai'dai tasaka password É—in ba kawai an buÉ—e mata kofar ne dan a shirya mata tarko, amma sam bata gane ba!.
Har da wani É—an siririn munafikin sallama ta yi yadda kukasan É—akin Pretty zata shiga.
Tashin sense, ai tana shiga cikin É—akin sai ganinta ta yi a wani irin kungurmin forest, wata duniya daban, wanda ganinsa kawai zai iya sa mai karamar zuciya zuciyar tasa ta buga ya mutu.
Ai bata san lokacin da ta kurma ihu ba na ganin wanna kungurmin forest bakin kirin mai cike da abin tsoro, gabaÉ—aya bishiyoyin cikin forest É—in suma jikinsu ya yi bakin kirin, ga wasu irin kawunan mutane, ga kasusuwan kwarangwal, abin dai sai wanda ya gani, ga wasu irin inuwa dake gilmawa ta gaban idanunta tamkar na wasu gungun aljanu, a gabaÉ—aya dajin nan babu wani abu mai É—an dama dama da zaka iya gani, sai zallar madarar abin tsoro mai firgita kwakwalwa.
Dik tsananin karfin hali irin nata sai da ta yi balai'n rasaza, ta kasa iya furta ko uppan, jikinta har kerma ya fara yi, sai ta fara danasanin meya kawota.
A hankali wani irin inuwar wani dogon halitta mai tsayin gaske ya fara nufo in da take tsaye, sam bata iya ganin wanna halitta, inuwarsa ne kawai zaka gani.
Da kyar ta iya É—aga kafarta da ya yi mata bala'in nauyi, a hankali ta fara ja da baya, inuwar yana kara tinkarota, jininta sai rawa yake yi, ta kasa iya furta sunan Allah da ya kawo mata É—auki.
Ganin da gaske wannan halitta ita yake nufowa yasa ta zage da iya karfinta na karshe ta tattare karfinta dikka ta juya da karfin gaske dan ta gudu ta fita waje, sai dai kash tana juyowa kofar É—akin ya rufe kansa da wasu irin mahaukatan locks masu ban mamaki wanda bata san da su a jikin kofar ba sai a yanzu.
Nan take gabaɗaya empire ɗin Black Tiger ya ɓacewa ganinta, ya zamana iya dajin ne kawai a wajen, kasar dajin in da take takawa kenan bakin kirin yake kamar gawayi.
Tashin sense, wani irin dukan tara tara kirjinta ya yi, da karfi ta wage baki ta kurma ihu, sai dai sam voice É—inta baya fita, kamar ma bata yi ihun ba.
Cike da fargabar abin da zata gani a hankali ta juyo kirjinta na dikan uku uku jikinta na kara tsananta kerma.
Wani irin mahaukacin ihu ta saki lokacin da ta gama juyowa ga wannan halitta dake nufota. Tin daga wanna ihu kuma bata sake iya ji ko ganin wani abin ba, ido da ido da ta yi da halittar yasa idanunta suka makance ta dai'na ganin komai, kunnuwanta suka kuramce ta dai'na jiyo sautin komai.
Me kuke tinanin ta gani ya makantar da ita? Me kuke tinanin zai faru da ta kurmance?
Yanzu wasansu zai fara, shin kuna tunanin dama zasu zubawa Sweetie ido ta musuluntar da su Ronnie ne? Su da jininsu na tsanar musulinci ce? Akwai matsala fa! Sweetie ta taro yakin da a yanzu dai ba iya shi zata yi ba! Saboda a yanzu ita kanta bata san wacece ita ba, bata san baiwar dake gareta ba bare ta yi amfani da shi wajen yakarsu ita ma dan ta taimakawa kanta da mutanen da zasu yarda da ita! Bata san ina ta dosa ba a halin yanzu, fatana dai Allah yasa kada su wujijjiga mana rayuwarta ko ma su shafe babinta a doran duniya!!.
===========================💘
DUBAI.🔥
Al'umma dai sun ki nutsuwa su kwantar da hankalinsu, saboda suna ganin mutuwa zasu yi, jami'an nan sun yi iya ka bakin ƙoƙarinsu kowa ya nutsu dan ma su iya gane kila makiyan suna a tare da su, amma ina kowa neman hanyar fita yake yi, dik da an rufe gates ɗin amma sun ki tsayuwa waje guda.
Gungun jami'ai ne suka yi wa ahalin Abu Abdussalam zobe domin su tabbatar da sun fitar da su lafiya lou.
Sai dai fa Ramish da aka hara yaki motsawa daga in da yake bare har ya bi ayarin Abu Abdussalam su koma gida.
Ya dai ce Bilal ya kasance a tare da Abbie É—in nasu, shi yana nan bari ya tabbatar da dik wanda ya zo nan dominsu ya koma gida lafiya ba tare da kwarzani ba, ba yadda Abu Abdussalam bai yi da shi a kan yazo su tafi ba amma yaki yarda.
Hankalin Abu Abdussalam a tsananin tashe, saboda yasan Ramish É—in aka hara kunga bai kamata ya tsaya a wajen ba, amma yaki tafiya, burinsa ya kama wanda ya yi wannan harbin.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Kaiwa suke suna sake komawa, suna safa da marwa a tsakiyar katafaren parlournsu, gabaÉ—aya zufa ce take ta keto masu, ta wanke fuskokinsu tamkar waÉ—an da aka watsawa ruwa, gabaÉ—aya parlourn da suke É—in A.c ne a kewaye ta ko'ina, amma a haka suke haÉ—a wannan zuba saboda bala'in zilmi da fargaba da suke ciki, fatansu É—aya shi ne Leesharh ta É—auki wanna call É—in, saboda wannan shi ne kawai damar da suke da shi, in har wanna dama ya kubce masu to abubuwa biyu dole su faru, na farko dole za'a kara tsananta tsaro a gidan Abu Abdussalam wanda ba zasu sake samun irin makamancin wanan dama ba, sannan dole su Ramish zasu shiga binciken wanenen yake yi masu wannan aiki?.
Sun san wanene Ramish tsab zai iya kamasu, dan kwararrene a aikinsa, dole su shiga tsananin tashin hankali.
Sai kiran wayar hannun Leesharh suke yi babu kakkautawa.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥